Bitar Makarantar Hidima ta Allah
Za a tattauna tambayoyin da ke gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 29 ga Yuni, 2015. An saka kwanan watan da za a tattauna waɗannan bayanan domin ku yi bincike sa’ad da kuke shirya makaranta a kowane mako.
Me ya sa yadda Michal ta yi wa Dauda magana bai dace ba, kuma wane darasi ne ma’aurata za su koya daga hakan? (2 Sam. 6:20-23) [11 ga Mayu, w11 10/1 shafi na 28 sakin layi na 1]
Mene ne Nathan ya yi sa’ad da Jehobah ya yi masa gyara don ya gaya wa Dauda ya cika burinsa na gina haikali ga Jehobah? (2 Sam. 7:2, 3) [11 ga Mayu, w12 2/15 shafi na 24 sakin layi na 6-7]
Me ya sa Nathan ya ba da kwatancin da ke 2 Sama’ila 12:1-7 maimakon ya gaya wa Dauda kai tsaye cewa ya yi zunubi mai tsanani? Ta yaya wannan labarin zai taimaka mana mu ƙware a koyarwarmu? [18 ga Mayu, w12 2/15 shafi na 24 sakin layi na 2-3]
Me ya sa ya yi wa Absalom sauƙi ya yaudari Isra’ilawa, kuma ta yaya za mu kāre kanmu daga mutanen da ke kamar “Absalom” a zamaninmu? (2 Sam. 15:6) [25 ga Mayu, w12 7/15 shafi na 13 sakin layi na 7]
Ta yaya Jehobah ya yi wa Dauda tanadi a lokacin da yake bukatar taimako kuma wane darasi ne za mu koya daga hakan? (2 Sam. 17:27-29) [1 ga Yuni, w08 9/15 shafi na 6 sakin layi na 15-16]
Ta yaya za mu amfana daga yadda Dauda ya bi da wani baƙo mai suna Ittai? (2 Sam. 18:2) [1 ga Yuni, w09 5/15 shafi na 27 sakin layi na 7]
Ta yaya Barzillai ya nuna cewa shi mai ibada ne duk da cewa yanayinsa ya canja? (2 Sam. 19:31-40) [15 ga Yuni, w07 6/1 shafi na 24 sakin layi na 13]
Ta yaya tawali’un Jehobah zai sa mutum ya zama “babba”? (2 Sam. 22:36) [15 ga Yuni, w12 11/15 shafi na 17 sakin layi na 7]
Ta yaya Nathan ya nuna aminci ga Allah kuma yaya za mu iya yin koyi da irin wannan halin? (1 Sar. 1:11-14) [22 ga Yuni, w12 2/15 shafi na 25 sakin layi na 1, 4-5]
A waɗanne hanyoyin rayuwa ne bawan Allah zai iya neman hujja don ya karya dokar Allah kamar yadda Sulemanu ya yi? (1 Sar. 3:1) [29 ga Yuni, w11 12/15 shafi na 10 sakin layi na 12-14]