Ku Taimaka Musu Su ‘Kafu Cikin Bangaskiya’
Abin farin ciki ne ganin yadda Jehobah yake yi wa aikinmu na almajirantarwa albarka, kuma tabbacin hakan shi ne yadda mutane fiye da 250,000 suke yin baftisma kowace shekara. (K. Sha 28:2) Muddin mai shela ya yi nazari da ɗalibinsa har ya yi baftisma, abin da yakan zo zuciyarsa shi ne ya daina nazari da wannan ɗalibin don ya sami zarafin taimaka ma wasu ɗalibai dabam. Ɗalibin ma yana iya ji kamar ya kamata ya daina nazarin domin ya sami lokacin yin wa’azi sosai. Amma, yana da muhimmanci ɗalibai su san abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa sosai. Ya kamata su zama “dasassu” cikin Kristi kuma su ‘kafu cikin bangaskiya.’ (Kol. 2:6, 7; 2 Tim. 3:12) Saboda haka, bayan ɗalibi ya yi baftisma, ya kamata ya ci gaba da nazari har sai ya gama nazarin littattafan nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da kuma “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah.”—Ka duba Hidimarmu ta Mulki na Afrilu 2011, shafi na 2.