30 ga Oktoba–5 ga Nuwamba
JOEL 1-3
Waƙa ta 143 da Addu’a
Gabatarwar Taro (minti 3 ko ƙasa da hakan)
DARUSSA DAGA KALMAR ALLAH
“ʼYa’yanku Maza da Mata Za Su Yi Annabci”: (minti 10)
[Ka saka bidiyon Gabatarwar Littafin Joel.]
Joe 2:28, 29—Shafaffun Kiristoci suna aiki a matsayin kakakin Jehobah (w02 8/1 27 sakin layi na 4-5; jd-E 167 sakin layi na 4)
Joe 2:30-32—Mutanen da suke kiran sunan Jehobah ne kaɗai za su tsira a lokacin yaƙin Armageddon (w07 11/1 29 sakin layi na 2)
Neman Abubuwa Masu Tamani: (minti 8)
Joe 2:12, 13—Mene ne waɗannan ayoyin suka koya mana game da tuba ta gaskiya? (w07 11/1 29 sakin layi na 5)
Joe 3:14—Mene ne “kwarin yankan shari’a”? (w07 11/1 29 sakin layi na 3)
Mene ne karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon ya koya maka game da Jehobah?
Waɗanne darussa ne kuma ka koya a karatun Littafi Mai Tsarki na wannan makon?
Karatun Littafi Mai Tsarki: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Joe 2:28–3:8
KA YI WA’AZI DA ƘWAZO
Haɗuwa ta Fari: (minti 2 ko ƙasa da hakan) Katin JW.ORG
Koma Ziyara: (minti 4 ko ƙasa da hakan) Katin JW.ORG—Ka riga ka ba da katin a haɗuwa ta fari. Ka ci gaba da tattaunawar kuma ka kammala da nuna wa ɗalibin inda zai kalli bidiyo a jw.org.
Nazarin Littafi Mai Tsarki: (minti 6 ko ƙasa da hakan) lv 196-197 sakin layi na 3-5
RAYUWAR KIRISTA
Jehobah Yana Taimaka Mana Mu Jimre Jarrabawa: (minti 9) Ka nuna bidiyon nan Jehobah Shi Ne Ƙarfina. Sai ka tambayi masu sauraro: Wace irin jarrabawa ce iyalin Henschel suka fuskanta? Ta yaya bangaskiya da kuma amincin iyaye za su taimaka wa yaransu? Ta yaya Jehobah zai taimaka maka kamar yadda ya yi wa Ɗan’uwa Henschel?
Ku Zama Abokin Jehobah—Sunan Jehobah: (minti 6) Ka nuna bidiyon nan Ku Zama Abokin Jehobah—Sunan Jehobah. Ka gayyaci yara zuwa kan bagadi kuma ka yi musu waɗannan tambayoyin: Mene ne sunan Jehobah yake nufi? Mene ne Jehobah ya halitta? Ta yaya Jehobah zai iya taimaka maka?
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya: (minti 30) kr babi na 20 sakin layi na 17-19; akwatunan nan “Aikin Agaji Ya Yi Tasiri a Rayuwarsa” da “’Yan’uwa a Faɗin Duniya Sun Taimaka da Aikin Agaji”; da kuma akwatin bita “Ka Gaskata da Mulkin Kuwa?”
Bita da Abin da Za A Tattauna Mako Mai Zuwa (minti 3)
Waƙa ta 72 da Addu’a