Me Ya Sa Ya Kamata Mu Kama Hanya Nan da Nan?
Sa’ad da muka haɗu da ’yan’uwanmu a taron fita wa’azi, muna jin daɗin tattaunawa da su sosai. Amma, da zarar an gama taron, zai dace mu kama hanya nan da nan zuwa yankin da za mu yi wa’azi. Wa’azin da muke yi aiki ne na gaggawa sosai. (2 Tim. 4:2) Idan muka tsaya muna jinkiri, za mu ɓata lokacin da ya kamata mu yi wa’azi da shi. Za mu sami zarafin tattaunawa da ’yan’uwanmu yayin da muke wa’azi tare da su. Idan muka tafi inda za mu yi wa’azi nan da nan bayan taron fita wa’azi, za mu nuna cewa muna yi wa Jehobah da kuma Ɗansa hidima da ƙwazo.—Rom. 12:11.