Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Afrilu pp. 20-2333
  • Ka Yi Koyi da Allah Wanda Yake Ƙarfafa Mu

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Koyi da Allah Wanda Yake Ƙarfafa Mu
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE NUFI DA ƘARFAFAWA
  • YADDA ZA MU IYA ƘARFAFA MUTANE
  • ABIN DA ZA KA IYA YI SAꞌAD DA KAKE BUKATAR ƘARFAFA
  • Shirin da Aka Yi don A Ƙarfafa Masu Hidima a Bethel
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ba Za Mu Taɓa Zama Mu Kaɗai Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka “Yi Wa Dukan Masu-makoki Ta’aziyya”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2011
  • Yadda Za a Taimaka ma Wadanda Aka Ci Zarafinsu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2019
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Afrilu pp. 20-2333

22-28 GA YUNI, 2026

WAƘA TA 90 Mu Riƙa Ƙarfafa Juna

Ka Yi Koyi da Allah Wanda Yake Ƙarfafa Mu

Ka “ƙarfafa wasu . . . da ƙarfafar da muka samu daga wurin Allah.”—2 KOR. 1:4.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda Jehobah yake ƙarfafa mutane da kuma yadda wasu suka bi misalinsa. Hakan zai taimaka mana mu san yadda mu ma za mu iya ƙarfafa mutane.

1. Me ya sa mu ke bukatar mu riƙa ƙarfafa mutane?

DUKANMU muna “baƙin ciki” don matsaloli dabam-dabam da muke fama da su. Saboda haka, muna bukatar ƙarfafa. (1 Bit. 1:6) Muna farin ciki idan aka ƙarfafa mu yayin da muke shan wahala. Saboda haka, zai dace mu yi saurin ƙarfafa wasu saꞌad da suke fama da matsaloli. (Mat. 7:12) Jehobah, “Allah da ke ƙarfafa mu,” ya koya mana yadda za mu iya “ƙarfafa wasu a kowanne irin wahala.” (2 Kor. 1:​3, 4; 1 Tas. 4:18) Muna ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu don muna ƙaunar su, ba don ya zama dole ba ne. A wannan talifin, za mu tattauna (1) abin da Littafi Mai Tsarki yake nufi da ƙarfafawa, (2) yadda za mu iya ƙarfafa mutane, da kuma (3) abin da za mu yi idan muna bukatar ƙarfafa.

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YAKE NUFI DA ƘARFAFAWA

2. Mene ne kalmar nan “ƙarfafa” take nufi a Littafi Mai Tsarki?

2 A Littafi Mai Tsarki, kalmar Girkanci da aka fassara zuwa ƙarfafa tana iya nufin abubuwa dabam-dabam. Alal misali, tana iya nufin taꞌaziyya, ko faɗan abin da zai kwantar wa mutum hankali, ko kuma taimaka wa wani ya ɗau matakin da ya dace. (Rom. 12:8) Ƙari ga haka, kalmar tana iya nufin yadda mutum yakan tsaya a gefen wani don ya taimaka masa. Don haka, idan muka ji kalmar nan ƙarfafa, wani abin da zai iya zuwa zuciyarmu shi ne, irin saurin da mutum yake yi don ya taimaka wa abokinsa da ke cikin matsala. Amma ko da mene ne muka yi don mu taimaka wa wanda yake fama da matsaloli, burinmu shi ne mu ƙarfafa shi kuma mu kwantar masa da hankali.

3. Mene ne muka koya daga labarin Barnabas? (Ka kuma duba hoton.)

3 A Littafi Mai Tsarki, wani Krista mai suna Yusufu ya ƙarfafa mutane sosai kuma ya taimaka musu. Hakan ya sa manzanni a lokacin suka soma kiran sa Barnabas, wanda da yake nufin “Ɗan Taꞌaziyya.” (A. M. 4:36) Sunan nan ya yi daidai da shi sosai, kuma ba a sake kiran sa da ainihin sunansa a Littafi Mai Tsarki ba. Barnabas yana yawan taimaka wa ꞌyanꞌuwa a lokacin da suke da bukata. Alal misali, jim kaɗan bayan Shawulu ya zama Krista, ya je Urushalima don ya haɗu da Kristocin da ke wurin. Amma ꞌyanꞌuwan sun ji tsoro sosai domin sun san cewa shi mai tsananta wa Kristoci ne. Duk da haka, Barnabas bai ji tsoron yi wa Shawulu alheri ba, kuma ya taimaka wa manzanni su karɓi Shawulu hannu bibbiyu.—A. M. 9:​26-28.

Barnabas yana kai Shawulu wurin wasu manzanni da suka haɗu a wani gida. Manzannin suna kallon Shawulu suna shakka yayin da yake zuwa kusa da su.

Barnabas ya yi wa Shawulu alheri kuma ya taimaka wa manzanni su karɓi Shawulu hannu bibbiyu (Ka duba sakin layi na 3)


YADDA ZA MU IYA ƘARFAFA MUTANE

4. Idan muna so mu ƙarfafa mutane, wace hanya ce ta fi kyau mu yin hakan? (Romawa 1:​11, 12)

4 Mu ziyarce su idan zai yiwu. Jehobah yana amfani da malaꞌiku da kuma mutane wajen ƙarfafa bayinsa. Alal misali, a lokacin da annabi Iliya yake baƙin ciki, Jehobah ya sa wani malaꞌika ya ƙarfafa shi. (1 Sar. 19:​4-7) Ban da haka, akwai lokacin da manzo Bulus ya so ya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa, ya gwammaci ya je ya same su don su ƙarfafa juna. (Karanta Romawa 1:​11, 12.) Idan ka ziyarci wani, kada ka yi saurin tafiya. Hakan zai sa ka sami isasshen lokacin ƙarfafa shi. (1 Kor. 16:7) Amma idan ba za ka iya zuwa wurin wani da ke bukatar ƙarfafa ba, za ka iya ƙarfafa mutumin ta wurin kiran sa a waya ko tura masa saƙo. Shin, za ka bar Jehobah ya yi amfani da kai wajen ƙarfafa mutane?

5. Me ya sa ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu a wasu lokuta zai iya yi mana wuya?

5 Yayin da abubuwa suke ƙara wuya a wannan kwanakin ƙarshe, zuwa wurin ꞌyanꞌuwanmu da suke bukatar ƙarfafa zai iya yi mana wuya sosai. Amma labarin Onesiforus wanda shi mutumin Afisa ne zai iya taimaka mana. A lokacin da aka sa Bulus a kurkuku a Roma, Onesiforus ya so ya ƙarfafa shi. Don haka, ya je Roma ya neme shi, duk da cewa hakan zai iya sa a kashe shi ko a jefa shi a kurkuku. (2 Tim. 1:​16-18) Kamar Onesiforus, ꞌyanꞌuwanmu a ƙasar Rasha suna ƙarfafa juna in ana tsananta musu. Idan aka kai wani ɗanꞌuwa kotu, ꞌyanꞌuwa sukan je kotun don su ƙarfafa wanda aka kama duk da cewa hakan zai iya sa a kama su. Me za ka iya yi yanzu don ka iya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa idan ana tsananta musu? Za ka iya yin nazari a kan yadda bayin Allah a dā da kuma a yau suka ƙarfafa juna. Da kuma yadda suka ci-gaba da kasancewa da farin ciki duk da cewa ana tsananta musu.

6. Ta yaya za mu yi koyi da Jehobah saꞌad da muke ƙarfafa mutane? (Ka kuma duba hoton.)

6 Mu saurare su da kyau. A lokacin da annabi Iliya ya ga kamar za a kashe shi ya yi adduꞌa ga Jehobah, kuma ya gaya masa yadda yake ji a zuciyarsa. Duk da cewa Jehobah ya san abin da yake damun annabi Iliya, ya saurare shi. Jehobah ya ci-gaba da sauraron sa duk da cewa Iliya yana ta maimaita abu ɗaya! (1 Sar. 19:​9, 10, 14) Ƙari ga haka, a lokacin da annabi Habakkuk yake gaya wa Jehobah game da muguntar da ake yi da kuma wahalar da mutane suke sha, Jehobah ya saurare shi. Jehobah ya yi haƙuri da shi duk da cewa yadda ya yi magana bai nuna cewa yana girmama Allah ba. (Hab. 1:​2, 3) A yau ma, Jehobah yana sauraronmu saꞌad da muke yin adduꞌa duk da cewa ya san abin da muke so mu roƙa. Saboda haka, idan ꞌyanꞌuwanmu suna magana, zai dace mu saurare su da kyau kamar yadda Jehobah yake yi. Kada mu katse su saꞌad da suke magana don mu faɗa raꞌayinmu. Idan suka faɗi wani abin da ba daidai ba, kada mu yi fushi da su. Kuma idan sun yi ta maimaita abu ɗaya, mu ci-gaba da sauraron su.—Yak. 1:19; M. Wa. 7:9.

Wata ꞌyarꞌuwa tana sauraron wata ꞌyarꞌuwa da take cikin damuwa yayin da taka bayyana yadda take ji har yamma ya yi sosai.

Saꞌad da ꞌyanꞌuwa suke yi maka magana, ka saurare su da kyau kamar yadda Jehobah yake yi (Ka duba sakin layi na 6)


7. Idan wani yana cikin damuwa, ta yaya za mu iya sanin abin da yake bukata?

7 Mu yi ƙoƙari mu san abin da mutumin yake bukata. Ba za mu iya sanin abin da ke cikin zuciyar mutum kamar yadda Jehobah yake yi ba. Saboda haka, idan muna so mu san abin da mutum yake bukata, wajibi ne mu saurare shi da kyau. Kada ka ɗauka cewa ka san abin da mutumin yake bukata. Mai yiwuwa, wani abu dabam ne yake damunsa. Don haka, idan wani da yake cikin damuwa yana gaya maka yadda yake ji, ka saurare shi da kyau. Kuma ka yi masa tambayoyin da za su taimaka maka ka san abin da yake bukata.—K. Mag. 20:5.

8. Ta yaya Yesu ya taꞌazantar da Marta da Maryamu bayan mutuwar Liꞌazaru? (Ka kuma duba hotunan.)

8 Ka yi laꞌakari da yadda Yesu ya taꞌazantar da Marta da Maryamu bayan mutuwar ɗanꞌuwansu Liꞌazaru. Ko da yake Marta da Maryamu suna baƙin ciki, Yesu ya taꞌazantar da su a hanyoyi dabam-dabam. Bayan da Marta ta yi magana da Yesu, Yesu ya ƙarfafa ta ta wurin tuna mata game da tashin matattu. Ya kuma taimaka mata ta ƙara gaskatawa da wannan alkawarin da Allah ya yi. Amma saꞌad da Maryamu ta zo wurin Yesu tana kuka, Yesu bai gaya mata kome game da tashin matattu ba. A maimakon haka, Littafi Mai Tsarki ya ce, Yesu ya zub da hawaye. Sai ya ce a nuna masa inda aka binne Liꞌazaru. (Yoh. 11:​20-35) Mene ne hakan ya koya mana? Saꞌad da muke so mu taimaka wa waɗanda suke fama da matsaloli, zai dace mu yi ƙoƙari mu san abin da kowannensu yake bukata. Hakan zai sa mu iya ƙarfafa su da kyau.

Hotuna: Wani dattijo ya ziyarci wasu ꞌyanꞌuwa dabam-dabam da matansu suka mutu. Na 1. Dattijon ya sa hannu a kafaɗar ɗanꞌuwan saꞌad da yake kuka. Na 2. Dattijon yana nuna wa wani ɗanꞌuwa da ya tsufa wani nassi yayin da suke kallon hotuna tare.

Kana bukatar ka fahimci ainihin abin da mutane suke bukata don ka iya ƙarfafa su da kyau (Ka duba sakin layi na 8)a


9. Me ya sa zai dace mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki wajen ƙarfafa mutane? (Romawa 15:​4, 5)

9 Mu yi amfani da Littafi Mai Tsarki. Idan wani yana fama da yanayi mai wuya kuma muka karanta masa wani nassi, hakan zai sa mutumin ya ƙara kasance da bege cewa Jehobah zai cika alkawuran da ya yi. (Karanta Romawa 15:​4, 5.) Ƙari ga haka, kasancewa da bege zai taimaka wa mutumin ya tuna cewa Jehobah yana ƙaunar sa kuma zai taimaka masa. (Isha. 40:31) Ta yaya za ka iya samun nassin da za ka yi amfani da shi wajen ƙarfafa wani? Za ka iya samun talifofi masu ban ƙarfafa a jw.org, sai ka rubuta nassosi masu ban ƙarfafa da ke talifofin. Ƙari ga haka, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka yi amfani da Kalmarsa a hanyar da ta dace wajen ƙarfafa mutane. Ruhu mai tsarki zai iya taimaka maka ka tuna da nassosi masu ban ƙarfafa a lokacin da kake bukata.—Yoh. 14:26.

10. Me ya sa muke bukatar mu yi magana cikin alheri saꞌad da muke ƙarfafa mutane?

10 Mu yi magana cikin alheri. A wasu lokuta, za mu bukaci mu taimaka wa mutumin da muke ƙarfafawa ya kasance da raꞌayin da ya dace game da matsalolinsa. A irin wannan lokacin, zai dace mu yi tunani sosai kafin mu faɗa abin da muke so mu faɗa. Burinmu shi ne mu faɗi abin da zai kwantar wa mutumin da hankali, ba abin da zai sa shi sanyin gwiwa ba. (K. Mag. 12:18) Za mu iya yin koyi da yadda Jehobah ya taimaka wa annabi Iliya. Iliya ya ɗauka cewa shi kaɗai ne ya rage a cikin masu bauta wa Jehobah. Ya kuma ga kamar aikin da ya yi a matsayin annabin Jehobah aikin banza ne. Jehobah ya taimaka wa Iliya ya daina irin tunanin da yake yi ba tare da nuna masa laifinsa ba. (1 Sar. 19:​15-18) Mu ma za mu iya ƙarfafa ꞌyanꞌuwa idan muka yi musu magana cikin alheri, kuma muka yi tunani sosai kafin mu faɗi wani abu. Saꞌad da kake ba da jawabi ko yin kalami a taro, ka yi magana cikin alheri, kuma ka tabbata cewa abin da kake so ka faɗa zai ƙarfafa ꞌyanꞌuwa.

11. Mene ne ꞌyanꞌuwanmu suke bukata idan suna shan wahala? (1 Yohanna 3:18)

11 Mu taimaka musu da abin biyan bukata. Idan ꞌyanꞌuwanmu suna shan wahala muna bukatar mu ƙarfafa su, amma ba shi ke nan ba. Muna kuma bukatar mu taimaka musu da abin biyan bukata. (Karanta 1 Yohanna 3:18.) Alal misali, Barnabas ya sayar da filinsa kuma ya ba wa manzani kuɗin don su yi amfani da shi wajen taimaka wa ꞌyanꞌuwa da suke fama da talauci. (A. M. 4:​36, 37) Kamar Barnabas, ꞌyanꞌuwa maza da mata da yawa a yau suna tallafa wa waɗanda suke da bukata. Alal misali, wata ꞌyarꞌuwa mai suna Gabriela daga ƙasar Poland, ta yi baƙin ciki sosai lokacin da ambaliya ta yi kaca-kaca da gidanta. ꞌYarꞌuwar ta ce: “Tsoro ya kama ni da iyayena, kuma mun damu sosai. Ba mu ma san yadda za mu sake gyara gidanmu ba. Amma a cikin rana ɗaya, ꞌyanꞌuwa a ikilisiyoyin da ke kusa da mu sun zo sun gyara gidanmu. Abin da ya faru ya taimaka mini in ƙara gaskata cewa, Jehobah yana amfani da bayinsa wajen ƙarfafa waɗanda suke fama da matsaloli.”

12. Idan muka riƙe amincinmu ga Jehobah duk da famar da muke yi, ta yaya hakan zai taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu?

12 Mu ci-gaba da riƙe amincinmu ga Jehobah. Saꞌad da Bulus ya ji cewa ꞌyanꞌuwan da ke Tasalonika sun ci-gaba da riƙe amincinsu ga Jehobah duk da tsanantawa, hakan ya ƙarfafa shi sosai. Bulus ya yi iya ƙoƙarinsa wajen taimaka musu su ci-gaba da kasancewa da bangaskiya. Saboda haka, jin cewa sun ci-gaba da riƙe amincinsu ya ƙarfafa shi sosai. (1 Tas. 3:​5-8) Bulus ya san cewa, idan shi ma ya ci-gaba da riƙe amincinsa ga Jehobah, hakan zai ƙarfafa ꞌyanꞌuwan su ma su ci-gaba da riƙe amincinsu ga Jehobah. (Kol. 2:​1, 2) Haka ma, idan ꞌyanꞌuwanmu sun ga cewa mun ci-gaba da riƙe amincinmu ga Jehobah duk da fama da muke yi, hakan zai ƙarfafa su sosai. Ƙari ga haka, za su kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka musu kamar yadda ya taimaka mana.

13. Mene ne muke bukatar mu ci-gaba da yi saꞌad da muke ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu?

13 Mu ci-gaba da yin haƙuri. A wasu lokuta, mai yiwuwa bayan mun yi iya ƙoƙarinmu wajen ƙarfafa mutum, mutumin zai ci-gaba da damuwa. Idan hakan ya faru, zai dace mu tuna da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa, mu riƙa “ƙarfafa juna.” Furucin nan ya nuna cewa abu ne da muke bukatar mu ci-gaba da yi. (1 Tas. 5:11) Saboda haka, saꞌad da muke ƙarfafa ꞌyanꞌuwanmu, zai dace mu yi haƙuri da su. (1 Tas. 5:14) Gaskiyar ita ce, a wasu lokuta dukanmu mukan shiga damuwa kuma mu bukaci ƙarfafa. To, mene ne za mu iya yi a irin wannan lokacin?

ABIN DA ZA KA IYA YI SAꞌAD DA KAKE BUKATAR ƘARFAFA

14-15. Me muke bukatar mu yi idan muna baƙin ciki ko damuwa?

14 Ka yi adduꞌa ga Jehobah. Idan kana baƙin ciki ko damuwa, ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka sami kwanciyar hankali. (Zab. 94:19) Ka gaya wa Jehobah ainihin yadda kake ji a zuciyarka. (Zab. 62:8) Gaskiyar ita ce, Jehobah ya riga ya san yadda kake ji kafin ma ka gaya masa. Amma yayin da kake yin adduꞌa kana nuna cewa ka gaskata yana sauraron ka kuma yana ƙaunar ka. Jehobah yana taimaka wa waɗanda suka ba da gaskiya gare shi kuma suka nemi taimakonsa. (Mar. 11:24) Filibiyawa 4:​6, 7 sun ce: “Ku faɗa wa Allah bukatunku . . . Ta haka kuwa Allah zai ba ku salama iri wadda ta wuce dukan ganewar ɗan Adam, za ta kuma tsare zukatanku da tunaninku.”

15 Ka nemi taimakon wasu. Ka gaya wa wani abokinka ko wani dattijo yadda kake ji a zuciyarka. ꞌYanꞌuwa maza da mata za su iya taimaka maka. Amma ba za su san ainihin abin da kake bukata idan ba ka gaya musu ba. (K. Mag. 14:10) Za ka iya gaya musu su saurare ka da kyau yayin da kake bayyana musu yadda kake ji. Ko kuma ka ce su nuna maka wani nassi ko talifin da zai ƙarfafa ka.

16. Mene ne zai iya faruwa saꞌad da ꞌyanꞌuwa suke ƙarfafa ka, amma me ya kamata ka tuna?

16 Ka yi haƙuri kuma ka riƙa gafartawa. ꞌYanꞌuwa za su iya yin abin da zai iya ɓata maka rai yayin da suke ƙoƙarin ƙarfafa ka. Za su iya yi ko faɗa abin da zai iya sa yanayinka ya ƙara muni. Idan hakan ya faru, ka yi haƙuri da su. (1 Kor. 13:​4, 7) Yaƙub 3:2 ta ce: “Idan kuwa wani ba ya kuskure a maganarsa, to, lallai shi cikakke ne.” Ka tuna cewa abin da ꞌyanꞌuwa suke so shi ne su taimaka maka. Amma kamar yadda kai ma kake yi a wasu lokuta, ꞌyanꞌuwa sukan yi kuskure ko da suna da niyyar yin abu mai kyau.—Mat. 26:41.

17. Mene ne za mu ƙudiri niyyar yi?

17 Dukanmu muna bukatar ƙarfafa domin muna rayuwa a kwanakin ƙarshe. Abubuwa suna ƙara wuya kuma maƙiyanmu suna ƙara tsananta mana. Saboda haka, bari mu ci-gaba da yin iya ƙoƙarinmu wajen ƙarfafa juna.

MECE CE AMSARKA?

  • Mene ne kalmar nan “ƙarfafa” take nufi a Littafi Mai Tsarki?

  • Waɗanne abubuwa ne muke bukatar mu yi don mu ƙarfafa mutane?

  • Waɗanne abubuwa ne za ka iya yi saꞌad da kake bukatar ƙarfafa?

WAƘA TA 130 Mu Riƙa Gafartawa

a BAYANI A KAN HOTO: Wani dattijo yana sauraron wani ɗanꞌuwa da bai daɗe da matarsa ta mutu ba. Daga baya, dattijon ya ziyarci wani ɗanꞌuwa da matarsa ta yi shekaru da mutuwa. Kuma suna magana game da abubuwan da ba za su taɓa mantawa ba game da ꞌyarꞌuwar.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba