Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 1/14 p. 2
  • Ku Taimaki Wanda Kuka Fita Wa’azi Tare

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Taimaki Wanda Kuka Fita Wa’azi Tare
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kasance Mataimaki Mai Kyau a Ƙofa
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Kada Ka Yi Sanyin Gwiwa a Hidimarka
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Hanyoyin Kyautata Yadda Muke Yin Wa’azi—Yadda Za Ka Zama Abokin Wa’azi Mai Taimako
    Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Ka Yi Aikin Da Aka Ba Ka Na Mai-bishara
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 1/14 p. 2

Ku Taimaki Wanda Kuka Fita Wa’azi Tare

1. Ta yaya za mu iya yin koyi da manzo Bulus sa’ad da muka fita wa’azi da ’yan’uwa?

1 A duk lokacin da manzo Bulus yake tare da ’yan’uwa, yana amfani da wannan damar don ya “ƙarfafa” su, shi kuma ya sami ƙarfafa. (Rom. 1:12) Yayin da kuka fita wa’azi tare da wani mai shela, ku riƙa yin amfani da wannan damar don ku ƙarfafa da kuma taimaka masa. Maimakon ku riƙa tafiya kawai ba magana, zai yi kyau ku gaya masa abin da ya taimaka muku ku ƙware a yin wa’azi.

2. Mene ne za mu iya yi don mu taimaki wanda muka fita wa’azi tare ya kasance da gaba gaɗi, kuma me ya sa hakan yake da muhimmanci?

2 Ku Taimake Shi Ya Kasance da Gaba Gaɗi: Wasu masu shela sukan rasa gaba gaɗi sa’ad da suka fita wa’azi, kuma hakan yana bayyana a fuskarsu da muryarsu. Za mu iya sa su kasance da gaba gaɗi ta wajen yaba musu. A waɗanne hanyoyi ne kuma za mu iya taimaka musu su kasance da gaba gaɗi? Wani mai kula mai ziyara yakan gaya ma waɗanda suke wa’azi tare yadda shi ma yakan ji tsoro da kuma yadda yin addu’a yana taimaka masa ya sha kan hakan. Wani ɗan’uwa kuma ya faɗi abin da yake taimaka masa ya kasance da gaba gaɗi. Ya ce: “Nakan yi murmushi kafin in soma magana, amma a wasu lokatai yin hakan ba ya kasance mini da sauƙi. Saboda haka, nakan yi addu’a sosai.” Shin akwai abin da ya taimaka muku ku daɗa kasancewa da gaba gaɗi sa’ad da kuke wa’azi? Idan haka ne, ku gaya ma wanda kuke wa’azi tare.

3. Mene ne za mu iya tattaunawa da wanda muka fita wa’azi tare da zai taimaka masa ya ƙware a yin wa’azi?

3 Ku Gaya Masa Dabarunku: Akwai wata tambaya ko wani furuci, mai yiwuwa game da wani batun da aka sani a yankinku, da yake taimaka muku ku soma tattaunawa da mutane cikin sauƙi? Shin kun sami sakamako mai kyau ne sa’ad da kuka yi amfani da wata gabatarwa a naku kalmomi? Idan haka ne, ku gaya ma wanda kuke wa’azi tare. (Mis. 27:17) Kafin ku isa wurin wanda kuke so ku sake ziyarta, za ku iya gaya ma wanda kuka fita wa’azi tare manufar ziyarar da kuma yadda kuka shirya za ku cim ma hakan. Bayan kun bar wurin ɗalibin, za ku iya bayyana ma wanda kuke wa’azi tare abin da ya sa kuka yi amfani da wani nassi ko bayyani ko kuma wata hanyar koyarwa a hanyar da kuka yi.

4. Me ya sa ya kamata mu riƙa taimaka wa ’yan’uwanmu masu shela?

4 Kiristoci masu wa’azi a ƙarni na farko ba su mai da hankali ga taimaka wa mutanen waje kaɗai ba. Sun san cewa yana da muhimmanci su ƙarfafa juna. (A. M. 11:23; 15:32) Manzo Bulus ya horar da Timoti, sa’an nan ya umurce shi ya koya wa mutane abin da ya koya. (2 Tim. 2:2) Idan muka yi wa ’yan’uwanmu Kiristoci alheri ta wajen taimaka musu sa’ad da muka fita wa’azi tare, za su zama ƙwararru kuma hakan zai sa su yi farin ciki. Ƙari ga haka, za mu faranta wa Ubanmu na sama rai.—Ibran. 13:15, 16.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba