Tsarin Ayyuka na Makon 26 ga Janairu
MAKON 26 GA JANAIRU
Waƙa ta 99 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 19 sakin layi na 9-17 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Alƙalawa 5-7 (minti 8)
Na 1: Alƙalawa 7:12-25 (minti 3 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Yadda Yesu Ya Nuna Cewa Ya Cancanci Ya Yi Sarauta (minti 5)
Na 3: Hanyoyin da Za Mu Iya Koya Game da Jehobah—igw 5 sakin layi na 1-4 (minti 5)
Taron Hidima:
Jigon Wata:Ku Yi Hidimar “Ubangiji da Iyakacin Tawali’u.”—Ayyukan Manzanni 20:19.
Waƙa ta 88
Minti 10: Littattafan da Za Mu Ba Mutane a Janairu da Fabrairu. Tattaunawa. Ka ba masu sauraro dama su faɗi sakamako masu kyau da suka samu a lokacin da suke ba mutane ƙasidar Albishiri Daga Allah! Ka sa a yi gajeren gwaji da zai nuna yadda za a ba da wannan ƙasidar. Bayan haka, ku tattauna talifin nan “Me Ya Sa Ya Kamata Mu Kama Hanya Nan da Nan?”
Minti 10: Dattawa da Suke Yi wa Ubangiji Hidima—Mai Gudanar da Nazarin Hasumiyar Tsaro. Ka gana da mai gudanar da Nazarin Hasumiyar Tsaro. Ka yi masa tambayoyin da ke gaba: Mene ne aikinka a matsayin mai gudanar da nazarin Hasumiyar Tsaro ya ƙunsa? Yaya kake yin shiri don nazarin Hasumiyar Tsaro? Me ya sa ba ka iya kiran dukan waɗanda suka ɗaga hannu don su yi kalami? Mene ne mai karatu da waɗanda suke ba da kalami da kuma ’yan’uwan da suke yawo da makarufo za su iya yi don kowa ya amfana kuma ya ji daɗin Nazarin Hasumiyar Tsaro? Ta yaya Makarantar Hidima ta Mulki da ka halarta kwanan nan ta taimaka maka ka kula da wannan aiki mai muhimmanci?
Minti 10: “Ku Yi Amfani da jw.org Yayin da Kuke Wa’azi—‘Ka Zama Abokin Jehobah.’” Tattaunawa. Ka ambata wasu abubuwa da wannan sashen dandalinmu take ɗauke da su sa’an nan ka kunna wa masu sauraro wani bidiyo a sashen don su kalla. Ka ba masu sauraro dama su faɗi hanyoyin da za mu iya yin amfani da sashen “Ka Zama Abokin Jehobah” sa’ad da muke wa’azi gida-gida ko a wuraren da akwai jama’a ko kuma a duk inda muka sami zarafin yin hakan.
Waƙa ta 135 da Addu’a