JIGON WATA: KA YI WA’AZIN KALMAR DA GAGGAWA.—2 TIM. 4:2.
Yadda Za Mu Koyi Yin Wa’azi da Gaggawa
Idan muna so mu tsira ma hallakar wannan duniyar, wajibi ne mu san cewa lokaci ya ƙure ma duniyar nan. Yin abubuwan da ke gaba zai taimaka mana mu riƙa tunawa a kullum cewa lokaci ya ƙure ma wannan duniyar.
Ku riƙa yin addu’a Mulkin ya zo.—Mat. 6:10.
Ku kiyaye zuciyarku ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki kowace rana.—Ibran. 3:12.
Ku yi amfani da lokacinku da kyau.—Afis. 5:15, 16; Filib. 1:10.
Ku bar idonku ya riƙa gani “sarai.” Kada ku bar sha’awoyin duniya su janye hankalinku.—Mat. 6:22, 25; 2 Tim. 4:10.
Ku zauna a shirye ta wajen mai da hankali ga yadda annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki suke cika.—Mar. 13:35-37.
Sanin cewa lokaci ya riga ya ƙure wa duniyar nan zai sa mu yi wa’azi da ƙwazo sosai har sai mun ƙarasa aikin.—Yoh. 4:34, 35.