Za Mu Yi Tafiya Cikin Sunan Jehovah Har Abada!
“Mu . . . za mu yi biyayya da sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin.”—MIKAH 4:5.
1. Waɗanne saƙonni aka rubuta a Mikah surori 3 zuwa 5?
JEHOVAH yana da abin da zai gaya wa mutanensa, kuma ya yi amfani da annabinsa Mikah. Nufin Allah ne ya yi maganin masu yin laifi. Zai yi wa Isra’ila horo domin riddanta. Amma abin farin ciki, Jehovah zai albarkaci waɗanda suke tafiya cikin sunansa. Waɗannan saƙonni sun fita sarai a surori 3 zuwa 5 na annabcin Mikah.
2, 3. (a) Shugabannin Isra’ila ya kamata su nuna wane hali, amma menene ainihi suke yi? (b) Ta yaya za ka yi bayanin ƙwalliyar magana da aka yi amfani da ita a Mikah 3:2, 3?
2 Annabin Allah ya ce: “Ku ji, ina roƙonku, ku shugabannai na Yakubu, ku mahukuntan gidan Isra’ila kuma; ba naku ba ne ku san shari’a?” Hakika, wannan shi ya kamata ya zama aikinsu, amma menene ainihi suke yi? Mikah ya ce: “Ku da ku ke ƙin nagarta, kuna son mugunta, masu-cire musu fata, namansu kuma daga ƙasussuwansu; kuna cin naman mutanena kuma; suna feɗe musu fatansu, suna kakkarya ƙasussuwansu; i, suna yanyanka su, sai ka ce domin tukunya, kamar nama cikin tukunyar dahuwa.”—Mikah 3:1-3.
3 Lallai, shugabannan suna tsananta wa fakirai, marasa kāriya! Waɗanda suka ji Mikah sun fahimce ƙwalliyar magana da aka yi amfani da shi a nan. Sa’ad da ake gyara rago da aka yanka ta wajen tafasawa, da farko ana feɗewa daga nan sai a rarraba. Wani lokaci ana fasa ƙashin domin a samu ɓargo. Sai a dafa naman da ƙashin a babbar tukunya, kamar wanda Mikah ya ambata. (Ezekiel 24:3-5, 10) Lallai wannan kwatanci ne da ya yi daidai da tsanani da mutanen zamanin Mikah suke sha a hannun miyagun shugabanni!
Jehovah Yana Son Mu Yi Gaskiya
4. Wane bambanci ya kasance tsakanin Jehovah da shugabannin Isra’ila?
4 Da bambanci ƙwarai tsakanin Makiyayi mai ƙauna, Jehovah, da shugabannin Isra’ila. Domin rashin gaskiyarsu sun kasa cika hakkinsu na kāre garken. Maimakon haka, sun cuci tumaki na alama domin son kai, suna hana su gaskiya wajen shari’a kuma su tilasta musu ‘ayyukan kisa,’ kamar yadda aka faɗa a Mikah 3:10. Menene za mu koya daga wannan yanayin?
5. Menene Jehovah yake bukata wajen waɗanda suke da hakki tsakanin mutanensa?
5 Allah yana bukatar waɗanda suke da hakki tsakanin mutanensa su yi shari’a ta gaskiya. Haka muke gani tsakanin bayin Jehovah a yau. Bugu da ƙari, wannan ya jitu da Ishaya 32:1, inda ya ce: “Duba, wata rana wani sarki za ya yi mulki cikin adalci, hakimai kuma za su yi mulki da shari’a.” Amma a zamanin Mikah, menene muka gani? ‘Masu ƙin nagarta, masu son mugunta’ sun nace wajen yin ha’inci a shari’a.
Addu’o’in Su Waye Ake Amsawa?
6, 7. Wane muhimmin darasi aka nanata a Mikah 3:4?
6 Shin miyagun tsarar Mikah za su yi tsammanin tagomashin Jehovah ne? Babu! Mikah 3:4 ta ce: “Za su tada murya ga Ubangiji, amma ba za ya amsa musu ba; i, za ya ɓoye musu fuskatasa a loton nan, daidai yadda suka yi zunubi cikin aikinsu.” Wannan ya nanata wani muhimmin darasi.
7 Jehovah ba zai amsa addu’o’inmu ba idan muna yin zunubi. Wannan haka yake idan muna rayuwa iri biyu, muna ɓoye zunubinmu muna nuna cewa muna bauta wa Allah da aminci. In ji Zabura 26:4, Dauda ya rera waƙa: “Ban tara zama da mutanen banza ba; ba kuwa zan shiga tare da masu-makirci ba.” Haka nan kuma Jehovah ba zai amsa addu’o’in masu taka Maganarsa da gangan ba!
Ruhun Allah Ya Ba da Ƙarfi
8. Wane gargaɗi aka ba annabawan ƙarya a zamanin Mikah?
8 Lallai wannan aikin ƙazanta ne yake tsakanin shugabannin ruhaniya na Isra’ilawa! Annabawan ƙarya suka sa mutanen Allah suna ta gantali ta ruhaniya. Shugabanni masu kwaɗayi suna cewa ‘Salama!’ amma ainihi yaƙi suke yi da duk wanda bai ba su kome su ci ba. “Domin wannan,” Jehovah ya ce, “za ya zama dare a gare ku, har da ba za ku sami ru’ya ba; za ya zama duhu a gareku har da ba za ku iya duba ba; rana kuma za ta faɗa a bisa annabawan; yini kuma za ya zama baƙi ƙirin a kansu. Masu ru’ya kuma za su ji kunya, masu-duba kuwa su ruɗe; i, dukansu za su rufe leɓunansu.”—Mikah 3:5-7a.
9, 10. Menene yake nufi a ‘rufe leɓuna,’ kuma me ya sa Mikah ba shi da dalilin yin irin wannan abu?
9 Me ya sa “za su rufe leɓunansu”? Wannan shi ne abin da miyagun mutanen zamanin Mikah suka yi domin kunya. Kuma ya dace waɗannan miyagun mutane su ji kunya. “Babu amsawa daga wurin Allah” in ji waɗannan miyagun mutanen. (Mikah 3:7b) Jehovah ba ya mai da hankali ga addu’o’in miyagu masu fahariya ba.
10 Mikah ba shi da dalilin ‘rufe leɓunansa.’ Ba shi da dalilin jin kunya. Jehovah ya amsa addu’o’insa. Ka lura da Mikah 3:8, inda annabin mai aminci ya ce: “Hakika . . . ta wurin ruhun Ubangiji cike ni ke da iko, da shari’a, da ƙarfi.” Lallai Mikah ya yi godiya a dukan hidimarsa mai tsawo da ya yi cikin aminci, ya kasance kullum ‘ta wurin ruhun Ubangiji cike da iko’! Wannan ya ba shi ƙarfi ya “bayyana ma Yakubu laifinsa, ga Isra’ila kuma zunubinsa.”
11. Ta yaya ake ba ’yan Adam ƙarfi su yi shelar saƙonnin Allah?
11 Mikah zai bukaci fiye da iko na ’yan Adam domin ya yi shelar saƙon Allah na hukunci. Ya bukaci ruhun Jehovah, ko kuma ikon aiki. Mu kuma fa? Za mu iya cika umurnin da aka ba mu mu yi wa’azi idan Jehovah ya ƙarfafa mu ta wajen ruhunsa mai tsarki. Ƙoƙarin mu yi wa’azi hakika ba zai yi nasara ba idan muna yin zunubi da ganga. Domin haka, Allah ba zai amsa addu’o’inmu ba na neman ƙarfi da za mu yi wannan aikin. Hakika ba za mu iya shelar saƙon hukunci na Ubanmu na samaniya ba idan “ruhun Ubangiji” ba ya tare da mu. Ta wajen addu’o’i da ake saurara tare da taimakon ruhu mai tsarki, za mu iya faɗan maganar Allah da gaba gaɗi kamar Mikah.
12. Me ya sa almajiran Yesu na farko suka ‘ci gaba da yin maganar Allah da ƙarfin zuciya’?
12 Wataƙila ka tuna da labarin da yake cikin Ayukan Manzanni 4:23-31. Ka yi tunani kana cikin almajiran Yesu na ƙarni na farko. Matsananta suna ƙoƙarin su rufe leɓan mabiyan Kristi. Amma waɗannan masu aminci suka yi addu’a ga Mamallakin Dukan Halitta, suna roƙo: “Ubangiji, ka dubi kashedinsu: ka ba bayinka kuma su faɗi maganarka da ƙarfinzuciya duka.” Menene sakamakon haka? Sa’anda suka yi addu’a, wurin da suke a tattare ya raurawa, dukansu suka cika da ruhu mai tsarki, suka yi maganar Allah da ƙarfin zuciya. Saboda haka, bari mu zuba wa Jehovah ido tare da addu’a kuma mu dogara ga taimakonsa ta wajen ruhu mai tsarki sa’ad da muke cika hidimarmu.
13. Menene zai faru wa Urushalima da Samariya, kuma me ya sa?
13 Ka sake tunanin zamanin Mikah. In ji Mikah 3:9-12, shugabannin masu alhakin kisa suna shari’a ne domin toshiya, firistoci kuma suna koyarwa ne da farashi, annabawan ƙarya kuma suna duba domin kuɗi. Ba abin mamaki ba ne da Allah ya rantse cewa babban birnin Yahuda, Urushalima, “za ta zama tuddai”! Tun da yake bauta ta ƙarya da lalata suna samun kasuwa a Isra’ila, an hure Mikah ya yi gargaɗi cewa Allah zai mai da Samariya “tulin gona.” (Mikah 1:6) Hakika, annabin ya rayu ya ga halaka da aka annabta ta Samariya a hannun sojojin Assuriyawa a shekara ta 740 K.Z. (2 Sarakuna 17:5, 6; 25:1-21) A bayyane yake cewa an idar da waɗannan saƙonni masu ƙarfi a kan Urushalima da Samariya ta ikon Jehovah.
14. Ta yaya annabci da aka rubuta a Mikah 3:12 ta cika, yaya wannan ya kamata ya shafe mu?
14 Babu shakka Yahuda za ta fuskanci hukuncin Jehovah. A cika annabci da yake rubuce a Mikah 3:12, “za a huɗe Sihiyona kamar gona.” Daga ra’ayinmu na ƙarni na 21, mun sani cewa waɗannan abubuwa sun faru sa’ad da Babiloniyawa suka halaka Yahuda da Urushalima a shekara ta 607 K.Z. Wannan ya faru shekaru da yawa bayan annabcin Mikah, amma ya tabbata cewa za ta zo. Babu shakka ya kamata mu ma mu kasance da tabbaci cewa wannan mugun zamani zai zo ƙarshensa a “ranar Allah” yadda aka annabta.—2 Bitrus 3:11, 12.
Jehovah Ya Gyara Al’amura
15. A naka kalmomi, yaya za ka kwatanta annabci da yake rubuce a Mikah 4:1-4?
15 Idan muka sake dubawa, za mu ga cewa Mikah ya sanar da saƙon bege mai ban sha’awa. Kalmomi masu ƙarfafawa ne muka samu a Mikah 4:1-4! Mikah ya faɗi kaɗan haka: “A cikin kwanaki na ƙarshe dutsen gidan Ubangiji za ya kahu a bisa ƙwankolin duwatsu, za ya ɗaukaka kuma bisa tuddai; al’ummai za su rugungunto zuwa gareshi . . . Za ya raba shari’a tsakanin ƙabilai dayawa; za ya raba tsakanin manyan al’ummai manisanta; har su buga takubansu su zama garmuna, masunsu kuma su zama lauzuna; al’umma ba za ta zare ma al’umma takobi ba, ba kuwa za su ƙara koya yaƙi ba. Amma kowa za ya zauna a ƙarƙashin kuringar anab nasa da itacen ɓaurensa; ba kuwa wani mai-tsoratadda su; gama bakin Ubangiji mai-runduna ya faɗi.”
16, 17. Yaya Mikah 4:1-4 take cika a yau?
16 Su wanene “ƙabilai dayawa” da kuma “manyan al’ummai” da aka ambata a nan? Ba al’ummai da gwamnati na wannan duniya ba ce. Maimako, annabcin game da mutane ne da suka fito daga dukan al’ummai da suka haɗa kai a bauta mai tsarki a dutsen bauta ta gaskiya ta Jehovah.
17 Cikin jituwa da annabcin Mikah, bauta mai tsarki na Jehovah ba da daɗewa ba za a yi ta a cikin dukan duniya. A yau mutane ‘masu zukatan kirki’ ana koyar da su tafarkin Jehovah. (Ayukan Manzanni 13:48) Jehovah yana shari’a kuma yana gyara batutuwa na ruhaniya ga masu bi da suke manne wa Mulkin. Za su tsira daga “babban tsananin” suna cikin “taro mai-girma.” (Ru’ya ta Yohanna 7:9, 14) Da yake sun riga sun mai da takubansu garmuna, har a yau suna morar salama da ’yan’uwansu Shaidun Jehovah da kuma wasu. Abin farin ciki ne a kasance tsakaninsu!
Ƙudura Aniya Yin Tafiya Cikin Sunan Jehovah
18. Menene ‘mutum ya zauna a ƙarƙashin itacen inabi da na ɓaure’ yake nufi?
18 A zamaninmu, da tsoro ya rufe duniya kamar bargo, muna farin ciki cewa mutane da yawa suna koyon hanyoyin Jehovah. Muna saurarar lokaci da yanzu ya yi kusa da dukan waɗanda suke ƙaunar Allah ba za su koyi yaƙi ba amma za su zauna ƙarƙashin inabinsu da kuma itacen ɓaurensu. A lokatan Littafi Mai Tsarki ana yawan shuka itacen inabi a garka. (Luka 13:6) Zama a ƙarƙashin itacen inabi da na ɓaure alama ce ta salama, bunƙasa, da kuma kwanciyar hankali. Ko a yanzu ma, dangantakarmu da Jehovah na kawo mana salama da kwanciyar hankali na ruhaniya. Sa’ad da wannan yanayi zai kasance a ƙarƙashin Mulkin, ba za mu ji tsoro ba domin za mu kasance da kwanciyar hankali.
19. Menene yake nufi a yi tafiya cikin sunan Jehovah?
19 Domin mu more tagomashi da albarka na Allah, dole mu yi tafiya cikin sunan Jehovah. An furta wannan a Mikah 4:5, inda annabin ya ce: “Dukan ƙabilan mutane za su yi biyayya da sunan allahnsu, mu kuwa za mu yi biyayya da sunan Ubangiji Allahnmu har abada abadin.” Yin tafiya cikin sunan Jehovah ba ya nufin faɗa kawai cewa shi ne Allahnmu. Ya bukaci fiye da yin kalami a taron Kirista da aikin wa’azin Mulki, ko da irin waɗannan ayyuka suna da muhimmanci. Idan muna tafiya cikin sunan Jehovah, za mu keɓe kanmu gare shi kuma mu yi ƙoƙari mu bauta masa da aminci da ƙauna daga zuciya ɗaya. (Matta 22:37) Babu shakka, da yake mu masu bauta masa ne mun ƙuduri aniya mu yi tafiya cikin sunan Jehovah Allahnmu har abada.
20. Menene aka annabta a Mikah 4:6-13?
20 Yanzu ka bincika kalmomin annabci na Mikah 4:6-13. “Ɗiyar Sihiyona” za ta je bauta ‘har Babila.’ Abin da ya faru ke nan da mazaunan Urushalima a ƙarni na bakwai K.Z. Duk da haka, annabcin Mikah ya nuna cewa raguwarsu za su komo Yahuda, kuma bayan an sake gina Sihiyona, Jehovah zai tabbata cewa an halaka dukan abokan gābanta.
21, 22. Ta yaya Mikah 5:2 ta cika?
21 Mikah sura 5 ta faɗi wasu aukuwa na ban mamaki. Alal misali, ka lura da abin da aka faɗa a Mikah 5:2-4. Mikah ya annabta cewa Sarki da Allah ya naɗa—wanda “mafitansa tun daga zamanin dā, tun fil’azal”—zai fito daga Baitalahmi. Zai yi kiwo cikin “ikon Ubangiji.” Bugu da ƙari, wannan Mai Mulki zai sami ɗaukaka, ba a Isra’ila ba kawai, amma “har iyakan duniya.” Sanin wannan zai ba wa dukan duniya mamaki, amma ba abin mamaki ba ne gare mu.
22 Waye ne mutum mafi muhimmanci da aka haifa a Baitalahmi? Kuma waye zai sami ɗaukaka “har iyakan duniya”? Babu wani sai Almasihu, Yesu Kristi! Sa’ad da Hirudus Mai Girma ya tambayi manyan firistoci da kuma marubuta inda za a haifi Almasihu, suka amsa: “A Baitalahmi na Yahudiya.” Suka yi ƙaulin kalmomin Mikah 5:2. (Matta 2:3-6) Wasu talakawa ma sun san da wannan, domin Yohanna 7:42, ya yi ƙaulinsu suna cewa: “Ko nassin ba ya faɗi ba Kristi daga cikin irin Dauda za ya fito, daga cikin Baitalahmi kuma, ƙauye inda Dauda ya ke?”
Wartsakewa ta Gaske ga Mutane
23. Menene yake faruwa yanzu wajen cika Mikah 5:7?
23 Mikah 5:5-15 ta yi nuni da hari na Assuriyawa da za su sami nasara na ɗan lokaci kuma ya nuna cewa Allah zai zartar da hukunci a kan al’ummai marar biyayya. Mikah 5:7 ta yi alkawarin maido da raguwar Yahudawa da suka tuba zuwa ƙasarsu, amma waɗannan kalmomi sun shafi zamaninmu. Mikah ya ce: “Ringin Yakubu kuma za ya kasance a cikin tsakiyar al’ummai dayawa kamar rāɓa daga wajen Ubangiji, kamar saukowar ruwa a bisa ciyawa.” An yi amfani da wannan bayani na alama wajen annabta cewa raguwar Yakubu, ko Isra’ila, za ta zama albarka ce daga Allah ga mutanen. “Waɗansu tumaki” na Yesu da suke da begen zama a duniya, suna farin cikin bauta da zuciya ɗaya tare da raguwar “Isra’ila na Allah” na zamani, suna taimako a wartsake wasu a ruhaniya. (Yohanna 10:16; Galatiyawa 6:16; Zephaniah 3:9) Game da wannan, akwai wani darasi na bincike. Mu masu shelar Mulki, dukanmu ya kamata mu daraja gatarmu ta kai wa mutane wartsakewa na gaske.
24. Waɗanne darussa daga Mikah surori 3 zuwa 5 ta shafe ka?
24 Menene ka koya daga surori 3 zuwa 5 na annabcin Mikah? Wataƙila darussa kamar waɗannan: (1) Allah yana bukatar mutane masu hakki tsakanin mutanensa su yi shari’a ta gaskiya. (2) Jehovah ba zai amsa addu’o’inmu ba idan muna zunubi da ganga. (3) Za mu iya cika umurni da aka ba mu na wa’azi idan Allah ya ƙarfafa mu ta wajen ruhunsa mai tsarki. (4) Domin mu more tagomashin Allah dole ne mu yi tafiya cikin sunan Jehovah. (5) Da yake mu masu shelar Mulkin ne, ya kamata mu riƙe gatarmu ta kai wartsakewa ta gaske ga mutane. Wasu darussa wataƙila sun shafe ka. Amma menene kuma za mu koya daga wannan littafi na annabci? Talifi na gaba zai taimake mu mu sami darussa masu amfani daga surori biyu na ƙarshe na annabcin Mikah mai ƙarfafa bangaskiya.
Yaya Za Ka Amsa?
• Menene Allah yake bukata daga waɗanda suke da hakki tsakanin mutanensa?
• Me ya sa addu’a da ruhu mai tsarki suke da muhimmanci game da hidimarmu ga Jehovah?
• Ta yaya mutane suke ‘tafiya cikin sunan Jehovah’?
[Hoto a shafi na 9]
Za ka iya bayyana kwatancin Mikah da ya ƙunshi tukunyar dafa abinci?
[Hotuna a shafi na 10]
Kamar Mikah muna cika hidimarmu da gaba gaɗi