“Mun Kawo Muku Ziyara Ne Domin . . .”
Sa’ad da masu gida suka buɗe ƙofa kuma suka gan mu a tsaye, suna iya yin mamakin abin da ya kawo mu. Sa’ad da muke gabatar da kanmu, mene ne za mu iya faɗa da zai sa su saki jiki? Bayan gaisuwa, wasu masu shela sukan soma bayaninsu da kalmar nan “domin.” Alal misali, suna iya cewa: “Mun kawo muku ziyara ne domin mutane da yawa sun damu game da matsalar aikata laifi; shin kana ganin . . .” Wasu kuma suna iya cewa: “Mun kawo muku ziyara ne domin muna koya wa mutane Littafi Mai Tsarki kyauta.” Idan muka gaya wa masu gida dalilin da ya sa muka kawo musu ziyara tun da wuri, hakan zai iya sa su saurari abin da za mu faɗa.