Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Maris pp. 20-25
  • Ka Yi Tunani Sosai Kafin Ka Ɗau Mataki

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yi Tunani Sosai Kafin Ka Ɗau Mataki
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • KA ZAMA MAI SAUƘIN KAI MAIMAKON GIRMAN KAI
  • KA KAME KANKA MAIMAKON SAURIN FUSHI
  • KA DOGARA GA JEHOBAH MAIMAKON KA JI TSORO
  • KA CI-GABA DA ƘOƘARIN ZAMA DA RAꞌAYIN JEHOBAH
  • Wani Mayaki da Kuma Wata Yarinya
    Darussa daga Littafi Mai Tsarki
  • Ta So Ta Yi Taimako
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Ya Yi Taurin Kai Amma Daga Baya Ya Yi Biyayya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Yarinya Ta Taimaki Jarumi
    Littafina na Labarun Littafi Mai Tsarki
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Maris pp. 20-25

25-31 GA MAYU, 2026

WAƘA TA 135 Jehobah Ya Ce: “Ɗana Ka Yi Hikima”

Ka Yi Tunani Sosai Kafin Ka Ɗau Mataki

“Wanda ya mai da hankali . . . zai yalwata.”—K. MAG. 16:20.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga cewa yin tunani sosai kafin mu ɗau mataki zai taimaka mana mu yi abin da ya dace a yanayi mai wuya.

1-2. Wace shawara ce Littafi Mai Tsarki ya ba mu, kuma ta yaya shawarar za ta taimaka mana?

SHIN, wani ya taɓa yi maka magana sai ka ji kamar bai girmama ka ba? Ka taɓa ji kamar wani bai fahimce ka ba, kuma ya yi abin da ya ɓata maka rai? Ko kuma ka taɓa fuskantar wani yanayi mai wuya da ya tsorata ka? A irin yanayoyin nan, ba zai yi wa mutum sauƙi ya faɗa ko ya yi abin da ya dace ba. To, mene ne zai iya taimaka mana? Littafi Mai Tsarki ya ba mu shawarwari a kan abubuwan da za mu iya yi.

2 Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa mu mu riƙa yin tunani kafin mu yi wani abu. Hakan yana nufin cewa za mu yi ƙoƙari mu san dalilin da ya sa wani abu ya faru. Ko kuma dalilin da ya sa wani ya yi abin da ya yi. Yin hakan zai sa mu yi abin da ya dace. Kuma zai taimaka mana mu iya “kame bakinmu” kuma mu san lokacin da ya kamata mu yi “shiru.” (K. Mag. 10:19; Zab. 4:4) Zai taimaka mana kada mu yi saurin fushi idan wasu suka ɓata mana rai. Kuma zai taimaka mana mu amince da duk wata shawara ko gyara da aka yi mana. (K. Mag. 19:20) Idan ba mu yi tunani sosai ba saꞌad da wani ya ɓata mana rai, hakan zai sa mu yi fushi, kuma mu mayar da martani a hanyar da ba ta dace ba. Amma idan muka yi tunani sosai kafin mu ɗau mataki, za mu amfana, za mu sa mutane farin ciki, kuma Jehobah zai yi farin ciki sosai. Bari mu tattauna labarai uku a Littafi Mai Tsarki da suka nuna yadda yin tunani kafin mu yi wani abu zai taimaka mana mu kasance da sauƙin kai, kada mu riƙa saurin fushi, kuma mu riƙa dogara ga Jehobah.

KA ZAMA MAI SAUƘIN KAI MAIMAKON GIRMAN KAI

3. Waye ne Naꞌaman?

3 Idan muna so mu yi abin da ya dace, dole ne mu guji girman kai. (1 Bit. 5:5) Yin tunani kafin mu yi wani abu zai taimaka mana. Me ya sa muka ce hakan? Bari mu yi laꞌakari da labarin Naꞌaman. Shi ne shugaban sojojin Suriya, wata ƙasa da ke kusa da Israꞌila. Amma yana fama da wata cuta mai tsanani, wato kuturta.—2 Sar. 5:1.

4. Mene ne Naꞌaman ya yi saꞌad da wata ꞌyar yarinya ta kawo wata shawara mai kyau?

4 Matar Naꞌaman tana da wata baiwa ꞌyar Israꞌila. Yarinyar ta gaya mata cewa maigidanta zai iya warkewa idan ya je wurin wani annabi a Israꞌila. (2 Sar. 5:​2, 3) Da Naꞌaman ya so da ya yi tunani cewa, ‘Wannan ƙaramar yarinyar da ta zo daga ƙasar maƙiyanmu, za ta iya kawo wata shawara mai amfani kuwa?’ Amma Naꞌaman bai yi hakan ba. A maimakon haka, ya nuna sauƙin kai, kuma ya bi shawarar da ta bayar. Ya nemi izini daga wurin sarkin Suriya don ya je Israꞌila a warkar da shi.—2 Sar. 5:​4, 5.

5. Me ya faru saꞌad da Naꞌaman ya je Israꞌila?

5 Naꞌaman ya je fadar Sarki Jehoram da fatan cewa za a warkar da shi. Amma Jehoram ya ɗauka cewa sarkin Suriya yana neman shi da faɗa ne shi ya sa ya turo Naꞌaman wurinsa. Saꞌad da annabi Elisha ya ji abin da ya faru, sai ya ce a Jehoram ya turo Naꞌaman wurinsa. (2 Sar. 5:​6-9) Amma Elisha bai yi abin da Naꞌaman ya yi tsammani zai yi ba. Elisha bai ma fito daga gidansa don ya marabci Naꞌaman ko ya yi masa magana ba. A maimakon haka, ya tura wani ya je ya gaya masa abin da zai yi don ya warke.—2 Sar. 5:10.

6. (a) Me ya sa wataƙila Naꞌaman ya ƙi bin abin da aka gaya masa da farko? (b) Ta yaya bayin Naꞌaman suka taimaka masa, kuma mene ne sakamakon? (2 Sarakuna 5:​13, 14)

6 Da farko, Naꞌaman bai so ya yi abin da mutumin da Elisha ya turo ya gaya masa ya yi ba. “Sai ya juya da fushi ya tafi.” (2 Sar. 5:​11, 12) Me ya sa? Mai yiwuwa ya ɗauka cewa ya kamata Elisha ya daraja shi sosai a matsayinsa na shugaban sojojin Suriya. Ƙari ga hakan, mai yiwuwa Naꞌaman ya ga kamar Elisha ya rena ƙasar Suriya. Don haka, ya yanke shawarar zai koma gida ba tare da an warkar da shi ba. Amma bayin Naꞌaman sun fahimci cewa annabin yana da niyyar warkar da shi da gaske. Sai suka roƙi Naꞌaman ya yi tunani sosai kafin ya ɗau mataki. A ƙarshe, Naꞌaman ya ƙaskantar da kansa, kuma ya bi umurnin da Elisha ya ba shi. A sakamakon hakan, ya warke!—Karanta 2 Sarakuna 5:​13, 14.

7. Mene ne za mu iya koya daga labarin Naꞌaman? (Karin Magana 22:4) (Ka kuma duba hotunan.)

7 Mene ne za mu iya koya daga wannan labarin? A wasu lokuta, za mu iya kasancewa da raꞌayin da ba daidai ba game da wani batu. Shi ya sa zai dace mu yi tunani sosai kafin mu yi wani abu. Bai kamata mu bar yadda muke ji a zuciyarmu ya shafi abubuwan da muke yi ba. Ƙari ga haka, muna bukatar mu zama masu sauƙin kai. Mutum mai sauƙin kai ya san cewa akwai abubuwan da bai sani ba. Ban da haka, a wasu lokuta muna bukatar wasu su taimaka mana mu fahimci wani yanayi da kyau. Kuma Jehobah ne zai fi taimaka mana mu yi hakan. Duk da cewa Naꞌaman ba ya bauta wa Jehobah, ya nuna sauƙin kai kuma ya saurari baiwar matarsa da kuma bayinsa. Mafi muhimmanci ma, ya saurari annabin Jehobah, wato Elisha. Naꞌaman ya ajiye girman kansa a gefe. Hakan ya sa ya yanke shawarar da ta dace kuma ya warke daga cutarsa. Mu ma a yau, kafin mu faɗa ko mu yi wani abu, zai dace mu ɗan dakata mu yi tunani. Alal misali, a ce wani ya ba mu shawara daga Littafi Mai Tsarki kuma ba mu yarda da shawarar ba, zai dace mu ɗan dakata mu yi tunani sosai. Domin abin da muke so mu yi ko faɗa, zai iya nuna ko muna da sauƙin kai ko girman kai.—Karanta Karin Magana 22:4.

Hotuna: Wani ɗanꞌuwa ya nuna sauƙin kai ta warin saurarawa da kyau saꞌad da wasu suke magana. Na 1. Yana saurarawa yayin da wani ɗanꞌuwa yana nuna masa wata shawarar da ke ƙasidar “Ka Mai da Hankali Ga Karatu da Kuma Koyarwa.” Na 2. Yana saurarawa yayin da wata ꞌyarꞌuwa da ta tsufa take gaya masa wani abu game da shirin da aka yi na yin waꞌazi da amalanke. Na 3. Yana saurarawa yayin da yake kallon shirin Tashar JW a wayarsa.

Kamar yadda Naꞌaman ya nuna sauƙin kai kuma ya saurari shawarar da aka ba shi, zai dace mu ma mu saurara saꞌad da aka yi mana gyara, saꞌad da wasu suke gaya mana game da wani damuwa, ko kuma saꞌad da ƙungiyar Jehobah ta ba da wani umurni (Ka duba sakin layi na 7)


KA KAME KANKA MAIMAKON SAURIN FUSHI

8. A wane yanayi ne zai iya mana wuya mu kame kanmu?

8 A wasu lokuta, abubuwa za su iya faruwa da za su iya ɓata mana rai sosai. Amma idan muka ɗan dakata, muka kuma yi tunani kafin mu faɗa ko mu yi wani abu, hakan zai taimaka mana mu kame kanmu. Gaskiyar ita ce, yin hakan ba ya cika yin sauƙi, musamman idan wani ya yi mana abin da bai dace ba. (Afis. 4:26) Bari mu yi laꞌakari da yadda Dauda da Abigail suka nuna basira a wani yanayi mai wuya.

9. Mene ne Nabal ya yi wa Dauda?

9 Lokacin da Shawulu yake so ya kashe Dauda, Dauda da mutanensa sun gudu zuwa dajin Faran. (1 Sam. 25:1) Saꞌad da suke wurin, sun taimaka wajen kāre makiyaya da kuma tumakin wani attajiri mai suna Nabal. (1 Sam. 25:​15, 16) Saꞌad da bayin Nabal suke yi wa tumakinsa aski, Dauda ya tura mutanensa su je su roƙi Nabal abinci. Sai suka je suka sami Nabal suka yi masa magana cikin ladabi da ban girma. (1 Sam. 25:​6-8) Amma Nabal ya nuna rashin godiya don abin da Dauda da mutanensa suka yi masa. Ya ƙi ya ba su abinci, har ma ya zazzagi Dauda da mutanensa.—1 Sam. 25:​10, 11.

10. Mene ne ya taimaka wa Dauda da Abigail su iya yin abin da ya dace? (1 Samaꞌila 25:​32, 33) (Ka kuma duba hoton.)

10 Da a ce kai ne Dauda, yaya za ka ji? Babu shakka za ka yi fushi sosai kamar yadda Dauda ya yi. Dauda ya yi fushi sosai har ya yi niyyar kashe Nabal! (1 Sam. 25:​13, 21, 22) Dauda da sojojinsa suna hanyar zuwa wurin Nabal ke nan lokacin da Abigail matar Nabal ta same su. Me ya sa ta yi hakan? Ta san cewa ko da yake Dauda ya yi fushi, shi mutumin kirki ne. Don haka, ta yi iya ƙoƙarinta don ta sa ya daina fushi kuma ya kame kansa. Ta kawo masa kyaututtuka da yawa kuma ta ba shi shawara mai kyau. (1 Sam. 25:​18, 23-31) Dauda ya yi tunani a kan shawarar da ta ba shi, kuma ya fahimci cewa abin da ta faɗa ya jitu da raꞌayin Jehobah. Hakan ya sa Dauda ya daina fushi kuma bai yi babban kuskure ba.—Karanta 1 Samaꞌila 25:​32, 33.

Dauda yana sauraron Abigail da kyau yayin da ta durƙusa tana roƙon sa. Mutanen Dauda suna tsaye suna kallon abin da ke faruwa. Bayin Abigail suna tsaye a bayanta riƙe da kyaututtuka da yawa.

