Tsarin Ayyuka na Makon 2 ga Nuwamba
MAKON 2 GA NUWAMBA
Waƙa ta 52 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
ia babi na 1 sakin layi na 14-27, da tambayoyi don bimbini da ke shafi na 16 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Labarbaru 16-20 (minti 8)
Na 1: 1 Labarbaru 17:15-27 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Matattu Za Su Sake Rayuwa Kuwa?—wp13 11/1 16 sakin layi na 1-2 (minti 5)
Na 3: Hanyoyin da Za Mu Riƙa ‘Rinjayar Mugunta da Nagarta’—Rom. 12:21 (minti 5)
Taron Hidima:
JIGON WATA: Ku zama “dasassu” da kuma ‘kafaffu cikin bangaskiya.’—Kol. 2:6, 7.
Waƙa ta 91
Minti 10: Ku Ba da Mujallu a Watan Nuwamba. Tattaunawa. Da farko, ka sa a yi gwaji a kan yadda za a iya ba da mujallun ta wajen yin amfani da gabatarwa da aka bayar. Bayan haka, ka sa a yi kalami a kan kowace gabatarwa.
Minti 10: Bukatun ikilisiya.
Minti 10: Mene ne Muka Cim ma? Tattaunawa. Ka ba masu shela dama su faɗi yadda suka amfana ta wajen yin amfani da bayanin da ke talifin nan “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Ka Koya wa Ɗalibanka Yin Nazari.” Ka ba ‘yan’uwa dama su faɗi labarai masu daɗi da suke da shi.
Waƙa ta 140 da Addu’a
Tunasarwa: Don Allah a kunna wa ‘yan’uwa sautin sabuwar waƙar don su saurara, sa’an nan su rera waƙar tare.