Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • w25 Nuwamba p. 30
  • Talifin da Zai Taimaka wa Matan da Aka Wulaƙanta

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Talifin da Zai Taimaka wa Matan da Aka Wulaƙanta
  • Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Yi Amfani da jw.org Yayin da Kuke Wa’azi—“Ka Zama Abokin Jehobah”
    Hidimarmu Ta Mulki—2015
  • Shawara A Kan Yin Nazari
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2023
  • A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi?
    A Ina Ne Za Mu Sami Amsoshin Muhimman Tambayoyi?
  • Mene ne Matsayin Mata a Tsarin Jehobah?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Dubi Ƙari
Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2025
w25 Nuwamba p. 30
Wata ꞌyarꞌuwa tana ba wa wata mata takardar nan mai jigo, “Women’s Safety​—⁠The Bible’s Perspective.”

Talifin da Zai Taimaka wa Matan da Aka Wulaƙanta

“ A DUNIYA ana wulaƙanta miliyoyin mata manya da ƙanana. Ke ɗaya daga cikinsu ce? Idan haka ne, ki ga abin da ya nuna cewa Allah ya damu da ke kuma yana so ya kāre ki, da kuma abin da zai yi wa waɗanda suke wulaƙanta mata.”

Abin da aka rubuta ke nan a farkon talifin jw.org ɗin nan mai jigo, “Women’s Safety—The Bible’s Perspective.” A ƙarshen talifin, akwai wani link da zai ba ka damar saukar da bayanan da ke talifin kamar takarda. Za a iya bugawa, kuma a nannaɗe shi kashi huɗu. Wata ꞌyarꞌuwa a Amurka mai suna Stacy ta ce: “Na sukar kuma na buga takardar da yawa, kuma ni da wata ꞌyarꞌuwa muka kai su wani wuri a yankinmu inda matan da ake wulaƙanta su, ko waɗanda suke cikin hali mai wuya suke zama.”

Wata mata da take aiki a wurin ta ce a ƙara mata takardun don ta raba wa wasu da suke wurin. Hakan ya sa aka ƙara ba da takardun guda 40, da kuma katin jw.org guda 30. Daga baya, matar da take kula da wurin ta ce tana so Shaidun su nuna wa matan da ke wurin yadda za su yi nazarin Littafi Mai Tsarki da kansu.

ꞌYarꞌuwa Stacy da wasu ꞌyanꞌuwa mata biyu sun kuma je wani wurin da matan suke. A wurin, sun rarraba takardun guda biyar kuma an ce su ƙaro. Wata mata da take aiki a wurin ta ce, “Muna bukatar wannan takardar, za ta taimaka wa matan da suke zama a nan.” Da ꞌyanꞌuwa matan suka sake komawa, wasu matan da suke wurin sun so su ga yadda ake gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki. Kuma biyu sun ce za su so su halarci taro a Majamiꞌar Mulki da za a yi a ƙarshen makon.

ꞌYarꞌuwa Stacy ta ce: “Yadda mutane suke son wannan talifin ya ba mu mamaki sosai. Rarraba wanda aka buga hanya ce mai kyau na gaya wa irin matan nan game da Mulkin Allah. Mun ji daɗin ganin yadda mutane suke farin ciki yayin da suka sami wannan saƙon. Kuma muna marmarin ganin yadda Jehobah zai taimaka mana mu ci-gaba da gaya wa irin matan nan saƙonsa.”

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba