Tsarin Ayyuka na Makon 14 ga Afrilu
MAKON 14 GA AFRILU
Waƙa ta 114 da Addu’a
Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
cl babi na 5 sakin layi na 18-21 da akwati a shafi na 55 (minti 30)
Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Fitowa 11-14 (minti 10)
Na 1: Fitowa 12:37-51 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Yin Amfani da Siffofi Ba Ya Daraja Allah—td 40A (minti 5)
Na 3: Abin da Ya Sa Ya Kamata Mu Yafe—lr babi na 14 (minti 5)
Taron Hidima:
Waƙa ta 100
Minti 15: Ku Yi Amfani da Kayayyakin Aiki da Jehobah Ya Tanadar Mana. Tattaunawa bisa ga bayanin da ke Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Disamba 2008, shafi na 20 sakin layi na 14-15. Ka ba masu sauraro dama su faɗi darussan da suka koya.
Minti 15: “Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Yadda Za Ka Zama Abokin Wa’azi Mai Taimako.” Tattaunawa. Ka sa a yi gwaji guda biyu da za su nuna abokin wa’azi da ba shi da ban taimako. Bayan kowane gwaji, ka ba masu sauraro dama su bayyana yadda suke ganin ya kamata abokin wa’azin ya bi da yanayin.
Waƙa ta 45 da Addu’a