Bitar Makarantar Hidima ta Allah
Za a tattauna tambayoyin da ke gaba a Makarantar Hidima ta Allah a makon 30 ga Disamba, 2013. An saka kwanan watan da za a tattauna waɗannan bayanan ne domin ku yi bincike sa’ad da kuke shiri don makaranta kowane mako.
1. Mene ne zai taimaka mana mu nuna tawali’u ga masu iko? (Tit. 3:2) [4 ga Nuwamba, w03 4/1 shafi na 31 sakin layi na 18-19]
2. Ta yaya ne aka ceci shafaffun Kiristoci ta wurin ‘wanka’ kuma aka ‘sabonta su ta ruhu mai tsarki’? [4 ga Nuwamba, w08 10/15 shafi na 30 sakin layi na 7]
3. Ta yaya za mu shiga cikin hutun Allah? (Ibran. 4:9-11) [11 ga Nuwamba, w11 7/15 shafi na 28 sakin layi na 16, 17]
4. A Ranar Kafara, wane ne babban firist yake wakilta, kuma mene ne hadayu da ya miƙa yake nunawa? (Ibran. 9:11-14) [18 ga Nuwamba, w09 9/15 shafi na 27 sakin layi na 9]
5. Me ya sa Yaƙub ya rubuta cewa “hikima mai-fitowa daga bisa tsatsarka ce da fari, bayan wannan mai-salama ce”? (Yaƙ. 3:17) [25 ga Nuwamba, w11 8/15 shafi na 30 sakin layi na 15]
6. Su wane ne “matattu” da aka yi wa “wa’azin bishara”? (1 Bit. 4:6) [2 ga Disamba, w08 11/15 shafi na 21 sakin layi na 8]
7. Bisa ga abin da ke cikin 1 Yohanna 2:7, 8, wace doka ce Yohanna yake kira ‘tsohuwa’ da kuma “sabuwa”? [9 ga Disamba, w08 12/15 shafi na 27 sakin layi na 5]
8. Wane ne ke da laƙabin nan “Alpha da Omega” da kuma “na Farko da na Ƙarshe”? (R. Yoh. 1:8, 17) [16 ga Disamba, w09 1/15 shafi na 30 sakin layi na 6]
9. Ta yaya ne ƙahoni uku na ƙarshe suka busa “kaito”? (R. Yoh. 8:13; 9:12; 11:14) [23 ga Disamba, w09 1/15 shafi na 32 sakin layi na 3]
10. Mene ne “sarari” ko kuma iska da aka zuba kasko na bakwai a ciki? (R. Yoh. 16:17) [30 ga Disamba, w09 2/15 shafi na 4, sakin layi na 1]