Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb20 Oktoba p. 3
  • Ka Daraja Dangantakarka da Jehobah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Daraja Dangantakarka da Jehobah
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kulla Dangantaka ta Kud da Kud da Jehobah Kuwa?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ka Dogara ga Jehobah a Koyaushe!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Abubuwan Da Ya Kamata Mu Guje Su
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2008
  • Matasa​—Jehobah Ne Babban Abokinku?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
mwb20 Oktoba p. 3
Hotunan wani mutum da yake karfafa dangantakarsa da Jehobah. Na 1. Yana addu’a. Alamar kibiya ta mike sama. Na 2. Yana karanta Littafi Mai Tsarki. Alamar kibiya ta dawo kasa.

RAYUWAR KIRISTA

Ka Daraja Dangantakarka da Jehobah

Shaidun Jehobah suna da wata gata na musamman. Da yake mu Kiristoci ne da muka yi alkawarin bauta wa Jehobah kuma muka yi baftisma, muna da dangantaka mai kyau da Maɗaukaki Jehobah. Ya jawo mu wurinsa ta wurin Ɗansa. (Yoh 6:44) Kuma yana jin addu’o’inmu.​—Za 34:15.

Ta yaya za mu kāre dangantakarmu da Allah? Zai dace mu guji abubuwa marasa kyau da Isra’ilawa suka yi. Jim kaɗan bayan da suka yi wa Jehobah alkawari cewa za su bauta masa shi kaɗai, sun yi ɗan maraƙi kuma suka bauta masa. (Fit 32:​7, 8; 1Ko 10:​7, 11, 14) Don haka, za mu iya tambayar kanmu: ‘Me zan yi idan na fuskanci jarraba? Abubuwan da nake yi suna nuna cewa ina daraja dangantakata da Jehobah?’ Ƙaunar da muke yi wa Ubanmu na sama za ta sa mu guji abubuwan da ya tsana.​—Za 97:10.

KU KALLI BIDIYON NAN KA KĀRE DANGANTAKARKA DA JEHOBAH (KOL 3:5), SA’AN NAN KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Me kwaɗayi ya ƙunsa?

  • Me ya sa za mu guji kwaɗayi da bautar gumaka?

  • Wace alaƙa ke tsakanin zina da bautar gumaka?

  • Me ya sa ya zama dole waɗanda suke da ƙarin ayyuka a ƙungiyar Jehobah su mai da hankali wajen kula da bukatun matansu?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba