Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 10/13 p. 1
  • Kalmar Allah Tana da Amfani Wajen Koyarwa

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kalmar Allah Tana da Amfani Wajen Koyarwa
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Makamantan Littattafai
  • Ka Kiyaye Azancinka
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
  • “Bari a Yi Nufin Allah”
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Kalmar Allah Tana da Iko
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • ‘Abinci a Lotonsa’
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
Dubi Ƙari
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 10/13 p. 1

Kalmar Allah Tana da Amfani Wajen Koyarwa

1. Mene ne jigon taron da’ira da za a yi a shekara ta 2014, kuma wace tambaya ce za a tattauna a taron?

1 Jehobah “Mai-koya” mana shi ne malamin da ya fi kowa iya koyarwa. (Isha. 30:20, 21) Amma ta yaya Jehobah yake koyar da mu? Ya ba mu littafin da ya fi sauran littattafai, kuma wannan littafin shi ne Kalmarsa da ya hure, wato, Littafi Mai Tsarki. Ta yaya za mu amfana daga koyarwar Allah a dukan fannonin rayuwarmu? Za a tattauna wannan tambayar a taron da’ira da za a yi a shekara ta 2014. Jigon taron da’irar shi ne, “Kalmar Allah Tana da Amfani Wajen Koyarwa,” kuma an ɗauko ne daga 2 Timotawus 3:16.

2. Amsoshin waɗanne tambayoyi ne za su sa mu gane muhimman darussan taron?

2 Ku Mai da Hankali ga Waɗannan Muhimman Darussan: A wannan taron, za mu sami amsoshi ga tambayoyin da ke gaba, waɗanda za su taimaka mana mu fahimci muhimman darussan da ake koya mana:

• Yaya muke amfana daga koyarwar Allah? (Isha. 48:17, 18)

• Wane tabbaci ne za mu iya kasancewa da shi idan muka daidaita yanayinmu don mu yi hidima ta cikakken lokaci? (Mal. 3:10)

• Mene ne ya kamata mu yi sa’ad da wata baƙuwar koyarwa ta so ta zama mana tarko? (Ibran. 13:9)

• Ta yaya za mu bi misalin Yesu a yin ‘koyarwa’? (Mat. 7:28, 29)

• Me ya sa ya kamata waɗanda suke koyarwa a cikin ikilisiya su koyar da kansu? (Rom. 2:21)

• A waɗanne hanyoyi ne za mu iya yin amfani da Kalmar Allah? (2 Tim. 3:16)

• Ta yaya “raurawar” ko kuma girgizar da al’ummai da Jehobah yake yi take amfanar mutane? (Hag. 2:6, 7)

• Wane tabbaci ne Jehobah yake da shi game da mu? (Afis. 5:1)

• Me ya sa ya kamata mu dāge sosai don mu ci gaba da bin koyarwar Jehobah? (Luk 13:24)

3. Me ya sa yake da muhimmanci mu halarci wannan taron kuma mu mai da hankali ga koyarwar da aka shirya mana a kan kari?

3 A ayoyin da suka gabaci ayar da aka ɗauko jigon wannan taron, manzo Bulus ya bayyana cewa zamaninmu zai kasance da wuya. Ya ce: “Miyagun mutane da masu-hila za su daɗa mugunta gaba gaba, suna ruɗi, ana ruɗinsu.” (2 Tim. 3:13) Zai dace mu saurari koyarwar Allah kuma mu bi ta don kada a ruɗe mu, ko ba haka ba? Saboda haka, bari mu yi iya ƙoƙarinmu mu halarci wannan taron kuma mu mai da hankali don mu amfana daga wannan koyarwa da aka shirya mana a kan kari.

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba