Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Afrilu pp. 26-31
  • Ku Ci-gaba da Ƙarfafa Aurenku

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Ci-gaba da Ƙarfafa Aurenku
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • YADDA ZA KU ZAƁI WANDA ZA KU AURA KUMA KU CI-GABA DA ZAMA ABOKAI NA KUD DA KUD
  • KU RIƘA KASANCEWA TARE
  • KU MANNE WA JUNA IDAN MATSALOLI SUKA TASO
  • Ya Za Ka Sami Macen Kirki?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Aure Kyauta Ne Daga Allah
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Zaman Aure
    Ku Ci Gaba da Kaunar Allah
  • Aure, Kyauta ne Daga Allah Mai Kauna
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Afrilu pp. 26-31

29 GA YUNI–5 GA YULI, 2026

WAƘA TA 131 ‘Abin da Allah Ya Haɗa’

Ku Ci-gaba da Ƙarfafa Aurenku

“Akwai irin abokin da ya fi ɗanꞌuwa aminci.”—K. MAG. 18:24

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga cewa maꞌauratan da suke so su ji daɗin aurensu suna bukatar su ƙaunaci Jehobah, kuma su zama abokan juna na kud da kud.

1. Me ya sa za mu iya ce abokan kirki kyauta ne daga wurin Jehobah?

ABOKAN kirki kyauta ne daga wurin Jehobah. (Yak. 1:17) Suna ƙaunar Allah kuma suna ƙaunar mu. Suna so mu yi farin ciki, da ƙarfafa mu lokacin da muke baƙin ciki, da kuma ba mu shawara a lokacin da muke bukatar hakan. A kullum suna taimaka mana, kuma za mu iya yarda da su. Irin abokan nan suna sa mu farin ciki!—K. Mag. 27:9.

2. Me ya sa yake da muhimmanci maꞌaurata su ci-gaba da ƙarfafa danƙon zumuncin da ke tsakaninsu? (Matiyu 19:6)

2 Yana da muhimmanci maꞌaurata su zama abokai na kud da kud. Zai dace su yi iya ƙoƙarinsu wajen ƙarfafa danƙon zumuncin da ke tsakaninsu. Idan ba su yi hakan ba, za su iya ji kamar sun kaɗaita, ko su yi baƙin ciki ko kuma su yi fushi. Amma, idan suka ci-gaba da yin iya ƙoƙarinsu, za su ƙulla dangantaka mai ƙarfi sosai. (Karanta Matiyu 19:6.) A wannan talifin, za mu ga yadda maꞌaurata za su iya ƙarfafa aurensu. Amma kafin nan, bari mu ga yadda ꞌyanꞌuwa maza da mata za su iya zaɓan wanda za su aura, kuma su ci-gaba da zama abokai na kud da kud.

YADDA ZA KU ZAƁI WANDA ZA KU AURA KUMA KU CI-GABA DA ZAMA ABOKAI NA KUD DA KUD

3-4. Mene ne zai taimaka wa wani ko wata ta zaɓi mijin kirki? (Karin Magana 18:22)

3 Kafin mu yanke wata shawara mai muhimmanci, muna bukatar mu yi tunani a kan sakamakon da zai biyo baya. Shawarar da muka yanke za ta iya canja rayuwarmu gabaki ɗaya. Saboda haka, muna bukatar mu yi tunani sosai kafin mu yanke wata shawara.

4 Ɗaya daga cikin shawarwari masu muhimmanci da za mu iya yankewa a rayuwa ita ce, zaɓan wanda za mu aura. Da yake Jehobah ne ya shirya zaman aure, zai dace mu bi ja-gorancinsa saꞌad da muke so mu zaɓi wanda za mu aura. Jehobah yana so namiji ya sami matar kirki, mace kuma ta sami miji nagari. Kuma Shi ne ya fi sanin abin da ya fi dacewa da mu. (Karanta Karin Magana 18:22; Isha. 48:​17, 18) Ƙaꞌidodin Littafi Mai Tsarki za su iya taimaka wa wani ko wata ta zaɓi wanda ya dace ta aura.

5. Me ya sa yake da muhimmanci Mashaidi ya auri wadda ta yi baftisma?

5 Da zarar mun yi baftisma, mun zama aminan Jehobah ke nan. (Zab. 25:14) Idan za ka so ka yi aure, zai dace ka zaɓi wadda take bauta wa Jehobah.a (1 Kor. 7:39) Yin hakan zai nuna cewa kana so ka bi ƙaꞌidodin Jehobah, kuma kana iya ɗaukan wadda za ka aura a matsayin kyauta daga wurin Jehobah. (K. Mag. 19:14) Ƙari ga haka, za ka guji matsalolin da ke tattare da auran wadda ba ta bauta wa Jehobah. (2 Kor. 6:14) Ko da ba ka sami wadda take bauta wa Jehobah da za ka so ka aura ba, kada ka kuskura ka auri wadda ba ta bauta wa Jehobah. Ko kuma ka soma fita zance da wata da tunanin cewa a kwana a tashi, za ta soma bauta wa Jehobah.

6-7. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu yi wa kanmu game da wanda muke so mu aura?

6 Gaskiyar ita ce, ba kawai don mutum ya yi baftisma ne zai sa ya zama aboki ko abokiyar auren kirki ba. Idan akwai wata da kake so ka aura, zai dace ka tambayi kanka: ‘Yaya take bi da danginta? Tana da son kai kuma ba ta daraja mutane? Su waye ne abokanta? Yaya take bi da matsaloli idan suka taso? Tana nacewa sai an bi raꞌayinta, ko tana amincewa da raꞌayin mutane musamman idan ta ga cewa bai taka dokar Allah ba? Mene ne raꞌayinta game da kuɗi?’

7 Ƙari ga haka, ka tambayi kanka: ‘Tana nuna cewa tana ƙaunar Jehobah sosai? Tana iya ƙoƙarinta don ta kasance da halayen da Jehobah yake so? Shin, za ta taimaka min in inganta yadda nake bauta wa Jehobah? Abubuwan da nake so in cim ma a ibadata ga Jehobah iri ɗaya ne da nata? Yadda nake ganin ta, za mu ci-gaba da zama abokan da suke ji da juna bayan mun yi aure? (Kol. 3:​9, 10) Ina ganin za ta daraja ni kuma to goyi bayan shawarwarin da nake yankewa, duk da cewa ni ajizi ne?’ Idan ke ꞌyarꞌuwa ce, za ki iya tambayar kanki: ‘Shin, ɗanꞌuwan da nake so in aura zai iya yanke shawarwari masu kyau a matsayinsa na shugabana, kuma mu ci-gaba da zama abokai na kud da kud?’ (1 Kor. 11:3) Amsa irin waɗannan tambayoyin bai da sauƙi. Saboda haka, zai dace ku yi ƙoƙari ku san wanda kuke so ku aura da kyau yayin da kuke fita zance.

8-9. Me zai taimaka ma wanda yake fita zance ya yanke shawara mai kyau? (Ka kuma duba hoton.)

8 A lokacin fita zance ne za ku san juna sosai, kuma ku san irin shawarar da za ku yanke. Ku yi ƙoƙari ku san raꞌayin mutane game da juna. Za ki iya tambayar ꞌyanꞌuwa a ikilisiya game da halayen ɗanꞌuwan. Alal misali, an san shi a matsayin mai sauƙin kai, mai hankali, da kuma sanin ya kamata? Wata ꞌyarꞌuwa mai suna Sarah daga French Guiana da ta auri wani ɗanꞌuwa mai suna Daniel ta ce: “Kafin mu yi aure na tambayi mutane game da Daniel. Alal misali, na tambayi wani ɗanꞌuwa da suke zama tare, da wani dattijo da ke ikilisiyarsu da abokanmu da suka waye mu sosai da kuma wasu ꞌyanꞌuwa mata a ikilisiyarsu.” Yana da muhimmanci ki tambayi wanda za ki aura ko akwai abubuwan da suka faru a rayuwarsa a dā ko suke faruwa yanzu da kike bukatar ki sani. Me ya sa? Domin akwai wasu abubuwan da za su iya jawo matsala daga baya.

9 Idan akwai abubuwan da ka lura kuma hakan ya sa ka soma shakka, ko kuma wasu ꞌyanꞌuwa sun gaya maka wani abu marar kyau game da wadda za ka aura. Kada ka yi watsi da hakan. Wannan zai taimaka maka ka yanke shawara ko za ku ci-gaba da fita zance ko za ku rabu.b Yanzu, bari mu ga yadda maꞌaurata za su ƙarfafa dangantakar da ke tsakaninsu.

Wani ɗanꞌuwa da wata ꞌyarꞌuwa da suke fita zance suna hira saꞌad da suka shaƙatawa da ꞌyanꞌuwa.

A lokacin da kuke fita zance, ku yi ƙoƙari ku san juna da kyau (Ka duba sakin layi na 8-9)


KU RIƘA KASANCEWA TARE

10. Me ya sa yake da muhimmanci maꞌaurata su riƙa kasancewa tare?

10 Maꞌaurata za su iya sa danƙon zumuncinsu ya ƙaru ta wajen kasancewa tare, ko da ayyuka sun yi musu yawa. Hakan zai ba su dama su tattauna da juna, da gaya wa juna abubuwan da suke tunani da yadda suke ji, da nuna wa juna ƙauna, kuma su shaƙata tare.

11. Mene ne zai iya jawo matsala tsakanin maꞌaurata?

11 Maꞌaurata da su abokan juna ne suna son kasancewa da juna a kowane lokaci. Ko da yake ɗaya daga cikinsu zai iya yin tafiya, idan tafiyar na dogon lokaci ne, hakan zai iya zama da haɗari sosai. Alal misali, wani zai iya samun aiki a wata ƙasa, kuma ya tafi ya bar iyalinsa har na watanni da yawa. Wataƙila hakan zai sa su sami kuɗi da yawa, amma hakan zai iya jawo matsaloli sosai a aurensu.

12-13. (a) Mene ne wasu maꞌaurata suka yi don su riƙa kasancewa tare? (Ka kuma duba hoton.) (b) Yaya ne ya kamata ku ɗauki dangantakarku da abokin aurenku? (Ka duba akwatin nan “Yaya Ne Ya Kamata Ku Ɗauki Dangantakarku da Abokin Aurenku.”)

12 Mene ne wasu maꞌaurata suka yi don su riƙa kasancewa tare? Wata mai suna Leah daga Guam, ta ce: “Ni da mijina muna jin daɗin yin abubuwa dabam-dabam tare. Da kyar mu je shaƙatawa ko wani wuri ba tare da juna ba.” Wata kuma mai suna Roxanne daga Amirka, ta ce: “Da yake ayyuka sun yi mana yawa, mukan shirya lokaci don mu kasance tare, kamar yadda muke shirya wasu ayyukan da suke da muhimmanci.” (Ka duba Amos 3:3.) Damien daga Faransa, ya ce: “Mun lura cewa yana da muhimmanci mu koyi abin da abokin aurenmu yake son yi. Kuma a sannu a hankali har mu soma jin daɗin yin sa.” (Mat. 7:12) Wata mai suna Katie daga Amirka, ta ce: “A wasu lokuta, mukan ajiye naꞌurorinmu a gefe don mu iya yin hira da juna.”

13 Abin da ya fi muhimmanci ma shi ne, maꞌaurata su riƙa yin ayyukan ibada tare. Myriam daga Faransa ta ce: “Kowace rana mukan fara da karanta Littafi Mai Tsarki, kuma mu gaya wa juna abin da muka koya da muke so mu yi amfani da shi a rayuwarmu. Ina jin daɗin irin wannan lokacin da muke kasancewa tare.” Ƙari ga haka, ina jin daɗin lokacin da muke adduꞌa tare, kuma in ji yadda mai gidana yake ƙaunar Jehobah. Katie da muka ambata ɗazu ta ce: “Mun fi jin daɗin lokacin da muke waꞌazi tare, domin yana taimaka mana mu kusaci juna sosai, kuma mu koyi sabbin abubuwan daga wurin juna.”—K. Mag. 27:17.

Ɗanꞌuwa da ꞌyarꞌuwar sun zauna suna hira bayan sun yi aure.

Ku ci-gaba da ƙarfafa aurenku ta wajen kasancewa tare (Ka duba sakin layi na 12-13)


Yaya Ne Ya Kamata Ku Ɗauki Dangantakarku da Abokin Aurenku?

Akwai waɗanda suke da muhimmanci sosai a rayuwarmu. Amma idan kana da aure, waye ne ya kamata ya fi muhimmanci a rayuwarka?—Filib. 1:10.

  1. 1. Jehobah. Dangantakarmu da Jehobah ce mafi muhimmanci a rayuwarmu. (Mat. 6:33; Mar. 12:30) Bai kamata mu yi abin da zai ɓata wa Jehobah rai don kawai mu faranta wa abokin aurenmu rai ba.—A. M. 5:29; ka duba Farawa 2:​16, 17; 3:6.

  2. 2. Aboki ko abokiyar aurenka. Saꞌad da ka yi aure, kai da matarka kun “zama ɗaya.” Saboda haka, wajibi ne ka kula da matarka kamar yadda kake kula da kanka.—Far. 2:24; Afis. 5:​28, 29, 33.

  3. 3. Wasu mutane da ayyukan ibada. Yana da kyau mu kula da iyayenmu, da danginmu, da ꞌyanꞌuwa a ikilisiya da kuma ayyukan ibada. Bisa ga abin da muka gani, Jehobah ne ya kamata ya zama farko a rayuwarmu. Bayan haka, sai aboki ko abokiyar aurenmu. Don haka, ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu mu faranta ran wanda muka aura.—1 Tim. 5:8.

KU MANNE WA JUNA IDAN MATSALOLI SUKA TASO

14-15. Me ya sa zai dace maꞌaurata su yi iya ƙoƙarinsu wajen warware matsalolinsu? Ka ba da misali.

14 Da yake maꞌaurata ajizai ne, a kwana a tashi matsaloli za su taso. Littafi Mai Tsarki ya ce “waɗanda suka yi aure, za su sha wahala a jikinsu.” (1 Kor. 7:28) Hakan yana nufin cewa za su yi fama da matsalolin da waɗanda suka yi aure suke fama da su. Idan irin matsalolin nan suka taso, zai dace maꞌaurata su yi iya ƙoƙarinsu wajen magance matsalolin tare, kuma su manne wa juna. Me ya sa?

15 Ga wani misali. A ce wani babban gini ko wani zane mai kyau sosai ya lalace, masu ginin ko zanen za su so su gyara shi. Za su iya kashe makuɗan kuɗi ko su ɗau lokaci sosai wajen yin gyarar. Kuma ba za su daina ba ko da yin gyarar zai ɗau shekaru da yawa. Me ya sa? Domin ginin ko zanen yana da muhimmanci sosai a gare su. Haka ma yake da aure. Ko da maꞌaurata suna ƙaunar junansu sosai, a kwana a tashi matsaloli za su taso. Amma kamar yadda za a iya gyara gini ko zanen da ya lalace, maꞌaurata za su iya shirya kuma su warware matsalolinsu. Yin hakan zai iya ɗau lokaci. Amma idan maꞌaurata suka yi iya ƙoƙarinsu don su warware matsalolinsu, hakan zai sa Jehobah farin ciki. (Mal. 2:16) Ƙari ga haka, yin hakan zai nuna cewa suna daraja da kuma ƙaunar Jehobah wanda shi ne ya shirya zaman aure.

16. Bisa ga 1 Korintiyawa 13:​4-8a, mene ne zai taimaka wa maꞌaurata da suke fuskantar matsaloli? (Ka kuma duba hoton da kuma akwatin nan mai jigo “Abubuwan da Za Su Taimaka Muku Ku Ci-gaba da Zama Abokai na Kud da Kud.”)

16 Idan matsaloli suka taso a aurenku, kada ku ga kamar rabuwa ne zai warware matsalolin. (1 Kor. 7:​10, 11) A maimakon haka, ka tambayi kanka, ‘Shin, akwai abubuwan da zan iya yi da za su sa mu ƙara kusantar juna?’ Ka bincika abin da Littafi Mai Tsarki ya ce game da nuna ƙauna, kuma ka yi tunani a kan yadda za ka ƙara kasancewa da halayen da aka ambata a 1 Korintiyawa 13:​4-8a. (Karanta.) Maimakon ku yi tunanin rabuwa, ku yi ƙoƙari ku ƙara kusantar juna. Kowannenku ya yi ƙoƙari ya san abin da yake bukatar ya yi don ku ci-gaba da farin ciki a aurenku. Ku roƙi Jehobah ya taimaka muku. Ku nemi littattafanmu da bidiyoyin da za su taimaka muku ku san abin da za ku yi. Za ku iya neman shawara daga wurin dattawa ko maꞌauratan da suka manyanta. Idan kuka dogara ga Jehobah wanda shi ne igiya mafi ƙarfi a cikin “igiyoyi uku” kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya kwatanta aure, dangantakarku za ta daɗa danƙo.—M. Wa. 4:12.

Ɗanꞌuwan da matarsa a gida suna ƙoƙarin warware wata matsala da ta taso. Matar tana kuka tana bayyana wa mijinta yadda take ji. Shi kuma mijin ya zauna shuru, ya sa hannu a kafaɗarta yana sauraronta. Akwai Littafi Mai Tsarki da kuma ƙasidar nan “Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya” a kan teburi da ke gabansu.

Ku ci-gaba da manne wa juna idan matsaloli suka taso (Ka duba sakin layi na 16)


Abubuwan da Za Su Taimaka Muku Ku Ci-gaba da Zama Abokai na Kud da Kud

Ƙungiyar Jehobah ta shirya abubuwa da dama da za su taimaka wa maꞌaurata su ci-gaba da zama abokai na kud da kud, kuma su warware matsaloli masu wuya idan suka taso. Shin, ka taɓa bin shawarwarin da aka bayar a bidiyoyi da ƙasida da kuma talifofin da ke gaba?

  • Ƙasidar Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya

  • Bidiyoyin da ke sashen Abin da Zai Sa Ma’aurata Farin Ciki

  • Talifofin da ke sashen “Taimako don Iyali”

  • Sashen “Aure da Iyali” a jw.org/ha

17. Me zai taimaka wa waɗanda suke so su yi aure da waɗanda sun riga su yi aure su yi farin ciki?

17 Jehobah yana so dukan bayinsa su yi farin ciki ko da sun yi aure ko suna shirin yin hakan. Saboda haka, idan kuna so ku yi aure, ku mai da hankali sosai wajen zaɓan wanda za ku aura. Idan kuma kun riga kun yi aure, ku ci-gaba da ƙarfafa dangantakar da ke tsakaninku. Ku yi ƙoƙari ku warware matsalolin da za su taso kuma ku roƙi Jehobah ya taimaka muku. Yin hakan, zai sa ku “ji daɗin rayuwa” da wanda kuke ƙauna!—M. Wa. 9:9.

MECE CE AMSARKA?

  • Ta yaya za ka iya zaɓan wadda za ka aura kuma ku ci-gaba da zama abokai na kud da kud bayan aurenku?

  • Mene ne zai taimaka wa maꞌaurata su ci-gaba da ƙarfafa dangantakar da ke tsakaninsu?

  • Mene ne zai taimaka wa maꞌaurata su ci-gaba da manne wa juna idan matsaloli suka taso?

WAƘA TA 132 Yanzu Mun Zama Ɗaya

a Shawarwarin da ke talifin nan za su amfani namiji da ta mace.

b Don samun ƙarin bayani a kan yadda za ku iya sanin juna sosai, ku duba ƙaramin jigon nan “Ku San Juna Sosai” a talifin nan mai jigo “Me Zai Taimaka wa Masu Neman Aure Su Yi Nasara?” da ke Hasumiyar Tsaro ta Mayu 2024.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba