Ku Ci Gaba da Ƙwarewa a Matsayinku na Masu Shelar Bishara
1. Waɗanne misalai a ƙarni na farko ne suka nuna cewa ya kamata mu ci gaba da ƙwarewa a matsayinmu na masu shela?
1 Ya kamata Kiristoci su ci gaba da ƙwarewa a matsayinsu na masu shelar bishara. Wannan ne dalilin da ya sa Yesu ya riƙa horar da mabiyansa don su inganta yadda suke wa’azi. (Luk. 9:1-5; 10:1-11) Saboda wannan dalilin ne ma Akila da Biriskilla suka zaunar da Afollos suka “ƙara bayyana masa tafarkin Allah sosai da sosai.” (A. M. 18:24-26, Littafi Mai Tsarki) Ƙari ga haka, Bulus ya ƙarfafa Timoti ya riƙa mai da hankali ga koyarwarsa don ci gabansa ‘ya bayyana ga kowa.’ (1 Tim. 4:13-15) Kome yawan shekarunmu a matsayin masu shelar bishara, muna bukatar mu ci gaba da kyautata yadda muke wa’azi.
2. Ta yaya za mu iya bin misalin wasu?
2 Ku Bi Misalin Wasu: Hanya ɗaya da za mu iya kyautata yadda muke koyarwa ita ce ta wajen bin misalin wasu. (Mis. 27:17) Saboda haka, ku kasa kunne sosai sa’ad da wanda kuke wa’azi tare yake magana. Ku nemi shawara daga ƙwararrun masu shela. (Mis. 1:5) Shin yana muku wuya ku koma ziyara ko ku soma nazari da mutane ko dai makamancin hakan? Ku sami mai kula da rukuninku na wa’azi ko wani ƙwararren mai shela don ya taimaka muku. Ƙari ga haka, ku riƙa yin addu’a a kai a kai don Jehobah ya ba ku ruhunsa mai tsarki, wanda zai sa ku ci gaba da ƙwarewa.—Luk. 11:13.
3. Me ya kamata mu yi idan aka ba mu shawara, ko da ba mu nemi shawarar ba?
3 Kada ku yi fushi idan aka ba ku shawara da za ta taimaka muku ku ƙware, ko da ba ku nemi shawarar ba. (M. Wa. 7:9) Ku karɓi shawarar cikin sauƙin kai kuma ku yi godiya kamar Afollos. Hakan zai nuna cewa ku masu hikima ne.—Mis. 12:15.
4. Saboda wane dalili mai kyau da ya Yesu ya bayar ne ya kamata mu ci gaba da ƙwarewa a matsayin masu shela?
4 Samun Ci Gaba Yana Kawo Ɗaukaka ga Allah: Yesu ya ba da wani kwatanci don ya ƙarfafa mabiyansa su ci gaba da ƙwarewa a matsayinsu na masu shela. Ya kwatanta kansa a matsayin itacen inabi, almajiransa kuma rassan itacen. Sai ya ce Ubansa yana tsabtace kowane reshen da yake ba da ’ya’ya domin reshen ‘ya daɗa ba da ’ya’ya.’ (Yoh. 15:2) Kamar yadda mai gonar inabi zai so rassan itatuwansa su riƙa ba da ’ya’ya sosai, haka ma Jehobah yake so mu ci gaba da ƙwarewa a yadda muke ba da ‘’ya’yan leɓunanmu.’ (Ibran. 13:15) Wane sakamako mai kyau ne za a samu idan muka ci gaba da ƙwarewa a matsayin masu shela? Yesu ya ba da amsar cewa: “Inda ake ɗaukaka Ubana ke nan, ku ba da ’ya’ya da yawa.”—Yoh. 15:8.