Da yake Dauda da Abigail sun yi tunani sosai, hakan ya sa sun yi abin da ya dace kuma Dauda bai aikata wani mummunar abu ba (Ka duba sakin layi na 10)


11. Ta yaya yin tunani kafin mu ɗau mataki zai taimaka mana saꞌad da wani ya yi abin da ya sa mu fushi? (Karin Magana 19:11)

11 Mene ne za mu iya koya daga wannan labarin? Ko da muna da ƙwararren hujjar yin fushi, muna bukatar mu ɗan dakata mu yi tunani. Yin hakan zai iya taimaka mana mu iya kame kanmu, kuma mu yi abin da ya dace. Wani abu kuma da zai taimaka mana mu iya kame kanmu kuma mu yanke shawarar da ta dace shi ne tuna cewa, yin abu cikin fushi zai iya jawo mummunar sakamako. (Karanta Karin Magana 19:11.) Saꞌad da Abigail ta gaya wa Dauda yadda matakin da yake so ya ɗauka zai sa Jehobah ya ji, hakan ya sa Dauda ya kame kansa. Idan wani ya yi abin da ya ɓata maka rai, zai dace ka yi tunani kafin ka mayar da martani. (Yak. 1:19) Ka roƙi Jehobah ya taimaka maka. Kuma ka yi ƙoƙari ka san abin da Jehobah yake so ka yi a irin wannan yanayin. Yin hakan zai sa ka huce kuma ka daina fushi.

12. Ta yaya wasu za su iya taimaka mana mu kame kanmu kuma mu yanke shawarar da ta dace?

12 Jehobah ya yi amfani da Abigail wajen taimaka wa Dauda ya yi tunani sosai kafin ya ɗauki mataki. A yau ma, zai iya yin amfani da ꞌyanꞌuwanmu maza da mata wajen taimaka mana mu fahimci raꞌayinsa game da wani batu. Saboda haka, idan wani abu ya sa ka fushi sosai, ka tattauna da wani ɗanꞌuwa da ya manyanta don ya taimaka maka ka san abin da ya kamata ka yi a yanayin da kake ciki. (K. Mag. 12:15; 20:18) Idan wani abu ya sa abokinka fushi sosai, ka taimaka masa kamar yadda Abigail ta yi. Kuma ka sa ya fahimci abin da Jehobah yake so ya yi a irin yanayin da yake ciki. Jehobah zai albarkaci ƙoƙarin da kake yi don ka taimaka wa mutane su fahimci raꞌayinsa.

KA DOGARA GA JEHOBAH MAIMAKON KA JI TSORO

13. Me ya kamata mu tuna idan muna jin tsoro?

13 A wasu lokuta, za mu iya fuskantar yanayoyin da za su iya sa mu ji tsoro. Amma idan muka tuna cewa Jehobah ne mai iko duka, hakan zai taimaka mana mu dogara gare shi ko da muna jin tsoro. (Zab. 27:1) Jehobah zai iya taimaka mana ko da muna ganin kamar ta mu ta ƙare. Abin da ya faru da annabi Yunana ke nan. Ko da yake yana ƙaunar Jehobah, ya ji tsoro sosai saꞌad da Jehobah ya ce ya je ya yi waꞌazi a wani wuri mai ban tsoro.

14. Me ya sa Yunana ya ji tsoron yin abin da Jehobah ya gaya masa?

14 Jehobah ya gaya wa Yunana ya yi wani abu mai wuya sosai. Jehobah ya ce ya je ya gaya wa mutanen Nineba cewa zai hallaka su. (Yona 1:​1, 2) Da a ce kai ne aka ba irin wannan aikin, yaya za ka ji? Mutum zai yi wata ɗaya yana tafiya da ƙafa daga Israꞌila zuwa Nineba. Ƙari ga haka, Assuriyawa mugaye ne sosai, har ma ana kiran Nineba “birni mai zub da jini.” (Nah. 3:​1, 7) Maimakon Yunana ya je wurin da Jehobah ya gaya masa, ya gudu zuwa wani wuri dabam.—Yona 1:3.

15. Me ya taimaka wa Yunana ya ƙara dogara ga Jehobah? (Yona 2:​6-9)

15 Saꞌad da Yunana yake guduwa daga aikin da Jehobah ya ba shi, Jehobah ya tuna masa cewa yana da iko sosai ta wurin kāre shi a hanya mai ban mamaki. (Yona 1:​15, 17) Wannan abin da ya faru ya taimaka wa Yunana ya daina jin tsoro, kuma ya gane cewa Jehobah zai iya kāre shi daga kowane irin yanayi. (Karanta Yona 2:​6-9.) Shi ya sa da Jehobah ya sake ba shi wata dama kuma, ya yi biyayya. Ya je Nineba, mutanen sun saurare shi, kuma suka tsira.—Yona 3:5.

16. Me zai iya taimaka mana saꞌad da muke tsoro? (Karin Magana 29:25) (Ka kuma duba hotunan.)

16 Mene ne za mu iya koya daga wannan labarin? Bai kamata mu bar tsoron mutum ko wani abu ya hana mu bauta wa Jehobah ba. (Karanta Karin Magana 29:25.) Yunana ya yi tunani a kan dukan abubuwan da suka faru a rayuwarsa. Kuma ya fahimci cewa, maimakon ya riƙa damuwa a kan abubuwan da za su iya faruwa da shi, zai dace ya kasance da tabbaci cewa Jehobah zai taimaka masa a duk yanayin da yake ciki. Mu ma idan muka yi tunani a kan yadda Jehobah ya taimaka da kuma kāre mu a dā, ba za mu ji tsoron abubuwan da za su iya faruwa da mu ba. Ƙari ga haka, za mu iya yin tunani a kan yadda Jehobah ya taimaka wa ꞌyanꞌuwanmu da suka dogara gare shi saꞌad da suke cikin yanayi mai wuya.a (Ibran. 13:6) Idan muka dogara ga Jehobah kuma muka taimaka wa wasu su yi hakan, muna nuna cewa mu masu hikima ne.

Hotuna: Na 1. Annabi Yunana yana takawa zuwa ƙofar birnin Nineba. Na 2. Wani matashi yana tafiya cikin makarantarsu kuma masu yin abin da Jehobah ba ya so suna koꞌina. Akwai tutar ꞌyan luwaɗi a koꞌina a wurin. Wani yaro kuma yana cin zalin wani yaro.

Da yake Yunana ya dogara ga Jehobah, hakan ya taimaka masa ya iya yin abin da Jehobah ya gaya masa (Ka duba sakin layi na 16)


KA CI-GABA DA ƘOƘARIN ZAMA DA RAꞌAYIN JEHOBAH

17. Mene ne zai taimaka mana mu ci-gaba da kasancewa da raꞌayin Jehobah?

17 Kamar yadda muka tattauna, idan muka yi tunani kafin mu ɗau mataki, hakan zai taimaka mana mu yi abin da ya dace a yanayi mai wuya. Mene ne zai taimaka mana mu ci-gaba da yin hakan? Jehobah ne zai fi taimaka mana. Shi ya sa ya ba mu Kalmarsa da kuma ruhu mai tsarki. (Neh. 9:20; Zab. 32:8) Ya yi mana tanadin abubuwan da za su taimaka mana mu yanke shawarwari masu kyau kuma mu iya kame kanmu. (Zab. 119:​97-101) Saboda haka, zai dace mu riƙa yin tunani a kan abubuwan da Littafi Mai Tsarki ya faɗa, kuma mu roƙi Jehobah ya ba mu ruhu mai tsarki. Hakan zai taimaka mana mu kasance da raꞌayin Jehobah, kuma mu yi abubuwa yadda Jehobah yake so mu yi.—K. Mag. 21:11.

18. Mene ne ka ƙudura niyyar yi?

18 Zai dace mu ci-gaba da roƙon Jehobah ya ba mu hikima kuma ya taimaka mana mu kasance da raꞌayinsa. (Zab. 14:2) Idan muka yi hakan, ba za mu taɓa “kauce wa hanyar hikima” ba. (K. Mag. 21:16) Bari mu riƙa neman taimakon Jehobah a duk yanayin da muka sami kanmu. Yin hakan, zai sa Jehobah farin ciki.

MENE NE MUKA KOYA DAGA LABARIN . . .

  • Naꞌaman?

  • Dauda da Abigail?

  • Yunana?

WAƘA TA 42 Adduꞌar Bawan Allah

a Alal misali, ka duba labarin Ɗanꞌuwa Georgiy Porchulyan a sashen nan “Tarihin Shaidun Jehobah” da ke JW Library® ko kuma jw.org/ha.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba