Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Maris pp. 14-19
  • Kada Ka Manta da Abin da Ya Fi Muhimmanci a Rayuwarka

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kada Ka Manta da Abin da Ya Fi Muhimmanci a Rayuwarka
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • WAƊANNE ABUBUWA NE ZA SU IYA JANYE HANKALINMU?
  • MENE NE YESU YA YI DON YA SA BAUTAR JEHOBAH FARKO A RAYUWARSA?
  • YADDA ZA MU GUJE WA ABUBUWAN DA ZA SU JANYE HANKALINMU DAGA IBADARMU
  • Ku Tsai da Shawarwari da Za Su Nuna Kun Dogara Ga Jehobah
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2023
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ka Nemi Amsoshin Waɗannan Tambayoyin
    Tsarin Ayyuka na Taron Daꞌira na Mai Kula da Daꞌira na 2026
  • Ka Nemi Amsoshin Waɗannan Tambayoyin
    Tsarin Ayyuka na Taron Daꞌira da Wakilin Reshen Ofishinmu na 2026
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Maris pp. 14-19

18-24 GA MAYU, 2026

WAƘA TA 35 Mu Riƙa Yin “Abin da Ya Fi Kyau”

Kada Ka Manta da Abin da Ya Fi Muhimmanci a Rayuwarka

“Ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji.”—AFIS. 5:17.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga yadda za mu nuna cewa ayyukan ibada ne suka fi muhimmanci a rayuwarmu ko da akwai wasu abubuwan da suke janye hankalinmu.

1-2. Ta yaya wani abu mai muhimmanci zai iya janye hankalinmu?

A CE kana tuƙi, sai wani ya soma kiranka a waya, za ka iya tunani cewa wani yana bukatar taimakonka. Amma a lokacin, ka san cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne ka mai da hankali a kan tuƙin da kake yi. A yau ma, muna da abubuwa da yawa masu muhimmanci da muke bukatar mu yi, kuma wajibi ne mu zaɓi wanda ya fi muhimmanci.

2 Dukanmu muna da abubuwa da yawa masu muhimmanci da ya kamata mu yi. Amma mun san cewa mai da hankali ga ayyukan ibadarmua ne ya fi muhimmanci. (Mat. 6:33) Shi ya sa bayin Jehobah a yau suna iya ƙoƙarinsu wajen guje wa abubuwan da za su iya janye hankalinsu daga yin abin da ya fi muhimmanci.—K. Mag. 4:25; Mat. 6:22.

3. Me za mu tattauna a wannan talifin?

3 A gaskiya, babu waninmu da zai so wani abu ya janye hankalinsa daga ayyukan ibada. Duk da haka, dukanmu muna fama da yanayoyin da za su iya janye hankalinmu. (Luk. 21:​34-36) Don mu ga yadda za mu mai da hankali a bautarmu ga Jehobah, za mu tattauna (1) abubuwan da za su iya janye hankalinmu, (2) abin da Yesu ya yi don ya guje wa abubuwan da za su iya janye hankalinsa daga bautarsa ga Jehobah, da kuma (3) yadda za mu guje wa abubuwan da za su iya janye hankalinmu daga bautarmu ga Jehobah.

WAƊANNE ABUBUWA NE ZA SU IYA JANYE HANKALINMU?

4-6. Waɗanne abubuwa ne za su iya janye hankalinmu?

4 Dukanmu muna da abubuwa da yawa a rayuwarmu da suke da muhimmanci sosai. Alal misali, wataƙila muna fama da rashin lafiya, ko kuma akwai wasu abubuwa da muke bukata mu kula da su a iyalinmu ko a rayuwarmu. Abubuwan nan suna da muhimmanci, kuma muna bukatar mu mai da hankali a kan su. Amma za su iya janye hankalinmu. Hakan zai iya faruwa idan muna yawan tunani a kan su har mu gagara samun lokaci da ƙarfin yin wani abu.

5 Da yawa cikinmu na zama a inda ake fama da tashe-tashen hankula, ko taɓarɓarewar tattalin arziki, ko kuma ɓarkewar cututtuka masu yaɗuwa. (2 Tim. 3:1) Idan muna fama da irin abubuwan nan, za mu iya damuwa sosai har mu yi ta tunani a kansu koyaushe.

