SHAWARA A KAN YIN NAZARI
Yadda Za Mu Iya Fahimtar Kwatanci da Dama da Ke Littafi Mai Tsarki
Sau da yawa Littafi Mai Tsarki yakan yi amfani da kwatanci wajen bayyana abubuwa. (Mat. 13:13) Mene ne zai taimaka mana mu iya fahimtar kwatancin da ke Littafi Mai Tsarki? Abubuwan da aka ambata a gaba za su iya taimaka mana:
Ka gane abin da ake magana a kai da kwatancin da aka yi. Alal misali, a Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 3:3, an kwatanta zuwan Yesu da zuwan ɓarawo. Abin da ake magana a kai shi ne zuwan Yesu, kuma an kwatanta shi da zuwan ɓarawo.
Ka yi tunani a kan alaƙar da ke tsakanin batun da kwatancin da aka yi. Ka yi ƙoƙari ka fahimci alaƙar da ke tsakanin abin da ake magana a kai da kuma kwatancin da aka yi.
Ka tabbata cewa ka fahimci gaskiyar batun. A wasu lokuta, mutum zai iya yi wa kwatancin da aka yi bahaguwar fahimta. Alal misali, a kwatancin da aka yi a Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 3:3 da aka ambata ɗazu, Yesu zai zo ba don ya saci wani abu ba. A maimakon haka, Yesu zai zo ne a lokacin da mutane ba su yi tsammani ba kamar yadda ɓarawo yake yi.