Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 11/13 p. 2
  • Tambayoyin Masu Shela

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Tambayoyin Masu Shela
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Makamantan Littattafai
  • A Wane Lokaci Ne Ya Kamata a Rufe Kai, Kuma Me Ya Sa?
    “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah”
  • Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2015
  • Tambayoyi Daga Masu Karatu
    Hasumiyar Tsaro Mai Shelar Mulkin Jehobah—2009
  • Abubuwan da Bai Kamata a Yi Ba a Wa’azi
    Littafin Taro Don Rayuwa ta Kirista da Hidimarmu—2017
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 11/13 p. 2

Tambayoyin Masu Shela

◼ Ya kamata ’yar’uwa mai shela ta ɗaura ɗankwali ne idan wani ɗan’uwa mai shela yana tare da ita sa’ad da take nazari da mutane?

Idan ’yar’uwa mai shela ta je nazari da wani da ta saba yin nazari da shi kuma mai shela namiji yana tare da ita, zai dace ta ɗaura ɗankwali. (1 Kor. 11:3-10) Littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah” ya bayyana a shafi na 210 cewa: “Alal misali, wataƙila tana bukatar ta . . . gudanar da nazarin Littafi Mai Tsarki a gaban namiji da ya yi baftisma. Domin waɗannan ayyukan sun shafi ikilisiyar Kirista, za ta rufe kanta ta nuna tana yin aikin da ainihi aikin maza ne.” Ya kamata ta yi hakan ko da suna yin nazarin a gida ne ko kuma a bakin ƙofa ko dai a wani wuri dabam.

Amma idan tana ƙoƙarin kafa nazarin ne kawai, kuma ko da tana tattauna ɗaya daga cikin littattafan da muke amfani da su wajen gudanar da nazari da mutane, ba ta bukata ta ɗaura ɗankwali idan tana tare da ɗan’uwa mai shela. Tun da yake ana kafa nazari da mutane a hankali ne bayan an tattauna da su sau da sau, mai shelar ce za ta yanke shawara a kan lokacin da zai dace ta soma ɗaura ɗankwali bisa ga yanayin.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba