Tambayoyi Daga Masu Karatu
Ya dace ne ’yar’uwa ta ɗaura ɗankwali sa’ad da take fassara jawaban Littafi Mai Tsarki zuwa yaren kurame a taron Kirista, manyan taro, ko kuma taron gunduma?
Galibi, ya kamata mace Kirista ta ɗaura ɗankwali sa’ad da take kula da al’amuran da ya kamata mijinta ko kuma wani ɗan’uwa a cikin ikilisiya ya kula da su. Hakan ya jitu da mizanin da manzo Bulus ya faɗa, cewa “kowace mace da ta ke yin addu’a ko wa’azi, kanta ba luluɓi, tana yi wa kanta ƙanƙanci,” domin “kan mace kuma namiji ne.” (1 Kor. 11:3-10) Sa’ad da ’yar’uwa ta ɗaura ɗankwalin da ya dace a irin wannan yanayin, hakan alama ce ta miƙa kai ga tsarin Allah a cikin ikilisiyar Kirista.—1 Tim. 2:11, 12.a
Idan ɗan’uwa yana ba da jawabi kuma ’yar’uwa tana fassarawa zuwa yaren kurame kuma fa? Hakika, ’yar’uwar tana idar da saƙo ne kawai daga mai jawabin zuwa ga jama’a. Wato, koyarwar ba ta ta ba ce amma ta ɗan’uwan da take yi wa fassara ce.
Amma fassara yaren kurame ya bambanta sosai da fassara harsunan da ake furtawa. A harsunan da ake furtawa, masu sauraro suna iya mai da hankali ga mai jawabin kuma har ila su saurari mai fassarar. Kuma akasin fassara yaren kurame, ’yan’uwa mata da suke fassara yaren da ake faɗi ba sa kasancewa a irin yanayin da za a mai da musu dukan hankali. A wani lokaci, suna iya zaɓan su zauna sa’ad da suke fassara, ko kuma su kasance a tsaye suna kallon mai jawabin maimakon jama’a. Saboda haka, ba wajibi ba ne ’yar’uwar da take fassara zuwa wani yaren da ake faɗi ta ɗaura ɗankwali ba.
Ƙari ga hakan, domin ci gaba da aka samu a fasaha wanda ake amfani da shi sa’ad da ake fassara zuwa yaren kurame, mai fassarar sau da yawa yakan zama ainihin wanda masu sauraro suke mai da wa hankali. Surar mai fassarar ita ce ake nunawa a babban talabijin a yawancin lokaci, yayin da wataƙila masu sauraro ba za su ga mai jawabin ba. Saboda haka, zai dace ’yar’uwa da take fassara zuwa yaren kurame ta fahimci hakkinta a matsayin mai fassara ta wajen ɗaura ɗankwali.
Yaya wannan canji ya shafi fassara Makarantar Hidima ta Allah, gwaji, da kalamai a Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya, Taron Hidima, da kuma Nazarin Hasumiyar Tsaro zuwa yaren kurame? Ya kamata ’yar’uwa wadda take fassara zuwa yaren kurame ta ɗaura ɗankwali a wannan lokacin ne? Ba zai zama wajibi ba ’yar’uwa ta ɗaura ɗankwali a wasu yanayi, tun da yake ya kamata dukan waɗanda suka halarci taron su fahimci cewa ba ita ba ce ainihi take gudanar da taron ba. Alal misali, kamar sa’ad da take fassara kalamai na masu sauraro, jawabai na ’yan’uwa mata, ko kuma gwaji. Amma, ya kamata ta ɗaura ɗankwali sa’ad da take fassara jawabai na ’yan’uwa maza a lokacin waɗannan taron, sa’ad da take yi wa mai gudanar da Nazarin Hasumiyar Tsaro fassara ko mai gudanar da Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya, ko sa’ad da take ja-gora a fassara waƙoƙi. A lokacin taro, ’yar’uwa tana iya fassara jawaban ’yan’uwa maza, mata, yara, da dattawa. Saboda haka, zai fi dacewa ta ɗaura ɗankwali a dukan lokacin taron.
[Hasiya]
a Don ƙarin bayani game da wannan batu na mace Kirista ta ɗaura ɗankwali, ka duba shafuffuka na 209 zuwa 212 na littafin nan “Ku Tsare Kanku Cikin Ƙaunar Allah.”