Mene Ne Yake Sa Ka “Farin Ciki”?
1. Wane dalili ne muke da shi na yin farin ciki a ƙarshen kowane wata?
1 Sa’ad da aka ce ’yan’uwa su ba da rahoton wa’azi a ƙarshen wata, mene ne “ke sa ka farin ciki”? (Gal. 6:4, NW) Ko da mu majagaba ne na musamman, waɗanda suke ba da rahoton awoyi 130 a kowane wata, ko kuma masu shela da aka amince su riƙa ba da rahoton mintoci 15, ya kamata dukanmu mu riƙa farin ciki saboda muna bauta wa Jehobah da zuciya ɗaya.—Zab. 100:2.
2. Me ya sa ya kamata mu yi iya ƙoƙarinmu a hidimarmu ga Jehobah?
2 Jehobah ya cancanci mu bauta masa da zuciya ɗaya tun da yake shi ne Ubangiji Allah Maɗaukakin Sarki. (Mal. 1:6) Ƙaunar da muke masa ne ya sa muka keɓe kanmu don mu yi nufinsa. Idan a ƙarshen kowace rana ko wata, mun tabbata cewa mun ba da “nunan fari” na lokacinmu da iyawarmu da kuzarinmu a hidimarmu ga Jehobah, hakan zai sa mu kasance da farin ciki. (Mis. 3:9) Amma idan zuciyarmu ta gaya mana cewa za mu iya yin abin da ya fi haka, to, zai dace mu yi iya ƙoƙarinmu don mu yi gyara.—Rom. 2:15.
3. Me ya sa bai dace mu gwada kanmu da wasu ba?
3 ‘Kada Ku Gwada Kanku da Wani’: Bai dace mu riƙa gwada abubuwan da muke cim ma da na wasu ba ko kuma mu gwada abubuwan da muka cim ma a lokacin da muke da kuzari da na yanzu. Yanayinmu yakan canja. Iyawarmu ba ɗaya ba ne. Idan muna gwada kanmu da wasu hakan zai iya sa mu yin gasa ko kuma mu ji kamar ba mu cancanta ba. (Gal. 5:26; 6:4) Yesu bai gwada mutane da wasu ba. Maimakon haka, ya yaba wa kowane mutum bisa ga abin da ya iya yi.—Mar. 14:6-9.
4. Waɗanne muhimman darussa ne za mu iya koya daga almarar Yesu na talent?
4 A almarar Yesu na talent, kowane ma’aikaci ya karɓi talent ‘gwargwadon iyawarsa.’ (Mat. 25:15) Sa’ad da mai gidan ya dawo, ya tambaye su yadda suka gudanar da ayyukansu, sai ya yaba wa waɗanda suka yi aiki daidai iyawarsu da yanayinsu, kuma ya ce su zo su yi farin ciki tare da shi. (Mat. 25:21, 23) Hakazalika, idan muna wa’azin Mulki da himma, za mu iya kasancewa da tabbaci cewa muna da amincewar Allah kuma hakan zai sa mu farin ciki!