Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w26 Janairu pp. 26-31
  • Mu Riƙa Koyar da Gaskiya Cikin Alheri

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Mu Riƙa Koyar da Gaskiya Cikin Alheri
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • A INA NE ZA MU IYA SAMUN GASKIYA?
  • DALILIN DA YA SA MUKE GAYA WA MUTANE GASKIYA
  • TA YAYA ZA MU RIƘA FAƊIN GASKIYA?
  • LOKACIN DA YA KAMATA MU FAƊI GASKIYA
  • Ka San Bambancin Gaskiya da Karya?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2024
  • Ka Nemi Amsoshin Waɗannan Tambayoyin
    Tsarin Ayyuka na Taron Daꞌira na Mai Kula da Daꞌira na 2026
  • Jehobah Yakan Cika Dukan Alkawuransa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
  • Ka Kasance da Sauƙin Kai Idan Akwai Abubuwan da Ba Ka Sani Ba
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2026
w26 Janairu pp. 26-31

30 GA MARIS–5 GA AFRILU, 2026

WAƘA TA 76 Yin Waꞌazi Yana Sa Mu Murna

Mu Riƙa Koyar da Gaskiya Cikin Alheri

“ Yahweh Allah mai [gaskiya].”—ZAB. 31:5.

ABIN DA ZA MU KOYA

Za mu ga muhimmancin gaya wa mutane gaskiya yadda za ta ratsa zukatansu.

1. Idan muna so mu kasance a cikin iyalin Jehobah, me muke bukatar mu yi?

IDAN muka haɗu da wata ꞌyarꞌuwa ko ɗanꞌuwa a karo na farko, ɗaya daga cikin tambayoyin da mukan yi musu ita ce, “Ta yaya ka koyi gaskiya?” Wasu sukan ce iyayensu ne suka koya musu gaskiya. Wasu kuma sukan ce bai daɗe da suka koyi gaskiya ba. Me ya sa mukan amsa hakan? Domin muna rayuwa ne bisa ga gaskiyar da muka koya daga Kalmar Allah. Kuma idan muna so mu ci-gaba da zama a cikin iyalin Jehobah, muna bukatar mu ƙaunaci gaskiyar, kuma mu yi rayuwar da ta jitu da gaskiyar. Hanya ɗaya da za mu iya yin hakan ita ce, ta wurin faɗin gaskiya da yin abubuwa cikin gaskiya.—Zab. 15:​1-3.

2. (a) Mene ne mutane suka sani game da Yesu? (b) Mene ne mutane za su yi idan suka ji gaskiyar da Yesu yake koyarwa?

2 Komen da Yesu ya faɗa gaskiya ne. Har maƙiyansa ma sun san cewa komen da yake faɗa gaskiya ne, duk da cewa ba sa son hakan. (Mat. 22:16) Yesu ya gaya wa mabiyansa abin da mutane za su yi, idan suka ji gaskiyar da yake koyarwa. Ya ce: “Ɗa zai yi gāba da babansa, ꞌya za ta yi gāba da mamarta, matar ɗa kuma za ta yi gāba da mamar mijinta.” (Mat. 10:35) Yesu ba zai so mutane su sami matsala tsakaninsu don abin da shi da mabiyansa suke koyarwa ba. Amma abin da zai faru ke nan. (Mat. 23:37) Ya san cewa mutane za su kasance da raꞌayi kashi biyu game da koyarwarsa. Wasu za su so, wasu kuma za su ƙi.—2 Tas. 2:​9-11.

3. Mene ne za mu tattauna a wannan talifin?

3 Kamar Yesu, mu ma muna iya ƙoƙarinmu don mu faɗi gaskiya kowane lokaci, ko da mutane ba sa son hakan. Ƙari ga haka, muna waꞌazi da koyar da gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki, ko da hakan yana sa wasu fushi. Saboda haka, saꞌad da muke koyar da gaskiya, muna bukatar mu lura da yadda muke magana, da kuma lokacin da za mu yi hakan. A wannan talifin, za a fara da amsa wannan tambayar: A ina ne za mu sami gaskiya game da Jehobah? Bayan haka, sai mu amsa tambayoyin nan: Me ya sa ya kamata mu gaya wa mutane gaskiyar da ke Littafi Mai Tsarki? Ta yaya za mu yi hakan, kuma a wane lokaci ne ya dace mu yi hakan? Amsoshin tambayoyin nan za su taimaka mana mu yi wa mutane waꞌazi a hanyar da za ta ratsa zukatansu, kuma mu ƙara zama masu faɗin gaskiya.

A INA NE ZA MU IYA SAMUN GASKIYA?

4. Me ya sa muka ce Jehobah shi ne tushen gaskiya?

4 Jehobah ne Tushen gaskiya. Komen da yake faɗa gaskiya ne. Alal misali, abubuwan da ya faɗa game da abubuwan da suka dace da waɗanda ba su dace ba, gaskiya ne. (Zab. 19:9; 119:​142, 151) Idan ya ce wani abu zai faru, yana faruwa. (Isha. 55:​10, 11) A kullum yana cika alkawarinsa. (L. Ƙid. 23:19) Littafi Mai Tsarki ya ce, ba zai taɓa yiwu Allah ya yi ƙarya ba! (Ibran. 6:18) Shi ya sa ya dace sosai da ake kiran Jehobah, Allah mai gaskiya.—Zab. 31:5.

5. Me ya sa sanin abubuwa game da Allah bai da wuya? Ka bayyana. (Ayyukan Manzanni 17:27)

5 Wasu mutane suna ganin yana da wuya mu san abubuwa game da Jehobah, Allah mai gaskiya. Amma ba haka ba ne. Abubuwan da muke gani sun tabbatar mana cewa akwai Allah. (Rom. 1:20) Saꞌad da manzo Bulus yake magana da wasu mutanen Girka a Atina da suka yi karatu sosai, ya gaya musu cewa, Allah yana so mu “neme shi” kuma bai da “nesa da kowannenmu.” (Karanta Ayyukan Manzanni 17:27.) Jehobah ne da kansa yake jawo mutane masu sauƙin kai su zo su san gaskiya game da shi.—Yoh. 6:44.

6. (a) Ka ambata wasu abubuwan da ke Littafi Mai Tsarki? (b) Me ya sa muke godiya don gaskiyar nan da muka sani?

6 Hanya ɗaya da za mu iya sanin Jehobah ita ce, ta wajen yin nazarin Littafi Mai Tsarki. Ruhu mai tsarki ne ya taimaka wa waɗanda suka rubuta Littafi Mai Tsarki. (2 Bit. 1:​20, 21) Saboda haka, komen da ke Littafi Mai Tsarki gaskiya ne, kuma za mu iya yarda da abin da ya faɗa. Alal misali, za mu iya yarda da abin da ya faɗa game da yadda aka halicci sama da ƙasa. (Far. 1:​1, 26) Za mu iya yarda da abin da ya faɗa game da yadda dukanmu muka zama masu zunubi. Da kuma dalilin da ya sa muke shan wahala da mutuwa. (Rom. 5:12; 6:23) Mun kuma yarda da abin da ya faɗa cewa, Jehobah zai yi amfani da Ɗansa ya magance matsalolin da “uban ƙarya” wato Shaiɗan ya jawo. (Yoh. 8:44; Rom. 16:20) Ƙari ga haka, mun yarda da abin da Littafi Mai Tsarki ya faɗa cewa, Yesu zai hallaka mugaye, ya ta da matattu, ya mai da duniya aljanna, kuma ya taimaka mana mu zama marasa zunubi. (Yoh. 11:​25, 26; 1 Yoh. 3:8) Jehobah ya koya mana gaskiya game da kansa, kuma ya ba mu damar koya ma wasu. Hakan babban gata ne.—Mat. 28:​19, 20.

DALILIN DA YA SA MUKE GAYA WA MUTANE GASKIYA

7-8. Shin, Jehobah ya damu da dalilin da ya sa muke faɗin gaskiya? Ka ba da misali. (Markus 3:​11, 12) (Ka kuma duba hotunan.)

7 Kamar yadda aka ambata ɗazu, muna bukatar mu riƙa faɗin gaskiya idan muna so mu kasance a cikin iyalin Jehobah. Amma ba shi ke nan ba. Jehobah ya damu da dalilin da ya sa muke faɗin gaskiya. Bari mu yi laꞌakari da abin da ya faru saꞌad da Yesu yake duniya. (Karanta Markus 3:​11, 12.) Saꞌad da Yesu yake waꞌazi kusa da Tekun Galili, mutane da yawa sun taru. A cikinsu, akwai masu aljannu da suka faɗi a gaban Yesu suna cewa: “Kai ne Ɗan Allah.” Me ya sa aljannun suka faɗi wannan gaskiya game da Yesu? Mai yiwuwa suna son mutane su ga kamar abubuwan da suke yi gaskiya ne. Kuma daga baya su sa su daina bauta wa Jehobah. Abin da aljannun suka faɗa gaskiya ne, amma dalilin da ya sa suka faɗi hakan ba daidai ba ne. Yesu ya san abin da ya sa suka yi hakan, kuma bai ji daɗi ba. Shi ya sa ya ja musu kunne kada su gaya wa mutane ko wane ne shi.

8 Mene ne muka koya daga wannan labarin? Jehobah ya damu da dalilin da ya sa muke faɗan wani abu. Saboda haka, yana da muhimmanci mu koya wa mutane gaskiya game da Jehobah don muna ƙaunar sa da dukan zuciyarmu. Kuma idan suna ƙoƙarin yaba mana don abin da muka koya musu, wajibi ne mu miƙa yabon ga Jehobah!—Mat. 5:16; ka kuma duba Ayyukan Manzanni 14:​12-15.

Wata ꞌyarꞌuwa tana nazarin Littafi Mai Tsarki da wata mata. Na 1. ꞌYarꞌuwar tana magana game da kanta kuma ta kife Littafi Mai Tsarki a kan tebur. Na 2. ꞌYarꞌuwar ta buɗe Littafi Mai Tsarki tana nuna wa matar wani nassi.

Saꞌad da kake koya wa wani gaskiya, waye ne zai dace ya karɓi yabon? (Ka duba sakin layi na 7-8)


9. Me ya kamata mu guje wa, kuma me ya sa?

9 Ga wani yanayi kuma da ya kamata mu guje wa. A ce wani dattijo ya gaya mana wani abin da ba kowa ne ya sani ba, sai mu kuma muka je muka gaya ma wasu. Idan daga baya mutanen da muka gaya musu suka gane cewa gaskiya ne muka faɗa, hakan zai iya sa su ga kamar mun san abubuwa da dama da wasu ba su sani ba. Mai yiwuwa, za su soma ɗaukanmu da muhimmanci fiye da yadda ya kamata. Amma hakan ba zai sa Jehobah farin ciki ba. (K. Mag. 11:13) Me ya sa? Domin dalilin da ya sa muka faɗi hakan ba daidai ba ne. Ban da hakan, ko da yake abin da muka faɗa gaskiya ne, ba mu ne ya kamata mu gaya wa mutane ba.

TA YAYA ZA MU RIƘA FAƊIN GASKIYA?

10. Mene ne ake nufi da cewa maganarmu “ta kasance da alheri da kuma daɗin ji”? (Kolosiyawa 4:6)

10 Karanta Kolosiyawa 4:6. Manzo Bulus ya tuna wa Kiristocin da ke Kolosi cewa, ya kamata abubuwan da suke faɗa su “kasance da alheri da kuma daɗin ji.” Mene ne hakan yake nufi? Ainihin furucin Girkanci da aka yi amfani da shi a wannan ayar, yana nufin mu riƙa faɗan abubuwan da za su amfani mutane, kuma mu yi hakan cikin alheri.

11-12. Me ya sa zai dace mu yi laꞌakari da yadda muke koya wa mutane gaskiya? Ka ba da misali. (Ka kuma duba hotunan.)

11 Zai dace mu bi shawarar Bulus saꞌad da muke koya wa mutane gaskiya. An kwatanta gaskiyar da ke Kalmar Allah da takobi mai baki biyu da za ta iya raba ruhu da rai. Hakan yana nufin cewa, gaskiyar da ke Kalmar Allah za ta iya sa mu gane ainihin yadda muke tunani, da dalilin da ya sa muke yin abubuwa. (Ibran. 4:12) Amma idan ba mu yi amfani da Kalmar Allah a hanyar da ta dace ba, za mu iya sa mutane su yi fushi, ko kuma mu shiga gardama da su. Ta yaya hakan zai iya faruwa?

12 A ce muna waꞌazi, sai muka haɗu da wani mutum mai yin amfani da gumaka wajen yin ibada, yana bikin Kirsimati da kuma Ista. Za mu iya yin amfani da Littafi Mai Tsarki mu nuna wa mutumin cewa, bauta wa gumaka wawanci ne don ba su da rai. Kuma mu nuna masa cewa bikin Kirsimati da Ista bikin arna ne. (Isha. 44:​14-20; 2 Kor. 6:​14-17) Idan muka gaya masa abubuwan nan a lokaci na farko da muka haɗu da shi, gaskiya ne muka faɗa. Amma hakan ba zai nuna cewa muna amfani da Kalmar Allah a hanyar da ta dace ba.

Wani ɗanꞌuwa da matarsa suna yi wa wani mutum waꞌazi a bakin kofar gidansa, yayin da iyalinsa suke sa kayan ado a kan bishiyar Kirsimati. Na 1. Ɗanꞌuwan ya nuna wa mutumin talifin nan mai jigo, “Mene Ne Littafi Mai Tsarki Ya Faɗa Game da Kirsimati?” da ke jw.org/ha. Mutumin ya naɗe hannu, fuskarsa a ɗaure yayin da yake saurara. Na 2. Ɗanꞌuwan ya nuna wa mutumin talifin nan mai jigo “How to Be a Good Dad” da ke jw.org. Mutumin yana saurara yana murmushi.

Ta yaya za ka riƙa koyar da gaskiya a hanyar da ta dace? (Ka duba sakin layi na 11-12)a


13. Ta yaya za mu sa abubuwan da muke faɗa su zama da daɗin ji?

13 Bulus ya kuma ce, abubuwan da muke faɗa su zama da daɗin ji. Hakan ba ya nufin cewa ba za mu faɗi gaskiya yadda take ba. A maimakon haka, yana ƙarfafa mu mu koya wa mutane gaskiya yadda za su ji daɗinsa. (Ayu. 12:11) Yin hakan bai da sauƙi. Idan ya zo ga abinci, a yawancin lokuta mukan ga kamar abin da ya mana daɗi, zai yi wa wasu daɗi. Amma hakan ba lallai ba ne. Haka ma, za mu iya ganin kamar kowa yana jin daɗin yadda muke magana. Amma mai yiwuwa ba haka yake ba. Alal misali, a alꞌadar wasu mutane, suna iya faɗan raꞌayinsu kai tsaye ko da suna magana ne da wanda ya girme su. Wasu kuma da alꞌadar su dabam ne, za su iya gani kamar bai dace ba ko kuma reni ne. Bulus ya kuma ƙara da cewa, “ku san irin amsar da ya yi kyau ku ba kowa.” Hakan yana nufin cewa saꞌad da muke magana da mutane, mu yi shi yadda za su ji daɗinsa, ba yadda muke so ba ko kuma yadda muke yi a alꞌadarmu ba.

LOKACIN DA YA KAMATA MU FAƊI GASKIYA

14. Shin, dukan abubuwan da Yesu ya sani ne ya koya ma almajiransa lokacin da yake duniya? Ka bayyana.

14 A kowane lokaci, Yesu yana yi wa mabiyansa magana da alheri. Kuma ya koya musu abubuwa da yawa. (Mar. 6:34) Amma akwai abubuwa da yawa da ba su sani ba. Yesu bai yi ƙoƙarin koya musu dukan abubuwan da ya sani ba. Ya yi laꞌakari da yanayinsu. Ya san cewa lokacin da zai koya musu wasu abubuwa bai kai ba. Ya ma gaya musu cewa ba za su fahimci wasu gaskiyar da yake so ya koya musu a lokacin ba. (Yoh. 16:12) Mene ne hakan ya koya mana?

15. Ya kamata mu koya wa ɗalibanmu dukan abubuwan da muka sani a tāke ne? Ka bayyana. (Karin Magana 25:11) (Ka kuma duba hoton.)

15 Misalin Yesu ya koya mana cewa, ba dukan gaskiyar da muka sani ne za mu koya wa mutane a tāke ba. Ta yaya za mu bi misalin Yesu? Wajibi ne mu yi laꞌakari da yanayin da mutane suke ciki. Bari mu sake yin laꞌakari da mutumin nan da yake jin daɗin yin bikin Kirsimati da kuma Ista tare da iyalinsa. Mun san cewa waɗannan bukukuwan arna ne, kuma Allah bai amince da su ba. Amma a ce mun soma nazarin Littafi Mai Tsarki da mutumin mako ɗaya ko biyu kafin bikin Kirsimati, kuma muka nuna masa cewa Allah bai amince da bukukuwan nan ba. Shin, zai dace mu ɗauka cewa zai daina yin bukukuwan nan tāke? Gaskiyar ita ce, wasu mutane sukan soma yin abin da suka koya daga Littafi Mai Tsarki nan da nan. Wasu kuma yakan ɗauki lokaci kafin su canja raꞌayinsu kuma su ɗauki mataki. Za mu iya taimaka wa ɗalibanmu su sami ci-gaba idan muka gaya musu abin da suke bukatar su sani, a lokacin da ya dace. Wato lokacin da zai yi musu sauƙi su fahimta.—Karanta Karin Magana 25:11.

Ɗanꞌuwan da matarsa suna nazari da mutumin a gidansa da ƙasidar nan, “Ka Ji Daɗin Rayuwa Har Abada!” kuma bishiyar Kirsimatin yana gefe.

Kamar Yesu, zai dace ka san lokacin da ya kamata ka koyar da gaskiya da kuma yawan abin da za ka faɗa (Ka duba sakin layi na 15)


16. Ta yaya za mu taimaka wa ɗalibanmu su ci-gaba da bauta wa Jehobah?

16 Taimaka wa mutane su koyi game da Jehobah na cikin abubuwan da suke sa mu farin ciki. Za mu iya taimaka musu su ci-gaba da bauta wa Jehobah idan muka yi waɗannan abubuwan: Mu kasance da halaye masu kyau da za su iya yin koyi da su. (3 Yoh. 3, 4) Mu tabbata cewa yadda muke rayuwa, yana nuna cewa mun amince da alkawuran da ke Littafi Mai Tsarki. Mu kasance da niyya mai kyau saꞌad da muke faɗin gaskiya. Ƙari ga haka, saꞌad da muke koya wa mutane gaskiya, mu yi hakan cikin alheri, da kuma a lokacin da ya dace. Kuma idan aka yaba mana, zai dace mu miƙa yabon ga Jehobah. Yin waɗannan abubuwan, za su nuna cewa muna bauta wa Jehobah, Allah na gaskiya.

MENE NE KA KOYA DAGA NASOSSIN NAN?

  • Ayyukan Manzanni 17:27

  • Kolosiyawa 4:6

  • Karin Magana 25:11

WAƘA TA 160 Albishirinku!

a BAYANI A KAN HOTUNA: A hoto na farko, wani ɗanꞌuwa ya ga bishiyar Kirsimati a gidan wani mutum, sai ya nuna masa wani talifi da ya nuna cewa Kirsimati bikin arna ne. A hoto na biyu, ɗanꞌuwan ya nuna wa mutumin wani talifin da ke ɗauke da shawarwari masu kyau game da yadda mahaifi zai kula da yaransa. A ganinka, wane batu ne zai fi ratsa zuciyar mutum a wannan lokacin?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba