Tsarin Ayyuka na Makon 21 ga Oktoba
MAKON 21 GA OKTOBA
Waƙa ta 33 da Addu’a
□ Nazarin Littafi Mai Tsarki na Ikilisiya:
wt babi na 17, sakin layi na 1-7 (minti 30)
□ Makarantar Hidima ta Allah:
Karatun Littafi Mai Tsarki: 1 Tasalonikawa 1-5–2 Tasalonikawa 1-3 (minti 10)
Na 1: 1 Tasalonikawa 2:9-20 (minti 4 ko ƙasa da hakan)
Na 2: Mene Ne Za Mu Iya Koya Daga Halayen Sulaimanu Masu Kyau da Marasa Kyau?—Rom. 15:4 (minti 5)
Na 3: Halitta Ya Jitu da Kimiyya na Gaske; Bai Yarda da Ra’ayin Juyin Rai Ba—td 20A (minti 5)
□ Taron Hidima:
Waƙa ta 125
Minti 15: Mene Ne Muka Koya? Tattaunawa. Ka sa a karanta Markus 1:40-42 da Markus 7:32-35 da kuma Luka 8:43-48. Ka tattauna yadda waɗannan ayoyin za su taimaka mana a wa’azi.
Minti 15: “Ku Yi Amfani da Dandalinmu Wajen Koyar da Yaranku.” Tambayoyi ana ba da amsoshi. Sa’ad da kuke tattauna sakin layi na 3, ka bayyana yadda za su iya shiga sashen “Umurni ga Iyaye” kuma ka ba da misalin umurnin da ke wurin. Sa’ad da kuke tattauna sakin layi na 4, ka ba iyalai dama su faɗi yadda suka yi amfani da dandalinmu a lokacin da suke bauta ta iyali.
Waƙa ta 88 da Addu’a