Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Yadda Za Mu Ba da Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?
Muhimmancinsa: Littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? shi ne ainihin littafin da muke amfani da shi wajen koyar da mutane. Amma kafin mu yi amfani da shi wajen yin nazari da wani, zai dace mu ba shi nasa kofi. Saboda haka, ya kamata dukanmu mu ƙware wajen ba da littafin a wa’azi. (Mis. 22:29) Akwai hanyoyi da yawa na yin hakan, kuma masu shela ne za su zaɓi gabatarwar da suka fi so.
Ku Bi Shawarar Nan a Wannan Watan:
Ku gwada yadda za ku yi hakan a ibadarku ta iyali.
Sa’ad da kake wa’azi, ka gaya wa wasu masu shela abin da kake da niyyar cewa kafin ka ba da littafin. (Mis. 27:17) Idan gabatarwa da ka yi amfani da ita ba ta jan hankalin mutane, ka gwada wata.