Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Janairu pp. 20-25
  • Ta Yaya Za Ka Nuna Godiya don Fansar Yesu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ta Yaya Za Ka Nuna Godiya don Fansar Yesu?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • WAƊANDA SUKE KAN YIN NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI
  • KIRISTOCIN DA SUKA YI BAFTISMA
  • WAƊANDA SUKA DAINA BAUTA WA JEHOBAH
  • MENE NE ZA KA YI?
  • Yadda Muke Amfana Daga Ƙaunar da Jehobah Ya Nuna Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Mene ne Fansar Yesu Ta Nuna Mana?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Me Ya Sa Muke Bukatar Fansar Yesu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ka Yi Shiri don Rana Mafi Muhimmanci a Shekara?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Janairu pp. 20-25

23-29 GA MARIS, 2026

WAƘA TA 18 Muna Godiya Domin Mutuwar Yesu

Ta Yaya Za Ka Nuna Godiya don Fansar Yesu?

“Ƙaunar Kristi a gare mu ce take tilasta mana.”—2 KOR. 5:14.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu tattauna yadda dukanmu za mu nuna cewa muna godiya don fansar Yesu.

1-2. Mene ne fansar Yesu za ta motsa mu mu yi, kuma me ya sa? (2 Korintiyawa 5:​14, 15) (Ka kuma duba hoton.)

IDAN wani ya cece ka daga ginin da ya rushe, za ka taɓa mantawa da wannan mutumin da ya cece ka? Zai yi wuya. Za ka yi farin ciki sosai. Kuma za ka so ka nuna wa mutumin cewa ba za ka taɓa manta da abin da ya yi maka ba.

2 Kamar yadda muka gani a talifin da ya wuce, muna bukatar wanda zai cece mu daga zunubi da kuma mutuwa. Kuma abin da Jehobah ya yi ke nan. Ya ba da Ɗansa, (1) don ya iya gafarta mana zunubanmu, (2) mu kasance da begen zama marasa zunubi a nan gaba, kuma (3) mu iya zama aminansa. Fansar ta sa mu kasance da begen yin rayuwa har abada a duniya. Ƙari ga haka, fansar ta nuna yawan ƙaunar da Yesu yake yi wa ꞌyanꞌadam. Ya ƙaunaci ꞌyanꞌadam sosai tun kafin ma ya zo duniya. (K. Mag. 8:​30, 31) Manzo Bulus ya ce, “ƙaunar Kristi a gare mu ce take tilasta mana.” (Karanta 2 Korintiyawa 5:​14, 15.) Hakan yana nufin cewa muna bukatar mu nuna godiya don fansar da Yesu ya bayar, kuma mu nuna cewa ba za mu taɓa manta da abin da ya yi mana ba.

Lokacin da ake ceto mutumin da gini ya rushe a kansa a talifin da ya wuce.

Idan wani ya cece mu daga ginin da ya rushe, babu shakka za mu nuna masa cewa muna godiya. Haka ma, yana da muhimmanci mu nuna godiya don yadda Jehobah da Yesu suka cece mu daga zunubi da kuma mutuwa (Ka duba sakin layi na 1-2)


3. Me ya sa yadda kowannenmu zai nuna godiya don fansar Yesu zai iya bambanta?

3 Mene ne za ka yi don ka nuna cewa kana godiya don fansar Yesu? Abin da kake so ka yi zai iya bambanta da na wani. Me ya sa? Ga wani misali. A ce mutane uku za su je wuri ɗaya, amma sun tashi daga wurare dabam-dabam. Babu shakka, inda za su bi ba ɗaya ba. Haka ma, yadda kowannenmu zai nuna godiya don fansar Yesu zai iya bambanta bisa ga ƙarfin dangantakar da ke tsakaninsa da Jehobah. Saboda haka, a wannan talifin, za mu tattauna yadda mutane kashi uku, za su nuna cewa suna godiya don fansar Yesu: (1) waɗanda suke kan yin nazarin Littafi Mai Tsarki, (2) Kiristocin da suka yi baftisma, kuma (3) waɗanda suka daina bauta wa Jehobah.

WAƊANDA SUKE KAN YIN NAZARIN LITTAFI MAI TSARKI

4. Me ya nuna cewa Jehobah yana ganin waɗanda suke kan yin nazarin Littafi Mai Tsarki?

4 Ga wani abin da zai dace ka yi laꞌakari da shi idan kana kan yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Da yake kana son ka koya game da Jehobah da kuma gaskiya da ke Littafi Mai Tsarki, hakan ya nuna cewa Jehobah yana son ka zama abokinsa kuma yana taimaka maka ka yi hakan. (Yoh. 6:44; A. M. 13:48) Jehobah yana ganin abin da ke zuciyarka. Hakan yana nufin cewa yana ganin ƙoƙarin da kake yi, da kuma canje-canjen da kake yi a rayuwarka. Kuma hakan, na sa shi farin ciki. (K. Mag. 17:3; 27:11) Fansar Yesu ce ta sa za ka iya kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah. (Rom. 5:​10, 11) Zai dace ka riƙa tunawa da hakan.

5. Ta yaya waɗanda suke kan yin nazarin Littafi Mai Tsarki za su bi shawarar da ke Filibiyawa 3:16?

5 Idan ana kan yin nazarin Littafi Mai Tsarki da kai, ta yaya za ka nuna godiya don fansar Yesu? Hanya ɗaya ita ce ta wurin bin abin da Bulus ya gaya wa ꞌyanꞌuwan da ke Filibi. Ya ce: “Babban abin shi ne duk inda muka kai, mu ci gaba daga nan.” (Filib. 3:16) Kamar yadda muka gani a wannan ayar, kada ka bar kome ya hana ka ci-gaba da tafiya a hanyar da za ta kai ga samun rai.—Mat. 7:14; Luk. 9:62.

6. Mene ne waɗanda ake nazari da su za su iya yi idan yana musu wuya su yi canje-canje? (Maimaitawar Shariꞌa 30:​11-14) (Ka kuma duba hoton.)

6 Me za ka iya yi idan ya yi maka wuya ka yarda da wani abin da ka koya daga Littafi Mai Tsarki kwanan nan? Ka ƙara yin bincike a kan batun. Kuma ka roƙi Jehobah ya taimaka maka ka fahimci batun da kyau. (Zab. 86:11) Idan kuma bayan hakan ba ka fahimci batun da kyau ba, ka daina damuwa a kan batun kuma ka ci-gaba da yin nazarinka. Mai yiwuwa daga baya za ka fahimci batun da kyau. Idan kuma barin wani halin da Jehobah ba ya so yana yi maka wuya, me zai taimaka maka? Ka tuna cewa duk abin da Jehobah ya ce mu yi, bai fi ƙarfinmu ba. Za ka iya yin abubuwan da za su sa shi farin ciki. (Karanta Maimaitawar Shariꞌa 30:​11-14.) Jehobah ya yi alkawari cewa zai taimaka maka. (Isha. 41:​10, 13; 1 Kor. 10:13) Saboda haka, kada ka gaji. Kada ka mai da hankali a kan abin da kake fama da shi. A maimakon haka, ka mai da hankali a kan abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi maka. Musamman yadda ya turo Ɗansa ya mutu a madadinka. Yayin da kake ƙara ƙaunar Jehobah, za ka ga cewa “umurnansa ba su da nauyi.”—1 Yoh. 5:3.a

Wani mutum da ke karanta darasi na 40 na littafin nan, “Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!” A kan tebur a gabansa, akwai kwalin sigari da wani kwano inda yake jefa waɗanda ya shanye.

Jehobah ba ya gaya mana mu yi abin da ya fi ƙarfinmu. Zai taimaka mana mu iya yin abubuwan da yake so (Ka duba sakin layi na 6)


7. Mene ne matasan da iyayensu Shaidu ne za su iya tunani a kai?

7 Matasan da iyayensu Shaidu ne kuma fa? Ku ma ɗaliban Littafi Mai Tsarki ne. Ku ne ɗalibai mafi muhimmanci ga iyayenku. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Ku yi kusa da Allah, shi kuwa zai yi kusa da ku.” (Yak. 4:8; 1 Tar. 28:9) Idan kuka ɗauki matakan da za su sa ku kusaci Jehobah, shi ma zai kusace ku. Ba don iyayenku Shaidu ne ya sa Jehobah ya damu da ku ba. Ya damu da ku ne don yana so ku ƙulla dangantaka ta kud da kud da shi. Mene ne Jehobah ya yi don hakan ya yiwu? Ya ba da Ɗansa a madadinku. Kada ku taɓa manta da wannan alherin da Jehobah ya yi muku. (Rom. 5:​1, 2) Saboda haka, kafin ku halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu na wannan shekarar, ku yi tunani a kan abin da Jehobah da Yesu suka yi muku. Saꞌan nan, ku yi tunani a kan yadda kuke so ku yi rayuwarku, da maƙasudan da za ku kafa da za su nuna cewa kuna godiya ga Jehobah domin fansar Yesu.b

KIRISTOCIN DA SUKA YI BAFTISMA

8. Ta yaya Kiristocin da suka yi baftisma suka nuna cewa suna godiya don fansar Yesu?

8 Idan kai Kirista ne da ya yi baftisma, babu shakka ka nuna a hanyoyi da yawa cewa kana godiya don fansar Yesu. Alal misali, ka yi canje-canjen da kake bukata a rayuwarka don ka iya ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah. Ka bi umurnin da Yesu ya bayar cewa mu almajirtar da mutane kuma mu koya musu game da Jehobah. Ka kuma yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma ka yi baftisma. Mai yiwuwa an tsananta maka don kana bauta wa Jehobah. (2 Tim. 3:12) Duk da haka, ka ci-gaba da bauta wa Jehobah da aminci. Hakan ya nuna cewa kana ƙaunar Jehobah kuma kana godiya don fansar Yesu.—Ibran. 12:​2, 3.

9. Idan mun yi baftisma, mene ne muke bukatar mu yi laꞌakari da shi?

9 Idan mun riga mun yi baftisma akwai wani abin da muke bukatar mu yi laꞌakari da shi. Da shigewar lokaci, za mu iya soma mantawa da muhimmancin fansar a gare mu. Ta yaya hakan zai iya faruwa? Bari mu yi laꞌakari da abin da faru da Kiristocin da ke Afisa a ƙarni na farko. Yesu ya yaba musu don yadda suke jimrewa. Amma ya gaya musu cewa, sun bar ƙaunarsu ta farko. (R. Yar. 2:​3, 4) Abin da Yesu ya gaya musu ya nuna cewa, da shigewar lokaci mutum zai iya yana bauta wa Jehobah, amma ba ya yin hakan da dukan zuciyarsa. Mai yiwuwa irin wannan mutumin yana adduꞌa, yana halartan taro, yana kuma fita waꞌazi don kawai ya saba da hakan, ba don ƙaunar da yake yi wa Jehobah da mutane ba. Mene ne za ka iya yi idan ƙaunarka ga Jehobah ta soma raguwa?

10. Ta yaya za ka iya yin abin da Bulus ya gaya wa Timoti ya yi? (1 Timoti 4:​13, 15)

10 Manzo Bulus ya gaya wa Timoti cewa ya riƙa yin tunani mai zurfi a kan yadda yake bauta wa Jehobah, kuma ya ba da kansa gabaki ɗaya ga bautar Jehobah. (Karanta 1 Timoti 4:​13, 15.) Kai ma za ka iya yin tunani a kan abin da za ka iya yi don ka ci-gaba da bauta wa Jehobah da ƙwazo. (Rom. 12:11) Alal misali, za ka iya yin shiri da kyau kafin ka halarci taro. Hakan zai sa ka mai da hankali sosai idan ka halarci taron. Kuma saꞌad da kake nazarin Littafi Mai Tsarki, za ka iya yin hakan a wurin da zai ba ka dama ka yi tunani mai zurfi a kan abin da kake koya. Kamar yadda kake bukatar ka riƙa ƙara itace a wuta don kar ta mutu, kana bukatar ka riƙa yin abubuwan nan. Hakan zai sa ka ci-gaba da nuna godiya don fansar Yesu da kuma sauran abubuwa masu kyau da Jehobah ya yi maka. Ƙari ga haka, kafin ranar da za a yi Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, za ka iya yin tunani a kan abubuwan da kake mora a rayuwarka don kai Mashaidi ne. Babu shakka, hakan zai taimaka maka ka ƙara nuna godiya don fansar Yesu. Fansar ce ta sa ka iya kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah.

11-12. Idan a wasu lokuta ba ka bauta wa Jehobah da ƙwazo, hakan yana nufin cewa ruhun Allah ba ya tare da kai? Ka bayyana. (Ka kuma duba hoton.)

11 Idan a wasu lokuta ba ka bauta wa Jehobah da ƙwazo kamar yadda kake yi a dā, kada ka yi sanyin gwiwa ko kuma ka ga kamar ruhun Jehobah ba ya tare da kai. Ka tuna da abin da Bulus ya gaya wa Korintiyawa game da hidimarsa. Ya gaya musu cewa, a wasu lokuta waꞌazin da yake yi ba domin ganin damansa ba ne. Amma ya ci-gaba da yin hakan domin an ba shi amana ne. (1 Kor. 9:17) Mene ne Bulus yake nufi?

12 A wasu lokuta, Bulus ba ya marmarin yin waꞌazi. Duk da haka, bai daina yin waꞌazi ba. Mu ma za mu iya yin koyi da shi. Mu yi iya ƙoƙarinmu wajen yin abin da ya dace ko da ba ma marmarin yin hakan. Mu roƙi Jehobah ya taimaka mana mu kasance da niyya da kuma ƙarfin yin abin da yake so mu yi. (Filib. 2:13) Mu ci-gaba da yin abubuwan da za su sa mu kusaci Jehobah. Mu kasance da tabbaci cewa, idan muka ci-gaba da yin abubuwan nan, ƙaunarmu ga Jehobah za ta sake yin ƙarfi, kuma za mu ci-gaba da yin hidimarmu da ƙwazo.

ꞌYanꞌuwa mata biyu suna waꞌazi. Ɗayan tana tura jaririnta a cikin abin ɗaukan jarirai tana baƙin ciki. Ɗayan kuma ta sa hannu a kafaɗar ꞌyarꞌuwar tana mata magana.

Ka ci-gaba da yin abubuwan da za su sa ka kusaci Jehobah ko da a wasu lokuta yin hakan yana maka wuya (Ka duba sakin layi na 11-12)


13. Mene ne za mu yi don mu tabbata cewa muna rayuwa kamar yadda Jehobah yake so?

13 A wasu lokuta, zai dace mu riƙa yin tunani game da yadda muke rayuwa. Abin da Bulus ya ce mu riƙa yi ke nan, a 2 Korintiyawa 13:5. Ayar ta ce, “Ku gwada kanku domin ku sani ko kuna bin Yesu Almasihu cikin aminci.” Alal misali, za ka iya tambayar kanka cewa, ‘Shin, ina sa Mulkin Allah farko a rayuwata?’ (Mat. 6:33) ‘Abubuwan da nake kallo da kuma yi saꞌad da nake hutawa, suna nuna cewa na tsani abubuwa marasa kyau?’ (Zab. 97:10) ‘Ina faɗa da kuma yin abubuwan da za su sa a sami zaman lafiya da haɗin kai a ikilisiya?’ (Afis. 4:​2, 3) Yayin da muke shirin halartan Taron Tunawa da Mutuwar Yesu, zai yi kyau mu yi tunani a kan tambayoyin nan. Idan muka yi tunani a kan abin da Jehobah da Yesu suka yi mana, hakan zai sa mu bincika kanmu don mu san ko muna rayuwa yadda Jehobah da Yesu Kristi suke so.c

WAƊANDA SUKA DAINA BAUTA WA JEHOBAH

14. Waɗanne abubuwa ne suka sa wasu ꞌyanꞌuwanmu suka daina bauta wa Jehobah?

14 Wasu ꞌyanꞌuwanmu maza da mata sun daina halartan taro, duk da cewa sun yi shekaru da yawa suna bauta wa Jehobah da aminci. Me ya sa? Wasu suna ganin matsalolin rayuwa sun yi musu yawa. (Luk. 21:34) Wasu kuma sun yi fushi don abin da wani ya faɗa ko ya yi musu. (Yak. 3:2) Ban da haka ma, wasu sun yi zunubi mai tsanani kuma suna jin kunyar neman taimako. Amma, ko da mene ne ya faru, me za ka iya yi idan ka daina bauta wa Jehobah kamar yadda kake yi a dā? Idan ka yi tunani a kan fansar Yesu, wane mataki ne hakan zai sa ka ɗauka?

15. Ta yaya Jehobah yake nuna cewa ya damu da bayinsa da suka daina bauta masa? (Ezekiyel 34:​11, 12, 16)

15 Ka yi tunani a kan yadda Jehobah yake ɗaukan waɗanda suka daina bauta masa. Ba ya watsi da su. A maimakon haka, yana neman su, ya ciyar da su, kuma ya taimaka musu su dawo wurinsa. (Karanta Ezekiyel 34:​11, 12, 16.) Mai yiwuwa abin da Jehobah yake yi maka ke nan yanzu haka! Da yake kana nazarin wannan talifin, hakan ya nuna cewa har ila kana son ka yi abin da Jehobah yake so. Jehobah ne ya jawo ka tun daga farko. Ya ga cewa kai mutumin kirki ne. Shi ya sa yake so ka dawo ka ci-gaba da bauta masa.

16. Mene ne zai taimaka wa wanda ya daina bauta wa Jehobah ya komo gare shi? (Ka kuma duba hoton.)

16 Ka yi laꞌakari da kalmomi masu ban ƙarfafa da ke ƙasidar nan, Ka Komo ga Jehobah. Wurin ya ce: “Ka tabbata cewa Jehobah zai kasance tare da kai idan ka komo gare shi. Zai taimaka maka ka daina alhini da kuma ɓacin rai. Ƙari ga haka, za ka sami kwanciyar hankali don za ka kasance da lamiri mai kyau. Za ka sake yin marmarin bauta wa Jehobah tare da ꞌyanꞌuwa masu bi.” Ka kuma tuna cewa, dattawa suna shirye su taimaka maka. Suna “kamar mafaka daga iska, kamar wurin ɓuya daga ruwan ƙanƙara.” (Isha. 32:2) Don ka nuna kana godiya don fansar Yesu, ka tambayi kanka: ‘Waɗanne abubuwa ne zan iya yi yanzu don in komo ga Jehobah?’ (Isha. 1:18; 1 Bit. 2:25) Alal misali, za ka iya halartan taro a Majami’ar Mulki. Ƙari ga haka, za ka iya gaya wa wani dattijo cewa kana so ka komo ga Jehobah. Dattijon zai iya shirya yadda za a soma nazari da kai. Ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai yi maka albarka yayin da kake ƙoƙarin nuna godiya don fansar Yesu.

Wani mutum da bai tsufa sosai ba, riƙe da Littafi Mai Tsarki a hannunsa ya tsaya kusa da Majamiꞌar Mulki. Yana kallon yadda ꞌyanꞌuwan da suka zo taro suke marabtar juna.

Ka tambayi kanka, ‘Waɗanne abubuwa ne zan iya yi yanzu don in komo ga Jehobah?’ (Ka duba sakin layi na 16)


MENE NE ZA KA YI?

17-18. Mene ne za mu iya yi kafin mu halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu na wannan shekarar?

17 Yesu ya ce an ba da fansar ne domin duk “wanda yake ba da gaskiya gare shi kada ya hallaka, amma ya sami rai na har abada.” (Yoh. 3:16) Fansar Yesu ta sa Jehobah ya ꞌyantar da mu daga zunubi da kuma mutuwa. Ba za mu so mu manta da wannan alherin da Jehobah ya yi mana ba. (Rom. 3:​23, 24; 2 Kor. 6:1) Kafin Taron Tunawa da Mutuwar Yesu da kuma bayan hakan, ka yi tunani a kan irin ƙaunar da Jehobah da Yesu suka nuna maka. Hakan zai sa ka nuna godiya.

18 Ta yaya za ka nuna godiya don fansar Yesu? Abin da za ka yi zai iya bambanta da abin da wani zai yi. Amma duk abin da ka zaɓa za ka yi, ka kasance da tabbaci cewa Jehobah zai albarkace ka tare da miliyoyin ꞌyanꞌuwa a faɗin duniya da suke ƙoƙarin yin rayuwa “don wanda ya mutu dominsu.”—2 Kor. 5:15.

TA YAYA ZA KA NUNA GODIYA DON FANSAR YESU IDAN . . .

  • kana kan yin nazari?

  • ka riga ka yi baftisma?

  • ka daina bauta wa Jehobah?

WAƘA TA 14 Mu Yabi Sabon Sarkinmu

a Akwatin nan mai jigo “Maƙasudi” da ke kusa da ƙarshen kowane darasi a littafin nan, Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada! zai taimaka maka ka san yadda za ka bi abin da kake koya yayin da kake nazarin Littafi Mai Tsarki.

b Don samun shawarwari a kan maƙasudan da za ka iya kafawa, ka duba talifin nan mai jigo, “Matasa—‘Ku Yi Aikin Cetonku’” da ke Hasumiyar Tsaro ta Disamba 2017.

c Don samun shawarwari a kan abubuwan da za mu iya yi don mu ci-gaba da nuna godiya ga Jehobah, ka duba talifin nan mai jigo, “Me Ke Motsa Ka Ga Bauta Ma Allah?” da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Yuni, 1995.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba