Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 10/14 p. 4
  • Tsarin Ayyuka na Makon 3 ga Nuwamba

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tsarin Ayyuka na Makon 3 ga Nuwamba
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Ƙananan Jigo
  • MAKON 3 GA NUWAMBA
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 10/14 p. 4

Tsarin Ayyuka na Makon 3 ga Nuwamba

MAKON 3 GA NUWAMBA

Waƙa ta 79 da Addu’a

Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:

cl babi na 15 sakin layi na 11-19 (minti 30)

Makarantar Hidima ta Allah:

Karatun Littafi Mai Tsarki: Kubawar Shari’a 14-18 (minti 10)

Na 1: Kubawar Shari’a 15:16–16:8 (minti 4 ko ƙasa da hakan)

Na 2: Littafi Mai Tsarki Ya Nuna Cewa Maryamu Ba Ta Ci Gaba da Zama “Budurwa” Ba—td 11B (minti 5)

Na 3: Ka Tuna da Jehovah da Kuma Ɗansa—lr babi na 37 (minti 5)

Taron Hidima:

Waƙa ta 103

Minti 10: Ku Taimaka wa Yara Su Yi Shiri don Zuwa Wa’azi. Tattaunawa. Ka saka wa masu sauraro bidiyon nan Ka Zama Abokin Jehobah—Zo Mu Je Wa’azi don su kalla. (Ka shiga dandalin jw.org, ka duba sashen KOYARWAR LITTAFI MAI TSARKI > YARA.) Ka tambayi yaran: Ku nawa ne kuke da jakar zuwa wa’azi? Me da me ke cikin jakarku? Mene ne Safiya ta fara sakawa a cikin jakar wa’azinta? Mene ne kuma take bukata ta saka a cikin jakar? Mene ne Safiya da mamarta za su yi bayan ta gama shirya jakarta? Ka sa wani ƙaramin yaro ko yarinya ta nuna yadda za ta ba da mujalla sa’ad da take wa’azi. Idan ba zai yiwu ku kalli bidiyon ba, sai ka yi wa yara tambayoyin da ke gaba: Ku nawa ne kuke da jakar wa’azi? Waɗanne takardu ne za ku iya sakawa a cikin jakar wa’azinku? Mene ne kuke yi kafin ku fita wa’azi tare da iyayenku? Ka sa wani ƙaramin yaro ko yarinya ta nuna yadda za ta ba da mujalla sa’ad da take wa’azi.

Minti 10: Yadda Wasu Suke Yin Wa’azi da Gaggawa. Dattijo ya gana da masu shela biyu ko uku, waɗanda suka daidaita ayyukansu don su daɗa ƙwazo a wa’azi ko kuma su yi hidimar majagaba. A ƙarshe, ya ambata tsarin fita wa’azi na ikilisiyar, kuma ya ƙarfafa masu shelar su daidaita ayyukansu don su sami damar fita wa’azi.

Minti 10: A Wace Hanya Ce Ka Kyautata Hidimarka? Mai kula da hidima ne zai tattauna wannan sashen. Ka ba masu sauraro dama su faɗi yadda suka amfana daga talifofi na kwanan nan a cikin jerin talifofin nan “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi.” A ƙarshe, ka ƙarfafa dukan masu shela su yi wa’azi da gaggawa ta wajen bin shawarwari da ke waɗannan talifofin.

Waƙa ta 100 da Addu’a

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba