Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 4/11 p. 2
  • Akwatin Tambaya

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Akwatin Tambaya
  • Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Makamantan Littattafai
  • Ku Taimaka Musu Su ‘Kafu Cikin Bangaskiya’
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Yadda Za Ka Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma—Sashe na Biyu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Yadda Za Ka Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma​—Sashe na Daya
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2020
  • Yadda Kowa a Ikilisiya Zai Taimaki Dalibi Ya Yi Baftisma
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah (Na Nazari)—2021
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2011
km 4/11 p. 2

Akwatin Tambaya

◼ Har tsawon wane lokaci ne za mu iya yin nazari da ɗalibin Littafi Mai Tsarki da ke samun ci gaba?

Ya fi kyau a ci gaba da nazari da ɗalibin Littafi Mai Tsarki da ke samun ci gaba har sai ya kammala littattafai biyu, wato, Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da kuma “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah.” Za a yi hakan ko idan ɗalibin ya yi baftisma kafin ya kammala littattafai biyun. Bayan ya yi baftisma za mu iya ci gaba da ba da rahoton sa’o’i da komawa ziyara da kuma nazarin da muka yi da shi. Idan wani mai shela ya bi mu zuwa wurin ɗalibin kuma ya sa baki a nazarin, zai iya ba da rahoto.—Ka duba Hidimarmu Ta Mulki ta Maris 2009, shafi na 2.

Yana da muhimmanci sababbi su kafu cikin gaskiya sosai kafin mu daina nazari da su. Suna bukatar su zama “dasassu” cikin Kristi da kuma ‘kafaffu cikin bangaskiya’ don su jimre da gwaje-gwajen da za su fuskanta. (Kol. 2:6, 7; 2 Tim. 3:12; 1 Bit. 5:8, 9) Ƙari ga hakan, suna bukatar tacaccen “sanin gaskiya” don su koyar da mutane da kyau. (1 Tim. 2:4) Ta wurin kammala littattafai biyu da ɗalibanmu, muna taimaka musu su kafu sosai a kan ‘hanya wadda ta nufa wajen rai.’—Mat. 7:14.

Kafin dattawa su yarda wani ya yi baftisma, ya kamata su tabbata cewa ya fahimci muhimman koyarwa na Littafi Mai Tsarki sosai kuma yana rayuwa da ta jitu da su. Ya kamata dattawa su mai da hankali musamman sa’ad da suke yin la’akari a kan ɗalibin da bai kammala littafin nazari na farko ba. Idan mutum bai cancanci yin baftisma ba, dattawa za su tabbata cewa ya samu taimako da ya dace don ya cancanci yin baftisma a nan gaba.—Ka duba ƙasidar nan ‘Ku je, Ku Almajirtar, Kuna yi Musu Baftisma’ shafuffuka na 57-60.

[Bayanin da ke shafi na 2]

Yana da muhimmanci sababbi su kafu cikin gaskiya sosai

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba