Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb20 Oktoba p. 5
  • Matasa​—Jehobah Ne Babban Abokinku?

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Matasa​—Jehobah Ne Babban Abokinku?
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
  • Makamantan Littattafai
  • Za Ka Iya Zama Aminin Jehobah
    Ka Ji Dadin Rayuwa Har Abada!—Don Nazarin Littafi Mai Tsarki
  • Allah Yana Gayyatarka Ka Zama Amininsa
    Za Ka Iya Zama Aminin Allah!
  • Mene ne Baibul Ya Ce Game da Yin Abokantaka?
    Amsoshin Tambayoyi Daga Littafi Mai Tsarki
  • Jehobah Ne Babban Amininmu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2014
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
mwb20 Oktoba p. 5
Wani dan’uwa matashi yana zaune kuma ya dukufa a nazarin Littafi Mai Tsarki.

RAYUWAR KIRISTA

Matasa​—Jehobah Ne Babban Abokinku?

Waɗanne irin halaye ne kake so abokinka ya kasance da su? Mai yiwuwa kana so ya kasance mai aminci da alheri da kuma bayarwa. Jehobah yana nuna dukan waɗannan halayen. (Fit 34:6; A. M 14:17) Idan ka yi masa addu’a, zai ji ka. Lokacin da kake bukatar taimako, zai taimaka maka. (Za 18:​19, 35) Yana gafarta zunubanka. (1Yo 1:9) Hakan ya nuna cewa Jehobah Abokin ƙwarai ne!

Ta yaya za ka zama abokin Jehobah? Ka koya game da shi ta wajen karanta Kalmarsa. Ka dogara gare shi. (Za 62:8; 142:2) Ka daraja abubuwan da yake darajawa, kamar Ɗansa da Mulkinsa da kuma alkawarinsa game da nan gaba. Ka koya wa mutane game da shi. (M.Sh 32:3) Idan ka ƙulla abota da shi, shi ma zai zama Abokinka har abada.​—Za 73:​25, 26, 28.

KU KALLI BIDIYON NAN MATASA​—‘KU ƊANƊANA KU GA JEHOBAH MAI ALHERI NE,’ SAI KU AMSA TAMBAYOYI NA GABA:

  • Hotunan da aka dauko daga bidiyon nan Matasa​—‘Ku Dandana Ku Ga Jehobah Mai Alheri Ne.’ Wata ’yar’uwa tana addu’a kafin ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki.

    Ta yaya za ka shirya yin alkawarin bauta ma Jehobah da kuma baftisma?

  • Hotunan da aka dauko daga bidiyon nan Matasa​—‘Ku Dandana Ku Ga Jehobah Mai Alheri Ne.’ Wani majagaba yana tattauna Littafi Mai Tsarki da wani mutum dan kabilar Karen (S’gaw).

    Ta yaya ’yan’uwa a ikilisiya za su taimaka maka ka bauta ma Jehobah?

  • Hotunan da aka dauko daga bidiyon nan Matasa​—‘Ku Dandana Ku Ga Jehobah Mai Alheri Ne.’ Wani dan’uwa da ya amfana daga tsofaffi, ya fita wa’azi da wani dan’uwa da ya tsufa.

    Ta yaya wa’azi yake ƙarfafa dangantakarka da Jehobah?

  • Hotunan da aka dauko daga bidiyon nan Matasa​—‘Ku Dandana Ku Ga Jehobah Mai Alheri Ne.’ Wata ’yar’uwa da ta yi tafiya ta tsawon awa biyu daga gidanta domin ta yi nazari da wata yarinya kurma.

    Abota da Jehobah za ta dawwama har abada!

    Wace hidima ce za ka iya yi a ƙungiyar Jehobah?

  • Me ka fi so game da Jehobah?

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba