Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • mwb17 Oktoba p. 7
  • Ka Yabi Jehobah Ta Yadda Kake Rayuwa!

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ka Yabi Jehobah Ta Yadda Kake Rayuwa!
  • Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Koyi Darasi Daga Kwatancin Talanti
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Ka Yi Farin Ciki don Ayyukan da Kake Yi a Kungiyar Jehobah
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
  • Mene Ne Yake Sa Ka “Farin Ciki”?
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • Matasa​—Jehobah Ne Babban Abokinku?
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2020
Dubi Ƙari
Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
mwb17 Oktoba p. 7

RAYUWAR KIRISTA

Ka Yabi Jehobah Ta Yadda Kake Rayuwa!

Rai kyauta ne mai tamani daga Allah. Yadda muke bi da rayuwarmu a kullum yana nuna ko mun daraja wannan kyauta ko a’a. A matsayinmu na Shaidun Jehobah, muna yin amfani da baiwarmu don mu girmama Jehobah, wanda ya ba mu rai. (Za 36:9; R. Yoh 4:11) Amma saboda matsaloli na yau da kullum, yana mana wuya mu sa ayyukan ibada farko a rayuwa. (Mk 4:​18, 19) Shi ya sa yake da kyau mu tambayi kanmu: ‘Ina bauta wa Jehobah da dukan ƙarfina kuwa? (Ho 14:⁠2) Aikin da nake yi yana shafan ibadata ga Jehobah? Wane maƙasudi ne na kafa a ibadata? Ta yaya zan faɗaɗa hidimata?’ Idan ka lura cewa kana bukatar ka inganta hidimarka, sai ka yi addu’a ga Jehobah kuma ka yi canji idan da bukata. Babu shakka, bauta wa Jehobah a kullum yana sa mu yi farin ciki a rayuwa!​—⁠Za 61:⁠8.

Edgardo Franco yana waka a wani filin kallo; Edgardo Franco yana wa’azi

Wa kake ba wa baiwarka?

KU KALLI BIDIYON NAN KA YI AMFANI DA BAIWARKA A HIDIMAR JEHOBAH, SAI KU AMSA TAMBAYOYIN NAN:

  • Me ya sa bai dace mu yi amfani da baiwarmu wajen yi wa duniyar nan hidima ba? (1Yo 2:⁠17)

  • Waɗanne albarka ne waɗanda suke bauta wa Jehobah da dukan ƙarfinsu suke samu?

  • A wace hanya ce za ka iya yin amfani da baiwarka wajen tallafa wa ƙungiyar Jehobah?

SHAWARA A KAN IBADA TA IYALI:

  • Ka gana da wani mai shela da ya daɗe yana bauta wa Jehobah, wataƙila wanda yake hidima ta cikakken lokaci. Wane irin sadaukarwa ne ya yi don ya iya bauta wa Jehobah da dukan ƙarfinsa? Ta yaya Jehobah ya albarkace shi?

  • Ka shiga Tashar JW, sai ka duba ƙarƙashin GANAWA DA LABARAI > ALBARKAR HIDIMA MAI TSARKI. Za ka ji da kuma ga mutane da dama da suka bayyana irin farin cikin da suke yi don sun yi amfani da rayuwarsu wajen taimaka wa ƙungiyar Jehobah

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba