Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w10 9/15 pp. 16-20
  • Haɗin Kai Na Kiristoci Yana Ɗaukaka Allah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Haɗin Kai Na Kiristoci Yana Ɗaukaka Allah
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Ƙananan Jigo
  • Makamantan Littattafai
  • Wasiƙar da Ta Nanata Haɗin Kai
  • Abin da ya Sa Haɗin Kai Yake Bukatan Ƙoƙartawa Sosai
  • “Kyautai ga Mutane” Suna Ɗaukaka Haɗin Kai
  • Ka Koyi Sababbin Halaye
  • Ka Koyi Sababbin Hanyoyin Yin Magana
  • Ƙaunar Allah Tana Haɗa Kanmu
  • Ana Gane Masu Bauta Ta Gaskiya Ta Haɗin Kansu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
  • Jehobah Yana Tattara Iyalinsa
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2012
  • Taron Tuna da Mutuwar Yesu na Kawo Hadin Kai
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2018
  • “Ku Kiyaye Ɗayantakar Nan da Ruhu Ya Ba Ku”
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2010
w10 9/15 pp. 16-20

Haɗin Kai Na Kiristoci Yana Ɗaukaka Allah

“Kuna ƙwazo ku kiyaye ɗayantuwar Ruhu.”—AFIS. 4:3.

1. Ta yaya Kiristoci na ƙarni na farko a Afisa suka ɗaukaka Allah?

HAƊIN kai na ikilisiyar Kirista a Afisa ta dā ya ɗaukaka Allah na gaskiya, Jehobah. A wannan cibiyar kasuwanci, wasu ’yan’uwa Kiristoci mawadata ne masu bayi, yayin da wasu bayi ne kuma wataƙila matalauta ne sosai. (Afis. 6:5, 9) Wasu a cikinsu Yahudawa ne da suka koyi gaskiya a cikin watanni uku da manzo Bulus ya yi yana magana a cikin majami’arsu. Wasu kuma a dā suna bauta wa allan Artimas kuma sun yi sihiri. (A. M. 19:8, 19, 26) A bayyane yake cewa Kiristanci na gaskiya ya jawo mutane daga wurare dabam dabam. Bulus ya fahimci cewa an ɗaukaka Jehobah ta wurin haɗin kan ikilisiya. Manzon ya rubuta: “Ɗaukaka tā tabbata a gare shi a ikilisiya”—Afi 3:21, Littafi Mai Tsarki.

2. Menene ya yi wa haɗin kan Kiristoci da ke Afisa barazana?

2 Amma, an yi wa haɗin kan ikilisiyar Afisa barazana. Bulus ya yi wa dattawan kashedi: “Daga cikin tsakiyarku kuma mutane za su tashi, suna faɗin karkatattun zantattuka, domin su janye masu-bi bayansu.” (A. M. 20:30) Wasu ’yan’uwa har ila suna nuna halin rarrabuwa da Bulus ya faɗa cewa yana “aiki yanzu a cikin ’ya’yan kangara.”—Afis. 2:2; 4:22.

Wasiƙar da Ta Nanata Haɗin Kai

3, 4. Ta yaya wasiƙar Bulus ga Afisawa ta nanata haɗin kai?

3 Bulus ya fahimci cewa idan Kiristoci za su ci gaba da yin abubuwa cikin haɗin kai, dole ne kowannensu ya yi ƙoƙari sosai ya sa a kasance da haɗin kai. Allah ya hure Bulus ya rubuta wasiƙa ga Afisawa wadda haɗin kai ne jigonta. Alal misali, Bulus ya rubuta game da nufin Allah na “tattara dukan abu cikin Kristi.” (Afis. 1:10) Ya kuma kamanta Kiristoci da duwatsu dabam dabam da ake gini da su. “Dukan gini, hadadde ne, yana girma sai ya zama haikali mai-tsarki cikin Ubangiji.” (Afis. 2:20, 21) Ƙari ga haka, Bulus ya nanata haɗin kan Yahudawa da ’Yan al’ummai Kiristoci, ya kuma tunasar da ’yan’uwan cewa Allah ne ya halicci dukansu. Ya kira Jehobah “Uba, wanda kowane iyali cikin sama da duniya ya sami sunansa daga gare shi.”—Afis. 3:5, 6, 14, 15.

4 Yayin da muke bincika sura na huɗu na littafin Afisawa, za mu ga dalilin da ya sa haɗin kai yake bukatan ƙoƙari, yadda Jehobah yake taimaka mana mu kasance da haɗin kai, da kuma halayen da za su taimaka mana mu kasance da haɗin kai. Me ya sa ba za ka karanta dukan surar ba, don ka amfana daga nazarin sosai?

Abin da ya Sa Haɗin Kai Yake Bukatan Ƙoƙartawa Sosai

5. Me ya sa mala’ikun Allah za su iya yin bauta cikin haɗin kai, amma me ya sa kasancewa da haɗin kai zai fi yi mana wuya?

5 Bulus ya roƙi ’yan’uwansa a Afisa su yi ‘ƙwazo su kiyaye ɗayantuwar ruhu.’ (Afis. 4:3) Don mu fahimci bukatar ƙoƙartawa a wannan batun, bari mu yi la’akari da mala’ikun Allah. Babu abubuwa biyu masu rai a duniya da suke da cikakken kamanni, saboda haka za mu iya kammala cewa Jehobah ya albarkaci kowanne cikin miliyoyin mala’ikunsa a hanya ta musamman. (Dan. 7:10) Duk da haka, suna bauta wa Jehobah cikin haɗin kai domin dukansu suna sauraronsa kuma suna yin nufinsa. (Karanta Zabura 103:20, 21.) Ko da yake mala’iku masu aminci suna da halaye dabam dabam, Kiristoci ma suna da aibobi dabam dabam. Wannan zai iya sa kasancewa da haɗin kai ya yi wuya.

6. Waɗanne halaye ne za su taimaka mana mu ji daɗin ba da haɗin kai ga ’yan’uwa da suke da aibobi dabam da namu?

6 Yayin da mutane ajizai suke ƙoƙari su kasance da haɗin kai, suna iya samun matsaloli da sauƙi. Alal misali, idan ɗan’uwa da yake da sauƙin hali amma sau da yawa yana zuwan taro a makare yana bauta wa Jehobah da ɗan’uwa da yake zuwa da wuri amma yana saurin fushi kuma fa? Kowannensu yana iya jin cewa halin ɗayan bai dace ba amma ya mance cewa akwai fannoni na halinsa ma da ba su da kyau. Ta yaya irin waɗannan ’yan’uwa biyu za su yi hidima tare cikin haɗin kai? Ka lura da yadda halayen da aka ambata a kalaman Bulus na gaba za su taimaka musu. Sai ka yi tunanin yadda za mu ɗaukaka haɗin kai ta wajen koyan irin waɗannan halayen. Bulus ya rubuta: “Ina roƙonku ku yi tafiya . . . da dukan tawali’u da ladabi, da jimrewa, kuna haƙuri da junanku cikin ƙauna; kuna ƙwazo ku kiyaye ɗayantuwar Ruhu cikin ɗaurin salama.”—Afis. 4:1-3.

7. Me ya sa yake da muhimmanci mu yi ƙoƙari mu kasance da haɗin kai da sauran Kiristoci ajizai?

7 Koyan bauta wa Allah cikin haɗin kai da mutane ajizai yana da muhimmanci domin jiki ɗaya ne kawai ake da shi na masu bauta ta gaskiya. “Akwai jiki ɗaya, da Ruhu ɗaya, kamar yadda aka kiraye ku kuma cikin begen nan ɗaya na kiranku; Ubangiji ɗaya, imani ɗaya, baftisma ɗaya, Allah ɗaya, shi Uban duka.” (Afis. 4:4-6) An haɗa ruhun Jehobah da albarka da yin cuɗanya da ’yan’uwa da Allah yake amfani da su. Ko da wani a cikin ikilisiya ya ɓata mana rai, ina za mu tafi? Babu wani wuri dabam da za mu ji maganar rai na har abada.—Yoh. 6:68.

“Kyautai ga Mutane” Suna Ɗaukaka Haɗin Kai

8. Menene Kristi yake amfani da shi don ya taimaka mana mu guji tasiri na rarrabuwa?

8 Bulus ya yi amfani da abin da sojoji a zamanin dā suka saba yi don ya kwatanta yadda Yesu ya yi tanadin “kyautai ga mutane” don su taimaki ikilisiya ta kasance da haɗin kai. Sojan da ya ci yaƙi zai iya kawo wani bawa gida don ya taimaka wa matarsa da aikin gida. (Zab. 68:1, 12, 18) Hakan nan ma, nasarar da Yesu ya ci bisa duniya ta sa ya samu bayi masu yawa da yardan rai. (Karanta Afisawa 4:7, 8.) Yaya Yesu ya yi amfani da waɗannan bayi na alama? “Ya kuma ba da waɗansu su zama manzanni; waɗansu, annabawa; waɗansu, masu-wa’azin bishara; waɗansu, Fastoci wato makiyaya da malaman koyarwa; domin su shiriya tsarkaka, saboda aikin hidima na bishara, domin ginin jikin Kristi: har dukanmu mu kai zuwa ɗayantuwar imani.”—Afis. 4:11-13.

9. (a) Ta yaya “kyautai ga mutane” suke taimaka mana mu kasance da haɗin kai? (b) Me ya sa kowanne mutum da ke cikin ikilisiya zai sa ta kasance da haɗin kai?

9 A matsayin makiyaya masu ƙauna, waɗannan “kyautai ga mutane” suna taimaka mana mu kasance da haɗin kai. Alal misali, idan dattijo a cikin ikilisiya ya lura cewa ’yan’uwa biyu suna ‘homa suna cakunan juna,’ zai iya sa ikilisiyar ta kasance da haɗin kai sosai ta wajen ba da gargaɗi don ya daidaita su “cikin ruhun tawali’u.” (Gal. 5:26–6:1) A matsayin malamai, waɗannan “kyautai ga mutane” suna taimaka mana mu kasance da bangaskiya mai ƙarfi bisa koyarwar Littafi Mai Tsarki. Ta haka suna ɗaukaka haɗin kai kuma suna taimaka mana mu samu ci gaba mu zama Kiristoci da suka manyanta. Bulus ya rubuta cewa za a yi hakan domin “kada nan gaba mu zama yara, waɗanda ana wofar da su suna lillo ga kowace iskan koyarwa, ta wurin rudun mutane masu-gwaninta zuwa makidar saɓo.” (Afis. 4:13, 14) Ya kamata kowane Kirista ya sa ’yan’uwa su kasance da haɗin kai, kamar yadda kowace gaɓa na jikinmu na zahiri yake ƙarfafa sauran ta wajen yi musu tanadin abin da suke bukata.—Karanta Afisawa 4:15, 16.

Ka Koyi Sababbin Halaye

10. Ta yaya lalata za ta kawo rashin haɗin kai?

10 Ka lura cewa sura ta huɗu na wasiƙar Bulus zuwa ga Afisawa ta nuna cewa nuna ƙauna zai sa mu kasance da haɗin kai a matsayin Kiristoci da suka manyanta? Bayan haka, ta nuna abin da ƙauna ta ƙunsa. Alal misali, bin hanyar ƙauna ta hana yin fasikanci da ƙazaman halaye. Bulus ya aririce ’yan’uwansa kada su “ƙara tafiya irin tafiya da Al’ummai suke yi.” Waɗannan mutanen “sun wuce gaban su ji” kuma “sun ba da kansu ga lalata.” (Afis. 4:17-19) Duniya ta lalata da muke zama ciki tana sa haɗin kanmu cikin haɗari. Mutane suna wargi game da fasikanci, suna rera waƙa game da shi, suna kallon shi don nishaɗi, kuma suna yin shi a ɓoye ko kuma a fili. Duk da haka, har ma yin kwarkwasa, wadda ta ƙunshi yin kamar kana son wata da ba ka da niyyar aurenta, zai iya sa ka bar Jehobah da kuma ikilisiya. Me ya sa? Domin tana kai ga yin fasikanci cikin sauƙi. Kuma, kwarkwasa da ke sa wanda ya yi aure ya yi zina za ta iya raba yara daga iyayensu da kuma ma’aurata marasa laifi daga abokan aurensu. Babu shakka tana kawo rarrabuwa! Da dalili mai kyau Bulus ya rubuta: “Ba haka kuka koyi Kristi ba”!—Afis. 4:20, 21.

11. Littafi Mai Tsarki ya ƙarfafa Kiristoci su yi wane canji?

11 Bulus ya nanata cewa mu bar hanyoyin tunani da ke kawo jayayya, maimakon haka mu koyi halayen da za su taimaka mana mu zauna da mutane cikin haɗin kai. Ya ce: “Ku tuɓe, ga zance irin zamanku na dā, tsohon mutum, wanda yana ƙara lalacewa bisa ga sha’awoyin yaudara; ku sabonta kuma cikin ruhun azancinku, ku yafa sabon mutum, wanda an halitta shi bisa ga Allah cikin adalci da tsarkin gaskiya.” (Afis. 4:22-24) Ta yaya za mu ‘sabonta kuma cikin ruhun azancinmu’? Idan muka yi bimbini cikin godiya game da abin da muka koya daga Kalmar Allah da kuma misali mai kyau na Kiristoci da suka manyanta, tare da ƙoƙartawa za mu samu sabon hali da aka ‘halitta bisa ga nufin Allah.’

Ka Koyi Sababbin Hanyoyin Yin Magana

12. Ta yaya faɗin gaskiya yake kawo haɗin kai, me ya sa yake wa wasu wuya su riƙa faɗin gaskiya?

12 Faɗin gaskiya yana da muhimmanci ga waɗanda suke cikin iyali ɗaya ko kuma ikilisiya. Yin magana cikin kirki babu ɓoye ɓoye yana iya sa mutane su zama abokai. (Yoh. 15:15) Idan mutum ya yi ƙarya ga ɗan’uwansa fa? Idan ɗan’uwansa ya gane, gami na aminci a tsakaninsu zai yi sanyi. Shi ya sa Bulus ya rubuta: “Ku riƙa faɗi wa junanku da makwabtanku gaskiya . . . gama mu gaɓaɓuwa ne na junanmu.” (Afis. 4:25) Wanda ya saba yin ƙarya, wataƙila ya soma tun yana yaro, zai yi masa wuya ya soma faɗin gaskiya. Amma Jehobah zai yi farin ciki don ƙoƙarin da yake yi ya canja kuma zai taimake shi.

13. Menene daina zage-zage ya ƙunsa?

13 Jehobah yana koya mana mu ɗaukaka daraja da haɗin kai a cikin ikilisiya da iyali ta wajen kula da yadda muke magana sosai. “Kada kowane ruɓaɓen zance shi fita daga cikin bakinku . . . Bari dukan ɗacin zuciya, da hasala, da fushi, da hargowa, da zage-zage, su kawu daga gare ku, tare da dukan ƙeta.” (Afis. 4:29, 31) Hanya guda da za mu guji baƙar magana ita ce mu koyi halin daraja mutane. Alal misali, mutumin da yake zagin matarsa ya kamata ya yi ƙoƙari ya canja halin da yake nuna mata, musamman yayin da ya koyi yadda Jehobah yake daraja mata. Allah ya shafa wasu mata da ruhu mai tsarki, kuma ya ba su begen yin sarauta tare da Yesu. (Gal. 3:28; 1 Bit. 3:7) Hakazalika, macen da take da halin zagin maigidanta ya kamata ta canja yayin da ta koyi yadda Yesu ya kame kansa a lokacin da aka ɓata masa rai.—1 Bit. 2:21-23.

14. Me ya sa nuna fushi yake da haɗari?

14 Rashin kame fushi yana da nasaba da zage-zage. Wannan ma zai iya raba waɗanda suka san juna. Yin fushi yana kama ne da wuta. Yana iya ya zama gobara kuma ya yi ɓarna. (Mis. 29:22) Wanda aka ba haushi ya kamata ya mai da hankali ya kame kansa don ya guji ɓata dangantaka mai kyau. Ya kamata Kiristoci su riƙa gafartawa, kada su riƙe mutum a zuciyarsu da kuma su sake ta da maganar. (Zab. 37:8; 103:8, 9; Mis. 17:9) Bulus ya shawarci mutanen Afisa: “Ku yi fushi, amma kada ku yi zunubi: kada rana ta faɗi kuna kan fushinku: kada kuwa ku ba Shaiɗan dama.” (Afis. 4:26, 27) Idan mutum ya kasa kame fushinsa, zai ba Iblis zarafin kawo rashin haɗin kai har ma da faɗa a cikin ikilisiya.

15. Ɗaukan abin da ba namu ba zai kawo wane sakamako?

15 Daraja kayan mutane yana kawo haɗin kai a cikin ikilisiya. Mun karanta: “Mai-yin sata kada ya ƙara yin sata.” (Afis. 4:28) Mutanen Jehobah sun amince da juna. Idan Kirista ya ci amanar wannan aminci ta wajen ɗaukan abin da ba nasa ba, zai ɓata wannan haɗin kai mai kawo farin ciki.

Ƙaunar Allah Tana Haɗa Kanmu

16. Ta yaya za mu yi amfani da furci mai ginawa mu ƙarfafa haɗin kanmu?

16 Ikilisiyar Kirista tana da haɗin kai domin ƙaunar da muke yi wa Allah tana motsa mu mu bi da mutane cikin ƙauna. Nuna godiya ga alherin Jehobah yana motsa mu mu yi ƙoƙari sosai mu bi wannan shawara: “[Ku faɗi] irin abin da ke mai-kyau garin ginawa yayinda ake bukata, domin shi ba da alheri ga waɗanda suke ji. Ku kasance da nasiha zuwa ga junanku, masu-tabshin zuciya, kuna yi ma junanku gafara, kamar yadda Allah kuma cikin Kristi ya gafarta maku.” (Afis. 4:29, 32) Jehobah yana gafarta wa mutane ajizai kamar mu. Bai kamata mu ma mu gafarta wa mutane sa’ad da muka ga ajizancinsu ba?

17. Me ya sa ya kamata mu ƙoƙarta sosai mu ɗaukaka haɗin kai?

17 Haɗin kan mutanen Allah yana ɗaukaka Jehobah. Ruhunsa yana motsa mu a hanyoyi dabam dabam don mu sa a kasance da haɗin kai. Ba za mu so mu ƙi ja-gorancin ruhun ba. Bulus ya rubuta: “Kada kuwa ku ɓata zuciyar Ruhu Mai-tsarki na Allah.” (Afis. 4:30) Haɗin kai dukiya ce da ya kamata mu adana. Yana sa dukan waɗanda suke da wannan haɗin kai su yi farin ciki kuma yana ɗaukaka Jehobah. “Ku zama fa masu-koyi da Allah, kamar ’ya’ya ƙaunatattu; ku yi tafiya cikin ƙauna.”—Afis. 5:1, 2.

Yaya Za Ka Amsa?

• Waɗanne halaye ne ke kawo haɗin kai tsakanin Kiristoci?

• Ta yaya lalata za ta hana mu kasancewa da haɗin kai?

• Ta yaya furcinmu zai taimaka mana mu ba da haɗin kai ga wasu?

[Hoton da ke shafi na 17]

Waɗanda suka fito daga wurare dabam dabam suna da haɗin kai

[Hoton da ke shafi na 18]

Ka fahimci haɗarurruka da ke tattare da kwarkwasa?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba