Tsarin Ayyuka na Makon 18 ga Nuwamba
MAKON 18 GA NUWAMBA
Waƙa ta 20 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
jl Darasi na 8-10 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: Ibraniyawa 9-13 (minti 10)
Na 1: Ibraniyawa 10:19-39 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Sujjada wa Gicciye Saɓo Ne—td 18B (minti 5)
Na 3: Hanyoyi Dabam-dabam da Za Mu Iya Ƙarfafa Mutane—Rom. 15:4; 2 Kor. 1:3, 4 (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 10
Minti 10: Tambayoyin Masu Shela. Tattaunawa.
Minti 10: “Mun Kawo Muku Ziyara Ne Domin . . .” Tattaunawa. Bayan haka, ka ambata littattafan da za a ba mutane a watan Disamba kuma ka sa a yi amfani da abin da aka tattauna a wannan talifin wajen yin gwaji ɗaya ko biyu.
Minti 10: Jehobah Yana Jin Addu’ar Bayinsa. (1 Yoh. 3:22) Tattaunawa bisa ga bayanin da ke cikin Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Fabrairu 2010 shafuffuka na 6-7, sakin layi na 6-7, da kuma Hasumiyar Tsaro ta 15 ga Disamba 2010, shafi na 27, sakin layi na 4. Ka ba masu sauraro dama su faɗi darussan da suka koya.
Waƙa ta 56 da Addu’a