Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 1/14 p. 1
  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Mikah

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Ku Bi Gurbin Annabawa—Mikah
  • Hidimarmu Ta Mulki—2014
  • Makamantan Littattafai
  • Za Mu Yi Tafiya Cikin Sunan Jehovah Har Abada!
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Bayin Jehovah Suna Da Bege Na Gaske
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Menene Jehovah Yake Bukata A Gare Mu?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2003
  • Ta Yaya Za Mu Kasance da Haƙuri Yayin da Muke “Jira”?
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2013
Hidimarmu Ta Mulki—2014
km 1/14 p. 1

Ku Bi Gurbin Annabawa—Mikah

1. Wace tambaya ce mai yiwuwa Mikah ya yi tunani a kai, kuma me ya sa wa’azinsa bai zama aikin banza ba?

1 ‘Yaushe ne za a kawo ƙarshen wannan mugun zamani?’ Mai yiwuwa annabi Mikah ya yi tunani sosai a kan irin wannan tambayar yayin da yake idar da saƙon hukuncin Jehobah bisa masarautar Isra’ila da Yahuda. Amma wa’azinsa bai zama aikin banza ba. A shekara ta 740 a zamanin Mikah, Jehobah ya cika annabcinsa game da Samariya. (Mi. 1:6, 7) Daga baya, aka halaka Urushalima a shekara ta 607 kafin zamaninmu. (Mi. 3:12) Ta yaya za mu yi koyi da Mikah yayin da muke jiran ranar hukuncin Jehobah a zamaninmu?

2. Me ya sa ya kamata mu kasance da haƙuri yayin da muke jiran ranar Jehobah, kuma me zai taimaka mana mu yi hakan?

2 Ku Kasance da Haƙuri: Mikah ya rubuta cewa: “Ni dai zan saurara ga Ubangiji; zan jira Allah na cetona.” (Mi. 7:7) Hakika Mikah bai yi zaman kashe wando ba yayin da yake jiran ƙarshen ya zo. Ya shagala sosai da aikinsa a matsayin annabin Jehobah. Yayin da muke jiran ranar Jehobah, ya kamata mu ma mu shagala da ayyuka ko tasarrufi masu tsarki da kuma ibada. (2 Bit. 3:11, 12) Haƙurin da Jehobah yake yi yana ba mutane damar tuba. (2 Bit. 3:9) Saboda haka, zai dace mu bi gurbin annabawa wajen kasancewa da haƙuri, kamar yadda Allah ya umurce mu mu yi.—Yaƙ. 5:10.

3. Me ya sa ya kamata mu roƙi Jehobah don ya ba mu ruhu mai tsarki?

3 Ku Dogara ga Jehobah don Ya Ba Ku Ƙarfi: Aikin da aka ba Mikah mai wuya ne, amma ya roƙi Jehobah ya ba shi ƙarfin yin aikin. (Mi. 3:8) Jehobah ya san za mu bukaci taimakonsa, shi ya sa ya umurce mu mu roƙe shi don ya ba mu ƙarfi. Da hannu sake, Jehobah yana ba da ƙarfi ga waɗanda suke bukatar hakan domin su iya cika hidimarsu a bautarsa. (Zab. 84:5, 7; Isha. 40:28-31) Ka taɓa shaida taimakon Jehobah yayin da kake yi masa hidima? Kana roƙon Jehobah ya taimaka maka da ruhu mai tsarki a kai a kai kuwa?—Luk 11:13.

4. Mene ne za mu iya koya daga misalin Mikah?

4 Yin nufin Jehobah ne abin da ya fi muhimmanci a rayuwar Mikah. Ya ƙudura ya kasance da aminci duk da cewa mutane masu rashin aminci ne suka kewaye shi. A yau ma, ana gwada amincinmu kowace rana. Saboda haka, zai dace mu ƙudura cewa za mu ci gaba da yin “biyayya da sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin.”—Mi. 4:5.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba