Gayyata ga Kowa
1. Yaushe ne za a soma rarraba takardun gayyata zuwa taron yanki?
1 Idan kana shirya wata liyafa ta musamman kuma kana son danginka ko abokanka su hallara, babu shakka, za ka yi farin ciki sosai sa’ad da kake gayyatar su. Hakazalika, ’yan’uwan da suka shirya taron yankin da za a yi nan ba da daɗewa ba sun yi aiki tuƙuru. Makonni uku kafin taron, Jehobah zai ba mu gatan gayyatar mutane zuwa taron. Mene ne zai taimaka mana mu rarraba takardun gayyatar da ƙwazo da kuma farin ciki?
2. Mene ne zai motsa mu mu yi wannan kamfen da ƙwazo?
2 Idan mun yi bimbini sosai a kan yadda muke amfana daga yadda Jehobah yake koyar da mu a taron yanki, hakan zai motsa mu mu rarraba takardun gayyatar da ƙwazo. (Isha. 65:13, 14) Ya kamata mu kuma tuna cewa ana samun sakamako mai kyau daga wannan kamfen. (Ka duba akwatin nan “Ana Samun Sakamako Mai Kyau.”) Wasu mutanen da muka gayyata za su halarci taron amma wasu ba za su halarta ba. Ko da mutane nawa ne suka halarci taron, ƙwazon da muka yi a lokacin wannan kamfen zai ɗaukaka Jehobah kuma ya nuna cewa shi mai karimci ne.—Zab. 145:3, 7; R. Yoh. 22:17.
3. Wane tsari ne za mu bi don rarraba takardun gayyatar?
3 Ya kamata kowane rukunin dattawa ya yanke shawara a kan yadda za a rarraba takardun gayyatar a yankin gabaki ɗaya, da kuma ko zai dace a ajiye wa mutanen da ba sa gida ko kuma a rarraba su sa’ad da ake wa’azi ga jama’a. A rarraba mujallu tare da takardun gayyatar a ƙarshen mako idan hakan zai yiwu. Bayan kamfen ɗin, za mu yi matuƙar farin ciki sa’ad da muka tuna cewa mun rarraba takardun da ƙwazo kuma mutane sun halarci wannan taron da Jehobah ya shirya mana!