Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Yadda Za Ka Zama Abokin Wa’azi Mai Taimako
Abin da Ya Sa Yake da Muhimmanci: Yesu ya san muhimmancin zuwa wa’azi tare da abokin wa’azi. Shi ya sa a lokacin da ya aiki almajiransa guda 70 yin wa’azi, ya haɗa su bibbiyu. (Luk 10:1) Abokin wa’azi zai iya taimakawa idan wanda yake tare da shi yana bukatar taimako a wani yanayi mai wuya sa’ad da suka fita wa’azi ko kuma idan bai san amsar da zai ba maigida ba. (M. Wa. 4:9, 10) Zai kuma iya gaya ma wanda yake tare da shi labarin abubuwan da ya taɓa fuskanta a wa’azi da kuma wasu shawarwari da za su iya taimaka ma abokin wa’azinsa ya ƙware sosai a yin wa’azi. (Mis. 27:17) Abokan wa’azi za su iya ƙarfafa juna ta irin tattaunawa da suke yi kafin su isa wani ƙofa.—Filib. 4:8.
Ku Bi Wannan Shawarar a Watan Nan:
Bayan kun gama yin wa’azi, ka gaya ma abokin wa’azinka wani abin da ya yi da ya sa ya zama abokin wa’azi mai ban taimako.