Tsarin Ayyuka na Makon 22 ga Yuni
MAKON 22 GA YUNI
Waƙa ta 67 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 26 sakin layi na 10-17 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Sarakuna 1-2 (minti 8)
Na 1: 1 Sarakuna 1:15-27 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Abin da Ya Sa Kiristoci na Gaskiya Suke da Wadar Zuci da Kuma Farin Ciki—igw 23 sakin layi na 1-3 (minti 5)
Na 3: Da Yake Rai Kyauta Ne, Me Ya Sa Muke Bukatar Mu Nemi Ceto?—Rom. 6:23; Filib. 2:12 (minti 5)
Taron Hidima:
Jigon Wata: “Ka tuna da kwanakin dā.”—K. Sha. 32:7.
Waƙa ta 75
Minti 15: Mene ne Muka Cim ma? Tattaunawa da sakataren ikilisiya zai yi. Ka ambata abin da ikilisiyar ta cim ma a lokacin Tuna da Mutuwar Yesu, bayan haka, ka yaba musu don ƙoƙarinsu. Ka ba masu sauraro dama su faɗi labaran da suka samu sa’ad da suke rarraba takardun gayyatar mutane zuwa taron Tuna da Mutuwar Yesu.
Minti 15: Ta Yaya Ya Riƙe Hannunka? (Isha. 41:13) Ka gana da mai shela ɗaya ko biyu da suka daɗe suna bauta wa Jehobah kuma ka ba su dama su faɗi abin da ya taimaka musu su shawo kan ƙalubalen da suke fuskanta a hidimarsu.
Waƙa ta 107 da Addu’a