Ana ba da ƙasidar nan Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya a ƙasar Georgia
Gabatarwa
HASUMIYAR TSARO
Tambaya: Wane ne ya fi ba da kyauta a sama da duniya?
Nassi: Yaƙ 1:17
Littafi: Wannan mujallar ta yi magana a kan yadda za mu nuna godiya don kyauta mafi daraja da Allah ya ba mu.
KU KOYAR DA GASKIYA
Tambaya: Mene ne sunan Allah?
Nassi: Za 83:18
Gaskiya: Sunan Allah shi ne Jehobah.
YADDA IYALINKU ZA TA ZAUNA LAFIYA
Gabatarwa: Muna nuna wa mutane wannan bidiyon game da iyali. [Ka nuna bidiyon Yadda Iyalinku Za Ta Zauna Lafiya.]
Littafi: Idan kana son ka karanta ƙasidar da aka ambata a bidiyon nan, zan iya ba ka shi ko kuma in nuna maka yadda za ka sauƙar da shi a dandalinmu.
KA RUBUTA TAKA GABATARWA
Ku yi amfani da fasalin da ke baya don rubuta taku gabatarwar wa’azi.