Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Wa’azi—Samun Wani da Za Ku Riƙa Kai wa Mujallu a Kai a Kai
Muhimmancinsa: Mutane da yawa da suke jin daɗin karanta mujallunmu ba sa so mu yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Wataƙila don sun fi son addininsu ko kuma suna ji ba su da lokacin yin nazari. Amma, yayin da suke karanta mujallunmu a kai a kai, suna iya yin marmarin Kalmar Allah. (1 Bit. 2:2) Wani talifi zai iya ratsa zuciyarsu ko kuma yanayinsu zai iya canjawa. Idan muna ziyartarsu a kai a kai, hakan zai iya sa su saki jiki da mu kuma zai taimaka mana mu san abin da suka fi so. A sakamakon haka, za mu iya soma nazarin Littafi Mai Tsarki da su.
Ku Bi Shawarar Nan a Wannan Watan:
Ka rubuta jerin sunayen mutanen da za ka riƙa kai musu mujallu kowane wata. Ka ba su sababbin mujallu kuma ka gaya musu cewa za ka kawo musu na wata mai zuwa.