Watchtower LABURARE NA INTANE
Watchtower
LABURARE NA INTANE
Hausa
Ɓ
  • Ā
  • ā
  • Ɓ
  • ɓ
  • ɗ
  • Ɗ
  • Ƙ
  • ƙ
  • ꞌY
  • ꞌy
  • LITTAFI MAI TSARKI
  • WALLAFE-WALLAFE
  • TARO
  • km 11/13 p. 3
  • Kalmar Allah Tana da Iko

Babu bidiyo don wannan zabin

Yi hakuri, bidiyon na da dan matsala

  • Kalmar Allah Tana da Iko
  • Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • Makamantan Littattafai
  • ‘Abinci a Lotonsa’
    Hidimarmu Ta Mulki—2010
  • Kalmar Allah Tana da Amfani Wajen Koyarwa
    Hidimarmu Ta Mulki—2013
  • “Bari a Yi Nufin Allah”
    Hidimarmu Ta Mulki—2011
  • Ka Kiyaye Azancinka
    Hidimarmu Ta Mulki—2012
Hidimarmu Ta Mulki—2013
km 11/13 p. 3

Kalmar Allah Tana da Iko

1. Mene ne jigon taro na musamman na shekarar hidima ta 2014?

1 Littafi Mai Tsarki ya fi duk wani abin da ’yan Adam suka ƙirƙiro amfani don yana da ikon canja rayuwarmu, daidaita tunaninmu da kuma muradinmu don su jitu da ra’ayin Jehobah. Kalmar Allah tana da iko sosai kuwa? Ta yaya za mu yi amfani da ikonta a hanyar da ta dace a rayuwarmu? Ta yaya za mu yi amfani da ita da kyau wajen taimaka ma wasu? Yayin da ake tattauna waɗannan batutuwa a taro na musamman da aka shirya don shekara ta 2014, mun tabbata cewa dukanmu za mu kyautata dangantakarmu da Allah. Jigon taron shi ne “Kalmar Allah Tana da Iko,” kuma an ɗauko shi ne daga Ibraniyawa 4:12.

2. Waɗanne tambayoyi ne ya kamata mu saurara don mu sami amsoshinsu?

2 Ku Mai da Hankali ga Amsoshin Waɗannan Tambayoyi: Yayin da kuke sauraron jawabai a wannan taron, ku mai da hankali ga amsoshin waɗannan tambayoyi da ke gaba.

• Me ya sa ya kamata mu dogara ga Maganar Jehobah? (Zab. 29:4)

• Ta yaya ikon Kalmar Allah za ta iya shafar rayuwarmu? (Zab. 34:8)

• Ta yaya za ku bar Kalmar Allah ta ja-gorance ku a wa’azi? (2 Tim. 3:16, 17)

• Ta yaya za mu guji faɗawa cikin tarkunan da duniyar Shaiɗan take ɗanawa? (1 Yoh. 5:19)

• Ta yaya matasa za su yi nasara a bautarsu ga Jehobah? (Irm. 17:7)

• Ta yaya za mu kasance da ƙarfi sa’ad da muka raunana? (2 Kor. 12:10)

• Mene ne zai taimaka mana mu yi canje-canje ko da mun riga mun shaƙu da wani hali marar kyau? (Afis. 4:23)

3. Ƙari ga jawaban da za mu ji, a wace hanya ce kuma za mu amfana daga wannan taro na musamman?

3 Hakika, za mu amfana sosai daga jin waɗannan bayanan! Ƙari ga taro na da’ira da na gunduma, wannan taro na musamman zai ba mu damar sanin ’yan’uwa da yawa daga ikilisiyoyi dabam-dabam kuma za mu ji daɗin yin cuɗanya da su. (Zab. 133:1-3; 2 Kor. 6:11-13) Saboda haka, ku nemi zarafi don yin hira da abokanku da kuka rabu da su da daɗewa, kuma ku ƙulla abota da wasu ’yan’uwa. Ƙari ga haka, idan akwai wani baƙo mai ba da jawabi wato, kamar mai kula da gunduma ko kuma wani ɗan’uwa daga Bethel, zai dace ku je ku gai da shi da matarsa. Hakika, muna da dalilai da yawa na yin ɗokin halartan wannan taro na musamman!

    Littattafan Hausa (1987-2026)
    Fita
    Shiga Ciki
    • Hausa
    • Raba
    • Wadda ka fi so
    • Copyright © 2026 Watch Tower Bible and Tract Society of Pennsylvania
    • Ka'idojin Amfani
    • Tsarin Tsare Sirri
    • Saitin Tsare Sirri
    • JW.ORG
    • Shiga Ciki
    Raba