Tsarin Ayyuka na Makon 29 ga Yuni
MAKON 29 GA YUNI
Waƙa ta 9 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 26 sakin layi na 18-23, da akwati da ke shafi na 269 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Sarakuna 3-6 (minti 8)
Bitar Makarantar Hidima ta Allah (minti 20)
Taron Hidima:
Jigon Wata: “Ka tuna da kwanakin dā.”—K. Sha. 32:7.
Waƙa ta 118
Minti 15: Littattafan da Za a Ba da a Watan Yuli. Tattaunawa. Ka tattauna wasu abubuwa da ke cikin littattafan da za a bayar, bayan haka, sai ka sa a yi gwajin da ke nuna wani mai shela yana koya wa wani da bai ƙware ba yadda zai ba da littattafan.
Minti 15: “Wasiƙa Daga Hukumar da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah.” Ka tattauna wasiƙa daga Hukuma da Ke Kula da Ayyukan Shaidun Jehobah da aka wallafa tare da Hidimarmu ta Mulki ta watan Afrilu, 2015. Ka ba ’yan’uwa dama su faɗi abubuwan da suka fi so a rahoton wa’azi na dukan duniya na shekara ta 2014. Ka kammala ta wajen ƙarfafa waɗanda suka iya karanta Turanci su ƙarasa karatun 2015 Yearbook.
Waƙa ta 108 da Addu’a