Kalmar Allah Tana Samun Iko a Rayuwarka Kuwa?
Karanta Littafi Mai Tsarki kullum zai taimaka mana mu zama “dasassu” da kuma ‘kafaffu cikin bangaskiya.’ (Kol. 2:6, 7) Amma idan muna son Kalmar Allah ta samu iko a rayuwarmu, wajibi ne mu yi tunani a kan abubuwan da muka koya kuma mu yi amfani da su. (Ibran. 4:12; Yaƙ. 1:22-25) Littafin Joshua 1:8 ta ambata hanyoyi uku da za mu bi don mu ji daɗin karatun Littafi Mai Tsarki: (1) Mu riƙa karanta Kalmar Allah “dare da rana.” (2) Mu riƙa “tunani a kansa.” Hakan ya nuna cewa mu riƙa karanta Littafi Mai Tsarki a hanyar da za ta ba mu damar yin bimbini da kuma fahimtar yanayin mutanen da muke karanta labaransu. (3) Mu yi ƙoƙari mu “aika bisa ga dukan abin da aka rubuta a ciki.” Bin waɗannan shawarwarin za su sa mu yi “nasara” kuma mu yi “albarka.”