Tsarin Ayyuka na Makon 9 ga Nuwamba
MAKON 9 GA NUWAMBA
Waƙa ta 48 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
ia babi na 2 sakin layi na 1-12 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Labarbaru 21-25 (minti 8)
Na 1: 1 Labarbaru 23:1-11 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Ta Yaya Yin Bimbini a Kan Abin da Ke Romawa 8:32 Zai Tabbatar Mana Cewa Dukan Alkawuran Allah Za Su Cika? (minti 5)
Na 3: Mene Ne Tashin Matattu Zai Ƙunsa?—wp13 11/1 16 sakin layi na 3-4 (minti 5)
Taron Hidima:
JIGON WATA: “Ni na dasa, Afollos ya yi ban ruwa; amma Allah ne ya ba da amfani.”—1 Kor. 3:6.
Waƙa ta 98
Minti 10: “Ni Na Dasa, Afollos Ya Yi Ban Ruwa; Amma Allah Ne Ya Ba da Amfani.” Jawabin da zai bayyana jigon wata. (1 Kor. 3:6) Idan da lokaci, ka taƙaita abin da ke Hasumiyar Tsaro ta 1 ga Afrilu, 2004, shafi na 10 sakin layi na 14 zuwa 21. Ka ɗan faɗi wasu abubuwan da za a tattauna a Taron Hidima na wannan watan kuma ka nuna yadda suke da nasaba da jigon.
Minti 20: “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yadda Za Mu Ba da Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?” Tattaunawa. Ka sa a yi gwaji guda biyu. Na farko, a yi amfani da bayanin da ke wannan talifin wajen yin gwajin, na biyu kuma a yi amfani da wani gabatarwa dabam da ke sa mutane su saurari saƙonmu.
Waƙa ta 111 da Addu’a