Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Janairu pp. 14-19
  • Me Ya Sa Muke Bukatar Fansar Yesu?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Me Ya Sa Muke Bukatar Fansar Yesu?
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • FANSAR TA SA JEHOBAH YA IYA GAFARTA MANA
  • FANSAR TA SA MUNA DA BEGEN ZAMA MARASA ZUNUBI
  • FANSAR TA SA MU KASANCE DA DANGANTAKA MAI KYAU DA JEHOBAH
  • FANSAR TA NUNA YAWAN TAUSAYIN JEHOBAH
  • Mene ne Fansar Yesu Ta Nuna Mana?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Ta Yaya Za Ka Nuna Godiya don Fansar Yesu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Yadda Muke Amfana Daga Ƙaunar da Jehobah Ya Nuna Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Muna Godiya don Jehobah Yana Gafarta Mana
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Janairu pp. 14-19

16-22 GA MARIS, 2026

WAƘA TA 20 Ka Ba da Ɗanka Mai Daraja

Me Ya Sa Muke Bukatar Fansar Yesu?

“Wane ne zai cece ni daga jikin nan da yake mutuwa?”—ROM. 7:24.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga cewa mutuwar Yesu ce ta sa Jehobah ya riƙa gafarta mana zunubanmu, mu kasance da begen zama marasa zunubi a nan gaba, kuma mu kasance da dangantaka mai kyau da Jehobah.

1-2. Daga mene ne muke bukatar a cece mu, kuma me ya sa? (Romawa 7:​22-24) (Ka kuma duba hoton.)

A CE wani mutum yana cikin wani gida sai gidan ya rushe kuma ya danne shi. Ko da yake yana da rai, ba zai iya fitowa da kansa ba sai an taimaka masa. Abin da zai iya yi kawai shi ne ya yi ta ihu, mai yiwuwa wani zai ji ya taimaka masa.

2 Dukan ꞌyanꞌadam suna cikin irin wannan yanayin. Ta yaya? Saꞌad da Adamu ya yi wa Mahaliccinsa rashin biyayya, ya zama mai zunubi. Kuma dukanmu mun gaji zunubi domin mun ꞌyaꞌyansa ne. Kamar mutumin da aka ambata a sakin layi na ɗaya, ba abin da mu da kanmu za mu iya yi game da zunubin, sai dai wani ya taimaka mana. A wasiƙar da Bulus ya rubuta zuwa ga Romawa, ya bayyana yanayin da muke ciki don zunubin da muka gāda. (Karanta Romawa 7:​22-24.) Bulus ya yi tambaya cewa, “wane ne zai cece ni daga jikin nan da yake mutuwa?” Sakamakon zunubin da Bulus ya gāda shi ne mutuwa. (Rom. 6:23) Kamar Bulus, mu ma a yau mun gāji zunubi da kuma mutuwa, kuma muna bukatar wanda zai cece mu daga wannan yanayin.

Wani mutum da gini ya rushe a kansa, ya miƙa hannunsa sama yana neman taimako.

Kamar mutumin da yake cikin wani gini sai ginin ya rushe, mu ma muna bukatar wanda zai taimaka mana mu tsira daga zunubin da muka gāda (Ka duba sakin layi na 1-2)


3. Waɗanne abubuwa ne za mu iya samu don fansar Yesu?

3 Bulus bai kammala maganarsa a hanyar da za ta nuna cewa babu mafita kwatakwata ba. Bayan ya yi tambayar nan cewa: “Wane ne zai cece ni daga jikin nan da yake mutuwa?” Sai ya amsa tambayar da kansa ya ce: “Godiya ga Allah, ta wurin Yesu Kristi Ubangijinmu!” (Rom. 7:25) A ayar nan, Bulus yana magana ne game da fansar da Yesu ya bayar.a Fansar ce ta sa (1) Jehobah zai iya gafarta mana zunubanmu, (2) mu kasance da begen zama marasa zunubi a nan gaba, kuma (3) mu iya ƙulla dangantaka mai kyau da Jehobah. A wannan talifin, za mu tattauna abubuwa ukun nan. Muna da tabbaci cewa hakan zai sa mu ƙara ƙaunar Jehobah, “Allah wanda yake ba da bege.” (Rom. 15:13) Za mu kuma ƙara gode wa Yesu “wanda ta wurinsa ne muka sami fansa.”—Kol. 1:14.

FANSAR TA SA JEHOBAH YA IYA GAFARTA MANA

4-5. Me ya sa dukanmu muke bukatar fansar? (Mai-Waꞌazi 7:20)

4 Muna bukatar fansar don Jehobah ya iya gafarta mana zunubanmu. Dukanmu mukan yi zunubi ta wurin abubuwan da muke faɗa da kuma abubuwan da muke yi. (Karanta Mai-Waꞌazi 7:20.) Amma, akwai wasu zunuban da suka fi wasu tsanani. Alal misali, dokar da Allah ya bayar ta hannun Musa ta ce, duk wanda ya yi zina ko ya kashe wani, a kashe shi. (L. Fir. 20:10; L. Ƙid. 35:​30, 31) Amma, ko da zunubin ba mai tsanani ba ne, zunubi zunubi ne. Alal misali, Dauda ya ce: “Zan yi hankali da hanyata, ba zan yi zunubi da harshena ba.” (Zab. 39:1) Hakan ya nuna cewa, za mu iya yin zunubi ta wajen abubuwan da muke faɗa.—Yak. 3:2.

5 Ka yi tunani a kan abubuwan da ka yi a dā. Shin, ka taɓa gaya wa wani mutum wani abu, kuma daga baya ka yi da na sani? Ka taɓa yin kurakuren da suka sa ka baƙin ciki? Dukanmu mun taɓa yin irin waɗannan abubuwan. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan mun ce ba mu da zunubi, ruɗin kanmu muke yi, gaskiya kuwa ba ta cikinmu.”—1 Yoh. 1:8.

6-7. Me zai sa Jehobah ya iya gafarta mana zunubanmu? (Ka kuma duba hoton.)

6 Jehobah ya aiko Yesu ya zo ya mutu a madadinmu, kuma ta haka ne zai iya gafarta mana zunubanmu. (Afis. 1:7) Amma, hakan ba ya nufin cewa Jehobah yakan ƙyale zunubanmu kamar ba kome ba ne. Jehobah ya tsani zunubi. (Isha. 59:2) Da yake Jehobah mai adalci ne, ya bukaci ya yi wani abu don ya iya gafarta mana zunubanmu.

7 A dokar da Allah ya bayar ta hannun Musa, an bukaci Israꞌilawa su riƙa yin hadaya da dabbobi don a iya gafarta musu zunubansu. (L. Fir. 4:​27-31; 17:11) Hadayun nan suna nuni ne ga hadayar da ta fi, wato hadayar Yesu da za ta sa mu sami albarku da yawa. Hadayar ce za ta iya sa Jehobah ya gafarta mana zunubanmu. Wasiƙar da Bulus ya rubuta wa ꞌyanꞌuwa a Korinti ta nuna cewa Bulus ya fahimci yadda za mu amfana daga fansar Yesu. Bayan ya ambata abubuwa marasa kyau da suke yi a dā, ya gaya musu cewa: “An tsabtace ku, an keɓe ku da tsarki ga Allah, an kuma mai da ku marasa laifi a gaban Allah cikin sunan Ubangiji Yesu Almasihu, da kuma Ruhun Allahnmu.”—1 Kor. 6:​9-11.

Wani Baꞌisraꞌile da matarsa da ɗansu a haikali suna miƙa wa firist tunkiya.

Hadayun dabbobin da Israꞌilawa suka yi suna nuni ne ga hadayar da ta fi, wato hadayar Yesu da za ta sa mu sami albarku da yawa (Ka duba sakin layi na 6-7)


8. Mene ne za ka iya yin tunani a kai kafin ka halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu na wannan shekarar?

8 Kafin ka halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu na wannan shekarar, ka yi tunani a kan yadda ka amfana domin Jehobah ya gafarta maka. Alal misali, saboda fansar Yesu, ba ka bukatar ka riƙa damuwa don zunuban da ka yi a dā da Jehobah ya riga ya gafarta maka. Shin, yana maka wuya ka yarda cewa Jehobah ya gafarta maka zunuban da ka yi a dā? Wataƙila ma ka taɓa gaya wa kanka cewa, ‘Na san Jehobah zai iya gafarta mini, amma ni ba zan iya gafarta wa kaina ba.’ Idan haka ne kake tunani a wasu lokuta, ka tuna cewa, Jehobah ne yake gafarta wa mutane, kuma ya ba wa Ɗansa Yesu ikon yin shariꞌa. Jehobah bai ba wa kai ko wani ɗanadam ikon zaɓan wanda za a gafarta wa da wanda ba za a gafarta wa ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: Idan “muna tafiya cikin haske kamar yadda Allah yake cikin haske, . . . jinin Yesu Ɗansa . . . yana tsabtace mu daga dukan zunubi.” (1 Yoh. 1:​6, 7) Muna da tabbaci cewa hakan gaskiya ne, domin Kalmar Allah ce. Fansar Yesu ta sa Jehobah zai iya gafarta mana zunubanmu. Kuma Littafi Mai Tsarki ya ce yana a shirye ya gafarta mana.—Zab. 86:5.

FANSAR TA SA MUNA DA BEGEN ZAMA MARASA ZUNUBI

9. Mene ne zunubi ya ƙunsa? (Zabura 51:5)

9 A Littafi Mai Tsarki, kalmar nan “zunubi” ta ƙunshi aikata wani abin da ba daidai ba, da kuma ajizancin da muka gāda tun muna cikin mahaifiyarmu. (Karanta Zabura 51:5.) Zunubin da muka gāda yana sa mu yi wasu abubuwan da ba su dace ba, amma ba shi ke nan ba. Yana sa mu yi rashin lafiya, mu tsufa kuma mu mutu. Shi ya sa jarirai ma da ba su taɓa yin zunubi ba sukan yi rashin lafiya kuma su mutu. Kuma shi ya sa mutanen kirki da marasa kirki ma suke mutuwa. Dukan ꞌyanꞌadam sun gāji wannan zunubin.

10. Yaya Adamu da Hauwaꞌu suka ji bayan da suka yi zunubi?

10 Ka yi tunanin yadda Adamu da Hauwaꞌu suka ji bayan da suka yi zunubi kuma suka zama ajizai. Zunubi ya sa sun yi baƙin ciki sosai. Nan da nan bayan sun yi zunubi, zuciyarsu ta soma damunsu. (Rom. 2:15) Sun soma ji a jikinsu cewa abubuwa sun taɓarɓare. Kuma suka soma ji cewa suna bukatar su rufe wasu ɓangarorin jikinsu, su kuma ɓuya daga Mahaliccinsu. (Far. 3:​7, 8) A lokacin ne karo na farko da Adamu da Hauwaꞌu suka ji kunya, suka damu, kuma suka soma baƙin ciki. Haka suka yi ta fama har suka mutu.—Far. 3:​16-19.

11. Waɗanne abubuwa ne muke fama da su don mu ajizai ne?

11 Da yake mu ma ajizai ne, a wasu lokuta, mukan ji kunya, mu damu, kuma mu yi baƙin ciki. Muna fama da matsalolin nan ne domin zunubin da muka gāda. Ko da muna iya ƙoƙarinmu don mu inganta rayuwarmu kuma mu guje wa matsaloli, ba za mu taɓa rabuwa da matsaloli ba. Me ya sa? Littafi Mai Tsarki ya ce, an sa mu “yi rayuwa marar amfani.” (Rom. 8:20) Babu shakka, kowane ɗanadam zai yarda cewa hakan gaskiya ne. Alal misali, mutane da yawa a yau sun yi ƙoƙarin inganta mahalli, da kawo ƙarshen aikata laifuffuka, da talauci, da kuma sa a sami zaman lafiya. Amma haƙarsu ba ta cim ma ruwa ba. Ta yaya fansar Yesu za ta cece mu?

12. Wane bege ne fansar ta sa mu kasance da shi?

12 Fansar ta sa “za a ꞌyantar da halittun da kansu ma daga bauta ga ruɓewa.” (Rom. 8:21) Abin da hakan yake nufi shi ne, bayan mun zama marasa zunubi a Aljanna, ba za mu sake yi rashin lafiya ko baƙin ciki ba. Ban da haka, ba za mu ƙara jin kunya ko mu damu ba. Ƙari ga haka, “Sarkin Salama,” wato Yesu Kristi, wanda ya ba da ransa dominmu, zai yi mulki. Kuma zai taimaka mana ta wajen kawo ƙarshen matsalolin da muka gagara magancewa.—Isha. 9:​6, 7.

13. Mene ne kuma zai dace ka yi tunani a kai kafin ka halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu na wannan shekarar?

13 Ka yi tunanin yadda rayuwarka za ta kasance a lokacin da za ka zama marar zunubi. Kowane safe za ka tashi kana jin garau. Ba za ka taɓa damuwa cewa kai da waɗanda kake ƙauna za ku yi fama da yunwa, ko rashin lafiya, ko kuma ku mutu ba. Amma ko a yanzu ma, za ka iya kasancewa da kwanciyar hankali idan ka yi tunani a kan begen da kake da shi na nan gaba. (Ibran. 6:​18, 19) Kamar ƙugiyar da ke riƙe jirgin ruwa, begen da kake da shi zai sa ka ƙara kasancewa da bangaskiya. Kuma zai taimaka maka ka jimre kowace irin matsalar da kake fama da ita. Za ka iya kasance da tabbaci cewa, Jehobah zai “ba da lada ga duk waɗanda suke nemansa.” (Ibran. 11:6) Wannan kwanciyar hankalin da za ka iya samuwa yanzu da kuma begen da kake da shi na nan gaba, sun yiwu ne kawai domin fansar Yesu.

FANSAR TA SA MU KASANCE DA DANGANTAKA MAI KYAU DA JEHOBAH

14. Ta yaya zunubi ta shafi dangantakarmu da Jehobah, kuma me ya sa?

14 Tun daga lokacin da Adamu da Hauwaꞌu suka yi zunubi, dangantakar da ke tsakanin Allah da mutane ta yi tsami. Littafi Mai Tsarki ya ce, zunubi ya sa ꞌyanꞌadam suna gāba da Allah. (Rom. 8:​7, 8; Kol. 1:21) Me ya sa? Domin Jehobah mai tsarki ne kuma ya tsani zunubi. Game da Jehobah, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idanunka masu tsarki ne, sun fi ƙarfin ganin mugunta, ba ka so ka kalli laifi.” (Hab. 1:13) Zunubi ya lalatar da dangantakar da ke tsakanin ꞌyanꞌadam da Jehobah. Don haka, muna bukatar abin da zai taimaka mana mu sake kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah. Fansar Yesu ce ta taimaka mana mu yi hakan.

15. Ta yaya fansar Yesu ta sake ba mu damar kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah?

15 Littafi Mai Tsarki ya ce, Yesu “ne hadaya ta ɗaukar alhakin zunubanmu.” (1 Yoh. 2:2) Ta yaya fansar Yesu ta sake ba mu damar kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah? Mutuwar Yesu ta ba wa Jehobah ƙwararren hujja da ta sa ya amince ꞌyanꞌadam su sake kasancewa da dangantaka mai kyau da shi. (Rom. 3:​23-26) Ta kuma ba wa waɗanda suka bauta wa Jehobah da aminci kafin mutuwar Yesu damar zama masu adalci. (Far. 15:​1, 6) Ta yaya hakan ya yiwu? Hakan ya yiwu ne domin Jehobah yana da tabbaci cewa Yesu zai ba da fansar a madadin ꞌyanꞌadam. (Isha. 46:10) Babu shakka, fansar ta ba wa ꞌyanꞌadam damar sake kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah.

16. Wane abu ne kuma za ka iya yin tunani a kai kafin ka halarci Taron Tunawa da Mutuwar Yesu na wannan shekarar? (Ka kuma duba hoton.)

16 Ka yi tunani a kan abubuwan da kake mora yanzu don kana da dangantaka mai kyau da Jehobah. Alal misali, kana iya kiran Jehobah “Uba,” kamar yadda Yesu ya ce mu yi. (Mat. 6:9) A wasu lokuta ma, kana kiran Jehobah “Abokinka.” A duk lokacin da za mu kira Jehobah “Uba” ko kuma “Abokinmu,” ya kamata mu yi hakan cikin sauƙin kai da ban girma. Me ya sa? Domin mu masu zunubi ne, kuma ba mu cancanci mu kasance da dangantaka mai kyau da Allah ba. Fansar Yesu ce kawai ta sa hakan ya yiwu. Jehobah ne da son ransa ya ba da Ɗansa don mu iya sake kasancewa da dangantaka mai kyau da shi. (Kol. 1:​19, 20) Shi ya sa duk da cewa mu ajizai ne, za mu iya zama aminansa.

Sojojin Roma suna shirin rataye Yesu a kan gungume. Sojoji biyu suna kawo Yesu wurin da gungumen yake, wani kuma yana riƙe da guduma da ƙusa.

Mutuwar Yesu ce kawai ta sa ꞌyanꞌadam su sake iya kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah (Ka duba sakin layi na 16)


FANSAR TA NUNA YAWAN TAUSAYIN JEHOBAH

17. Ta yaya fansar Yesu ta nuna cewa Jehobah mai yawan tausayi ne? (Afisawa 2:​4, 5)

17 Fansar ta nuna cewa Jehobah “mai yawan tausayi ne.” Domin “tun saꞌad da muke matattu ta wurin zunubanmu, sai ya rayar da mu.” (Karanta Afisawa 2:​4, 5.) Kamar mutumin nan da gini ya faɗi a kansa, “waɗanda suke marmarin samun rai na har abada” sun san cewa suna bukatar wanda zai taimaka musu su sami ꞌyanci daga zunubin da suka gāda. (A. M. 13:48) Jehobah yana taimaka wa irin waɗannan mutanen ta wajen sa su koyi gaskiya game da Shi da Ɗansa. (Yoh. 17:3) Shaiɗan ya yi babban kuskure da ya ɗauka cewa idan Adamu da Hauwaꞌu suka yi zunubi, hakan zai hana Jehobah cika nufinsa.

18. Me ya kamata mu tuna yayin da muke tunani a kan fansar?

18 Yayin da muke tunani a kan abubuwan da muke morewa don fansar Yesu, muna bukatar mu tuna ainihin dalilin da ya sa Jehobah ya ba da fansar. Jehobah ya ba da fansar ba don kawai mu samu ceto ba, amma don ya warware zargin da Shaiɗan ya yi masa a lambun Adnin. (Far. 3:​1-5, 15) Ta wajen fansar, Jehobah ya nuna cewa abubuwan da Shaiɗan ya faɗa game da shi ƙarya ne. Fansar ta kuma nuna cewa Allah yana ƙaunar mu, domin mun sami ceto daga zunubi da mutuwa. Kuma duk da cewa mu ajizai ne, Jehobah ya nuna mana alheri ta wajen ba mu damar nuna cewa abubuwan da Shaiɗan ya faɗa game da shi ƙarya ne. (K. Mag. 27:11) Ta yaya za ka nuna godiya don fansar Yesu? Za mu amsa wannan tambayar a talifi na gaba.

TA YAYA FANSAR YESU TA SA . . .

  • Jehobah ya gafarta mana zunubanmu?

  • mu kasance da begen zama marasa zunubi a nan gaba?

  • mu sake kasancewa da dangantaka mai kyau da Jehobah?

WAƘA TA 19 Jibin Maraice na Ubangiji

a MAꞌANAR WASU KALMOMI: Fansa tana nufin abin da ake biya don a saki wanda yake a ɗaure. Mutuwar Yesu fansa ce domin ta sa ꞌyanꞌadam masu biyayya su sami ꞌyanci daga zunubi da mutuwa.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba