Wasu ’yan’uwa suna ba da ƙasidar nan Albishiri Daga Allah! a ƙasar Azerbaijan
Gabatarwa
AWAKE!
Tambaya: Ta yaya za mu yi amfani da lokacinmu a yadda ya dace?
Nassi: M. Wa 4:6
Littafi: Wannan mujallar Awake! ta ba da wasu shawarwari a kan yadda za mu yi amfani da lokacinmu a yadda ya dace.
KU KOYAR DA GASKIYA
Tambaya: Me ya sa aka halicce mu?
Nassi: Za 37:29
Gaskiya: Allah ya halicci mutane don su yi rayuwa har abada a duniya.
ALBISHIRI DAGA ALLAH!
Tambaya: A ina ne kake ganin za mu iya samun albishiri? [Ka nuna bidiyon nan Za Ka So Ka Ji Albishiri?]
Nassi: Ish 52:7
Littafi: Wannan ƙasidar tana ɗauke da “bishara ta alheri” daga Littafi Mai Tsarki.
KA RUBUTA TAKA GABATARWA
Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.