SHAWARA A KAN YIN NAZARI
Ka Ji Kamar Kana Wurin
Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da labaran abubuwa da yawa da suka faru, da za su iya koya mana darussa masu kyau. Idan ka yi tunani a kan labaran nan, kuma ka ji kamar kana wurin saꞌad da suka faru, za ka ƙara fahimta kuma ka amfana daga abin da ka karanta. Ga wasu abubuwan da za su taimaka maka ka iya yin hakan.
Ka yi karatu da babbar murya. Karanta Littafi Mai Tsarki da babbar murya zai taimaka maka ka fahimci batun da kyau. Idan kuna karatun a matsayin iyali, za ku ƙara fahimtar batun da kyau idan kowannenku ya ɗauki matsayin wani dabam a labarin, kuma ya karanta abin da ya faɗa.
Ka yi tunani a kan yanayin da suke ciki. Saꞌad da kake karanta Littafi Mai Tsarki, ka yi ƙoƙari ka fahimci yadda mutanen da ke labarin suke tunani da kuma yadda suke ji a lokacin. Alal misali, ka tambayi kanka: ‘Me ya sa mutumin ya faɗa ko ya yi abin da ya yi? Da a ce ni ne yaya zan ji ko kuma wani irin tunani ne zan yi?’
Ka yi zane. Zana labarin da kake karantawa zai taimaka maka ka tuna, ka gane, kuma ka ji kamar kana warin. Kada ka damu ko da abin da ka zana ba abin a zo a gani ba.