Ku Yi Koyi da Masu Shela da Suka Fi Ku Ƙwarewa
Muna ɗaukan masu shela da suka ƙware da muhimmanci sosai. Wasu sun daɗe suna bauta wa Jehobah da aminci. Wasu kuma a kwana-kwanan nan ne suka ƙware a yin wa’azi. Waɗannan masu shelan sun shaida yadda Yesu yake ja-gorar ikilisiyar Kirista a waɗannan kwanaki na ƙarshe ta wajen faɗaɗa aikin wa’azi da kuma almajirtar da mutane. (Mat. 28:19, 20) Ta wurin saka hannu a yin wa’azi, sun sami “mafificin girman iko” da ke taimaka musu sa’ad da suke fuskantar ƙalubale da kuma gwaji. (2 Kor. 4:7) Akwai abubuwa da yawa da za mu iya koya daga waɗannan masu shela da suka ƙware. Suna jin daɗin koya ma wasu abubuwan da suka koya idan suka sami damar yin hakan. (Zab. 71:18) Saboda haka, zai dace mu nemi hanyoyin da za mu yi koyi da su. Ta yaya za mu yi hakan?
Sa’ad da Muke Wa’azi. Sababbi ko waɗanda ba su ƙware ba suna bukatar horarwa don su ƙware a yin wa’azi. Za mu iya koyan abubuwa da dama ta wajen lura da yadda waɗanda suka ƙware suke wa’azi. (Ka duba Hasumiyar Tsaro ta 15 Fabrairu, 2015, “Kada Ka Yi Sanyin Gwiwa a Hidimarka,” sakin layi na 3 da ke ƙarƙashin kan maganan nan “Ka Taimaka wa Waɗanda Ba Su Ƙware Sosai Ba.”) Ta yaya ka amfana daga yin wa’azi tare da irin waɗannan masu shela?
Shin za ka iya gaya wa wani mai shela da ya ƙware cewa kana son ku je wa’azi tare? Idan mai shelar naƙasasse ne, za ka iya yin nazari da ɗaya daga cikin ɗalibanka a gidansa. Bayan kun gama nazarin, ka tambaye shi abubuwan da ya lura sa’ad da kuke nazarin da kuma shawarar da zai iya ba ka.
Ku Riƙa Cuɗanya da Su: Za ka iya sanin masu shela da suka ƙware ta wurin yin cuɗanya da su. Za ka iya gayyatar ɗaya daga cikinsu sa’ad da kuke ibada ta iyali kuma ku yi masa wasu tambayoyi. Idan mai shelar naƙasasse ne, shin za ku iya zuwa gidansa don ku yi ibada ta iyalin tare a wasu lokatai? Ku tambaye shi yadda ya soma bauta wa Jehobah. Wace albarka ce ya samu? Wane ci gaba ne ya shaida a yankin? Waɗanne abubuwa ne suke sa shi farin ciki a hidimarsa ga Jehobah?
Ya kamata mu fahimci cewa waɗannan ƙwararrun ma suna da kasawarsu kuma mu daidaita ra’ayinmu game da su. Kamar kowa, waɗannan masu shela da suka ƙware suna da baiwa dabam-dabam a hidima. (Rom. 12:6-8) Wasu sun tsufa kuma ba za su iya yin cuɗanya da mu kamar yadda suke yi a dā ba. Duk da haka, za mu iya koyan abubuwa da yawa daga wurinsu don sun ƙware wajen bauta wa Jehobah da aminci.