6 Mai yiwuwa mun san mutanen da suka yi fama da irin abubuwan nan har rayuwarsu ta taɓarɓare. Babu shakka, hakan zai iya sa su baƙin ciki sosai. Gaskiyar ita ce, Jehobah bai halicci ꞌyanꞌadam su riƙa yawan damuwa ko shan wahala ba. Wasu mutane suna ganin kamar ba za su taɓa iya yin rayuwa yadda suke so ba. Shi ya sa wasu suke yawan yin nishaɗi da shaƙatawa don su mance da matsalolinsu. Me za mu yi idan muka sami kanmu a irin yanayoyin nan? Bari mu ga abubuwan da Yesu ya yi da za su taimaka mana mu guji abubuwan da za su iya janye hankalinmu daga ibadarmu ga Jehobah.

MENE NE YESU YA YI DON YA SA BAUTAR JEHOBAH FARKO A RAYUWARSA?

7. A lokacin da Yesu yake duniya, waɗanne abubuwa ne za su iya janye hankalinsa?

7 Wasu abubuwan da za su iya janye hankalin Yesu su ne, matsalolin da mutane suke fama da su, da kuma na siyasa. Alal misali, a zamaninsu, mutane da yawa suna fama da rashin lafiya da kuma talauci. (Mat. 14:14; Mar. 14:7) Kuma sun yi fama da rashin adalci daga wurin Romawa da kuma ꞌyanꞌuwansu Yahudawa. Saꞌad da mutane suka ga cewa Yesu yana da ikon yin abubuwa masu ban mamaki, sun so ya zama sarkinsu. (Yoh. 6:​14, 15) Ban da haka, Shaiɗan ya gaya wa Yesu cewa zai ba shi dukan mulkokin duniya. Da Yesu ya so, da zai soma tunani a kan abubuwan da zai samu idan ya zama mai mulkin duniya. (Mat. 4:​8, 9) Ƙari ga haka, a lokacin da Yesu ya gaya wa almajiransa wahalar da zai sha, Bitrus ya gaya masa cewa, “kada ka yi wa kanka irin wannan fatan.” Wannan shawarar za ta iya sa Yesu ya so yin rayuwar da ba zai sha wahala ba.—Mat. 16:​21, 22.

8. Waɗanne abubuwa ne suka taimaka wa Yesu ya ci-gaba da sa bautar Jehobah farko a rayuwarsa?

8 Waɗanne abubuwa ne suka taimaka wa Yesu ya ci-gaba da sa bautar Jehobah farko a rayuwarsa? Na ɗaya, ya kasance da raꞌayin Jehobah. (Yoh. 8:28; 14:9) Na biyu, ya mai da hankali a kan aikin waꞌazi da koyar da mutane. (Mat. 9:35) Na uku, ya san ainihin abubuwan da suka fi muhimmanci. (Yoh. 4:34) Ya ƙi ya yi abin da Shaiɗan ya gaya masa. Kuma ko da yake Bitrus yana masa fatan alheri ne, ya san cewa abin da ya faɗa bai jitu da nufin Jehobah ba. (Mat. 4:10; 16:23) Yesu bai bar abubuwan da mutane suka faɗa, ko raꞌayinsu, ko abubuwan da suka yi masa su janye hankalinsa daga yin abubuwan da Jehobah yake so ya yi ba. A yau, za mu iya fama da wasu abubuwan da za su janye hankalinmu daga bautar Jehobah, da ba iri ɗaya ba ne da wanda Yesu ya fuskanta. Amma idan muka yi abubuwa ukun nan da Yesu ya yi, za mu ci-gaba da sa bautar Jehobah farko a rayuwarmu.

YADDA ZA MU GUJE WA ABUBUWAN DA ZA SU JANYE HANKALINMU DAGA IBADARMU

9. Mene ne Afisawa 5:17 ta gaya mana mu yi?

9 Mu kasance da raꞌayin Jehobah. Yin hakan zai taimaka mana mu san abin da za mu yi don mu faranta wa Jehobah rai. (Karanta Afisawa 5:17.) Za mu iya sanin abubuwan da Jehobah yake so ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki da yin tunani a kai. Za mu iya sanin abin da Jehobah yake so mu yi a kan wani batu ko da Littafi Mai Tsarki bai yi magana kai tsaye game da batun ba. Ta yaya za mu iya yin hakan? Ta yin nazarin Littafi Mai Tsarki don mu san raꞌayin Jehobah, kuma mu yi niyyar yin abin da muka koya.

10. Ta yaya za mu iya sanin raꞌayin Jehobah?

10 Za mu iya sanin raꞌayin Jehobah ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki, da kuma yin laꞌakari da yadda ya bi da mutane. (Irm. 45:5) Yayin da muke karanta labaran, zai dace mu yi wa kanmu tambayoyi kamar: ‘Mene ne labarin ya koya mini game da Jehobah? Mene ne nake bukatar in yi don in riƙa ganin abubuwa yadda Jehobah yake ganin su?’ Gaskiyar ita ce, mun san cewa Jehobah ya fi mu hikima sosai. (Isha. 55:9) Saboda haka, wajibi ne mu roƙe shi ya taimaka mana mu iya yin nufinsa. (Zab. 143:10) Kuma mu roƙe shi ya taimaka mana mu kasance da raꞌayinsa.—1 Yoh. 5:14.

11. Mene ne Jehobah ba ya so mu yi?

11 Jehobah yana so mu kasance a shirye kafin ƙarshen zamanin nan ya zo. Shi ya sa ba ya so wani abu ya janye hankalinmu daga abubuwan da suka fi muhimmanci. (Mat. 24:44) Ba ya so mu riƙa yawan damuwa a kan abubuwa har mu soma yin baƙin ciki. (Mat. 6:​31, 32) Shi ya sa Jehobah yake ba mu shawarwari masu kyau don mu san abin da za mu yi idan muka soma damuwa game da lafiyarmu ko aikinmu ko gidan da za mu zauna ko kuma iyalinmu. Ya yi alkawari cewa zai ba mu hikima da kuma ƙarfin jimre matsalolinmu.—Zab. 55:22; K. Mag. 3:​5-7.

12. Me zai taimaka mana mu rage yawan damuwa game da abubuwan da suke faruwa a duniya? (Matiyu 5:3)

12 Mu mai da hankali a kan ayyukan ibada. Dukanmu muna damuwa a kan munanan abubuwan da suke faruwa a duniya, kuma ba abin da za mu iya yi a kai. Saboda haka, idan muka ci-gaba da yin ayyukan ibadarmu, hakan zai taimaka mana mu rage damuwa a kan abubuwan da suke faruwa. Jehobah ya halicce mu yadda za mu riƙa marmarin so mu kusace shi. Idan muka ci-gaba da yin abubuwan da za su sa mu kusaci Jehobah, hakan zai sa mu yi farin ciki. (Karanta Matiyu 5:3.) Za mu iya yin hakan ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki, da kuma yin iya ƙoƙarinmu a hidimarmu ga Jehobah. Hakan zai sa Jehobah farin ciki, kuma zai nuna cewa muna amfani da lokacinmu yadda ya dace.—K. Mag. 23:15.

13. Ta yaya za mu nuna cewa muna amfani da ‘lokacinmu da kyau’?

13 Littafi Mai Tsarki ya ce mu riƙa amfani da ‘lokacinmu da kyau.’ (Afis. 5:​15, 16, NWT) Ba game da yadda muke amfani da lokacinmu a ayyukanmu mu ne kawai ayoyin nan suke magana ba. Suna kuma taimaka mana mu yi tunani sosai a kan yadda muke amfani da lokacinmu kafin ƙarshen duniyar nan ya zo. Ta yaya za mu yi amfani da lokacinmu da kyau? Idan muna yawan mai da hankali a kan labarai marasa daɗi da ake watsawa kowace rana, hakan zai iya sa mu karaya, kuma mu rage ƙwazo a bautarmu ga Jehobah. Zai fi kyau mu rage lokacin da muke karanta, ko sauraro, ko kuma kallon labaran. Yin hakan zai sa mu sami lokaci da kuma ƙarfin yin abubuwa a ibadarmu ga Jehobah. Zai kuma dace mu ƙara ƙwazo a waꞌazi da kuma yawan mutanen da muke nazari da su. Mun san cewa zai dace mu yi amfani da duk wata dama da muka samu wajen taimaka wa mutane su “kai ga sanin gaskiya” kuma su sami ceto.—1 Tim. 2:4.

14. Ta yaya za mu amfana idan muka ci-gaba da mai da hankali a kan ayyukan ibadarmu? (Ka kuma duba hoton.)

14 Idan muka mai da hankali a kan ayyukan ibadarmu, hakan zai taimaka mana mu riƙa tuna dalilin da ya sa munanan abubuwa suke faruwa a duniya. Yayin da muke ganin tashe-tashen hankula, da taɓarɓarewar tattalin arziki, da kuma ɓarkewar cututtuka masu yaɗuwa, ba ma tsoro domin mun san cikar annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki ne. Nan ba da daɗewa ba, Jehobah zai kawo ƙarshen abubuwan nan kuma ya sa duniya ta zama Aljanna. Kafin wannan lokacin, mun san cewa Jehobah zai taimaka mana mu jimre kuma hakan yana kwantar mana da hankali.—Zab. 16:8; 112:​1, 6-8.

Wani ɗanꞌuwa da matarsa suna tafiya babu tsoro suna jan amalanken waꞌazi. Hotuna: A bayansu akwai hotuna da ke nuna abubuwan da ke ta da hankalin mutane a duniya. Na 1. Masu zanga-zanga. Na 2. ꞌYan takara guda biyu. Na 3. Sojoji a bakin daga. Na 4. Magunguna. Na 5. Hoton da ke nuna yadda arzikin wani kamfani yake taɓarɓarewa.

Mu ci-gaba da yin ayyukan ibada da ƙwazo ko da munanan abubuwa da yawa suna faruwa a duniya (Ka duba sakin layi na 14)b


15. Bisa ga 1 Bitrus 4:​7, mene ne ya kamata mu yi, kuma me ya sa?

15 Mu riƙa tuna da abin da ya fi muhimmanci. Yawancin mutane a yau suna yawan mai da hankali a kan jin daɗi, kuma ba su damu cewa ƙarshen duniyar nan ya yi kusa ba. Ko da yake jin daɗi da shaƙatawa ba laifi ba ne, zai dace mu guji tunani irin na mutanen duniyar nan. Mene ne zai taimaka mana? Muna bukatar mu “natsu.” (Karanta 1 Bitrus 4:7.) Mene ne hakan yake nufi? Hakan yana nufin yin tunanin da ya dace don kada mu ɓata lokaci muna jin daɗi kawai. Yin irin wannan tunanin ya jitu da raꞌayin Jehobah, kuma zai nuna cewa mun san abin da ya fi muhimmanci.—2 Tim. 1:7.

16. Mene ne za mu iya koya daga abin da Yesu ya yi kafin ya mutu?

16 Yesu bai manta da abin da ya fi muhimmanci a rayuwa ba. Har lokacin da zai mutu, ya san cewa abin da ya fi muhimmanci shi ne riƙe aminci ga Jehobah da kuma yin nufinsa. Don haka, ya yi adduꞌa sosai da dukan zuciyarsa. Amma almajiransa ba su yi hakan ba. Maimakon su yi adduꞌa, sun yi barci. “Domin baƙin ciki da suke ciki ya gajiyar da su.”—Luk. 22:​39-46; Yoh. 19:30.

17. Me ya sa mutane da yawa suke amfani da dandalin sada zumunta, kuma ta yaya hakan zai iya shafan su? (Ka kuma duba hoton.)

17 Kamar almajiran Yesu, baƙin ciki zai iya sa mu damuwa har ya gajiyar da mu. Abubuwan da suke faruwa a wannan lokacin za su iya sa mu damuwa sosai. Mutane da yawa a yau suna yawan amfani da dandalin sada zumunta don su iya mance da matsalolinsu. Suna amfani da shi wajen tura wa abokansu da danginsu da ke wurare dabam-dabam a faɗin duniya hotuna, da saƙonni da dai sauransu. Kuma suna amfani da shi wajen kallon bidiyoyi da yawa da kuma buga wasanni. Amma da yake abubuwan da ake kallo da kuma karantawa a dandalin sada zumunta ba su da iyaka, suna cin lokaci kuma suna gajiyar da mutane da yawa. Don kada mu ma mu faɗa a cikin irin wannan yanayin, zai dace mu tambayi kanmu: ‘Shin abubuwan da nake kallo da kuma yi a dandalin sada zumunta suna ƙarfafa ni kuwa, ko suna janye hankalina daga abubuwan da suka fi muhimmanci?’

Wata ꞌyarꞌuwa zaune a ɗakinta tana so ta karanta Littafi Mai Tsarki. Amma akwai saƙonni daga manhajoji dabam-dabam da suke janye hankalinta.

