Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Koyar da Sababbi
Muhimmancinsa: Wajibi ne sababbin almajiran Yesu su koyi kiyaye “dukan iyakar abin” da ya umurce mu, kuma hakan ya haɗa da koya wa mutane gaskiya. (Mat. 28:19, 20) Sababbi da yawa sun ƙware su soma yin jawabi a Makarantar Hidima ta Allah kuma wataƙila sun soma yi wa danginsu da abokansu wa’azi. Amma, yayin da suke ƙara daraja abin da suke koya kuma suka san cewa Jehobah yana so kowa ya ji bishara, hakan zai iya motsa su su so yin wa’azi. (Rom. 10:13, 14) Bayan an amince sababbi su zama masu shela da ba su yi baftisma ba, zai dace a koyar da su sosai domin hakan zai taimaka musu su kasance da gaba gaɗi.—Luk. 6:40.
Ku Bi Shawarar Nan a Wannan Watan:
Ka kai ɗalibinka wa’azi gida-gida da kuma koma ziyara. Idan ba ka da ɗalibi, ka gayyaci wani mai shela da bai ƙware sosai ba don ku yi wa’azi tare.