“ Ku Kiyaye Ɗayantakar Nan da Ruhu Ya Ba Ku”
MANZO BULUS ya ƙarfafa Kiristocin da ke Afisa cewa, ku ci-gaba da “yarda da juna cikin ƙauna. Ku yi ƙwazo sosai ku kiyaye ɗayantakar nan da ruhu ya ba ku, ta wurin salamar da ta ɗaure ku tare.”—Afis. 4:2, 3.
“Ɗayantaka,” ko haɗin kai da ke tsakaninmu, ruhu mai tsarki ne yake sa ya kasance. Hakan yana nufin cewa ruhun Allah ne yake sa mutane su kasance da haɗin kai. Amma kamar yadda Bulus ya ambata, muna bukatar mu yi wani abu don mu ci-gaba da kasancewa da haɗin kai. Mene ne muke bukatar mu yi? Kowane Kirista yana bukatar ya yi ƙwazo sosai wajen ‘kiyaye ɗayantakar nan da ruhu ya ba mu.’
Alal misali, a ce wani ya ba ka sabuwar mota. Waye ne yake da hakkin kula da motar? Gaskiyar ita ce, ba za ka ɗora wa wanda ya ba ka motar laifi idan motar ta lalace don ba ka kula da ita ba.
Haka ma, haɗin kai da ke tsakaninmu kyauta ce daga wurin Jehobah. Amma kowannenmu yana da hakkin sa mu ci-gaba da kasancewa da haɗin kai. Idan babu zaman lafiya tsakaninmu da wani ɗanꞌuwa ko wata ꞌyarꞌuwa, zai dace mu tambayi kanmu, ‘Shin ina yin iya ƙoƙarina don a kasance da haɗin kai a ikilisiya?’
MU YI IYA ƘOƘARINMU MU KASANCE DA HAƊIN KAI
Kamar yadda Bulus ya faɗa, a wasu lokuta muna bukatar mu yi ƙoƙari sosai don mu kiyaye haɗin kai da ke tsakaninmu. Muna bukatar hakan musamman a lokacin da wani ɗanꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa ta yi mana wani abin da ya ɓata mana rai. Shin, a duk lokacin da wani ya yi maka laifi ne ya kamata ka je ka same shi ka yi masa magana? Ba lallai ba. Ka tambayi kanka, ‘Yin hakan zai sa yanayin ya daɗa muni ne, ko zai sa mu sasanta?’ A wasu lokuta abin da ya fi alheri shi ne, mu yafe ko kuma mu manta da zancen.—K. Mag. 19:11; Mar. 11:25.
Ka tambayi kanka, ‘Yin hakan zai sa yanayin ya daɗa muni ne, ko zai sa mu sasanta?’
Kamar yadda Bulus ya rubuta, muna bukatar mu ci-gaba “da haƙuri, . . . da juna cikin ƙauna.” (Afis. 4:2) Wani littafi ya ce, abin da manzo Bulus ya faɗa yana iya nufin “ɗaukan mutane yadda suke.” Hakan yana nufin mu amince cewa ꞌyanꞌuwanmu ajizai ne kamar mu. Ko da yake dukanmu muna ƙoƙari mu kasance da “sabon hali.” (Afis. 4:23, 24) Babu waninmu da zai iya yin hakan babu kuskure. (Rom. 3:23) Idan mun ci-gaba da tuna cewa dukanmu ajizai ne, zai yi mana sauƙi mu ci-gaba da haƙuri da juna, kuma mu gafarta wa juna. Ta yin hakan za mu ‘kiyaye ɗayantakar nan da ruhu ya ba mu.’
Idan muka yafe kuma muka manta da laifofin da wasu suka yi mana, hakan zai sa mu kasance da salama a cikin ikilisiya. Kalmar Girkanci da aka fassara zuwa “salamar da ta ɗaure ku tare” a Afisawa 4:3, daidai yake da kalmar nan “jijiyoyi” da ke Kolosiyawa 2:19. Irin jijiyoyin nan, suna kama da igiyoyi masu ƙarfi da ke haɗa ƙasusuwa biyu. Haka ma, idan muna ƙaunar ꞌyanꞌuwanmu kuma muna zaman lafiya da su, hakan zai ƙarfafa dangantakar da ke tsakaninmu da su ko da ba ma jin daɗin abin da suke yi.
Saboda haka, idan wani ɗanꞌuwa ya yi maka laifi, ko ya ɓata maka rai, ko ya yi wani abin da ba ka so, ka tausaya masa, maimakon ka mai da hankali a kan abin da ya yi da ba daidai ba. (Kol. 3:12) Dukanmu ajizai ne, kuma a wasu lokuta, mukan yi abin da wani ba ya so. Sanin hakan zai taimaka mana mu ci-gaba da yin iya ƙoƙarinmu wajen ‘kiyaye ɗayantakar nan da ruhu ya ba mu.’