Zai dace mu yi hattara don kada dandalin sada zumunta da nishaɗi da shaƙatawa su janye hankalinmu daga abubuwan da suka fi muhimmanci (Ka duba sakin layi na 17)


18. Me ya sa muke bukatar mu mai da hankali sosai saꞌad da muke zaɓan irin nishaɗin da za mu yi?

18 Saꞌad da muke kallon bidiyoyi masu tsayi, ko gajerun bidiyoyi, ko kuma buga wasanni a intane, bai kamata mu wuce gona da iri ba. Ko da yake yin abubuwan nan za su iya sa mu wartsake kuma mu ji daɗi. Amma zai dace mu yi tunani a kan yawan lokacin da muke amfani da shi, da kuma irin abubuwan da muke kallo. A yawancin lokuta, bayan mutum ya gama kallon wani bidiyo, wani kuma zai ɓullo. Kuma idan mutumin bai mai da hankali ba zai ci-gaba da kallo. Wasu bidiyoyin da suke ɓullowa za su iya nuna lalata da mugunta. Abin da ya faru da wani ɗanꞌuwa a Asiya ke nan. Ya soma da kallon soma taɓi na wasu bidiyoyi a intane. Da ya gama kallo sai wasu kuma suka ɓullo. Kafin ya sani, ya soma kallon bidiyoyin da ake lalata. A kwana a tashi, sai ya soma kallon bidiyoyin batsa. Amma abin farin cikin shi ne da taimakon dattawa da kuma abokansa, ya daina. Ya ciccire manhajojin da yake kallon bidiyoyin da su. Kuma ya rage yawan lokacin da yake amfani da wayarsa. Wannan labarin ya nuna mana cewa muna bukatar mu mai da hankali sosai a kan yadda muke amfani da lokacinmu.

19. Me zai iya faruwa idan muna mai da hankali a kan jin daɗi da shaƙatawa?

19 Muna kuma bukatar mu yi tunani sosai saꞌad da muke shaƙatawa ko kuma yawon buɗe ido. Dukanmu muna bukatar mu huta kuma mu ɗan shaƙata. Hakan yakan inganta lafiyar jikinmu. Amma idan muna yawan mai da hankali a kan shaƙatawa kawai, hakan zai iya cinye mana lokacin yin abubuwan da suka fi muhimmanci. (Filib. 1:10) Saꞌad da muke tunanin shaƙatawa ko kuma yawon buɗe ido, zai dace mu tambayi kanmu cewa: ‘Yawan lokacin da nake yawon buɗe ido ko kuma shaƙatawa yana nuna cewa na san abin da ya fi muhimmanci kuwa? Abubuwan da nake yi suna nuna cewa na san “ƙarshen dukan abu ya yi kusa”?’

20. Ta yaya za mu amfana idan muka guji duk wani abin da zai iya janye hankalinmu daga ayyukan ibadarmu?

20 Za mu amfana sosai idan muka guji duk wani abin da zai iya janye hankalinmu daga ayyukan ibadarmu. (Isha. 48:17) Da taimakon Jehobah za mu iya jimre matsalolin da muke fuskanta. Ba za mu damu sosai don abubuwan da suke faruwa a duniya ba. Kuma za mu guji sa yawan jin daɗi da shaƙatawa su zama abu mafi muhimmanci a rayuwarmu. Saboda haka, bari mu ci-gaba da kasancewa da raꞌayin Jehobah, mu ƙara ƙwazo a ayyukan ibadarmu, kuma a kullum mu riƙa tuna da abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwarmu. Yin hakan zai sa mu riƙa sa bautar Jehobah farko a rayuwarmu. Kuma a nan gaba, za mu sami rai na har abada.—1 Tim. 6:19.

DON MU IYA SA BAUTAR JEHOBAH FARKO A RAYUWARMU, ME YA SA YAKE DA MUHIMMANCI MU CI-GABA DA . . .

  • kasancewa da raꞌayin Jehobah?

  • yin ayyukan ibadarmu?

  • mai da hankali a kan abubuwan da suka fi muhimmanci a rayuwarmu?

WAƘA TA 129 Za Mu Riƙa Jimrewa

a MAꞌANAR WASU KALMOMI: Ayyukan ibadarmu su ne duk wani abin da ke da alaƙa da bautarmu ga Jehobah. Sun ƙunshi yin nazarin Littafi Mai Tsarki, da halartan taro, da yin ibada ta iyali, da kuma yin waꞌazi. Sun kuma ƙunshi gina da kula da wuraren ibada, da aikin agaji, da yin ayyuka dabam-dabam a taron yanki da kuma yin hidima a Bethel.

b BAYANI A KAN HOTO: Wani ɗanꞌuwa da matarsa sun ci-gaba da yin waꞌazin Mulkin Allah da ƙwazo, maimakon su mai da hankali a kan abubuwan da ke ta da hankalin mutane a duniya.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba